بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
عَبَسَ وَتَوَلَّىٰٓ ١Yã game huska* kuma ya jũya bãya أَن جَآءَهُ ٱلۡأَعۡمَىٰ ٢Sabõda makãho yã je masa وَمَا يُدۡرِيكَ لَعَلَّهُۥ يَزَّكَّىٰٓ ٣To, me ya sanar da kai cẽwa watakila shi ne zai tsarkaka أَوۡ يَذَّكَّرُ فَتَنفَعَهُ ٱلذِّكۡرَىٰٓ ٤Ko ya tuna, dõmin tunãwar ta amfane shi أَمَّا مَنِ ٱسۡتَغۡنَىٰ ٥Amma wanda ya wadãtu da dũkiya فَأَنتَ لَهُۥ تَصَدَّىٰ ٦Sa'an nan kai kuma ka ɗora bijira zuwa gare shi وَمَا عَلَيۡكَ أَلَّا يَزَّكَّىٰ ٧To, me zai cũce ka idan bai tsarkaka ba وَأَمَّا مَن جَآءَكَ يَسۡعَىٰ ٨Kuma, amma wanda ya zomaka yana gaugãwa وَهُوَ يَخۡشَىٰ ٩Alhãli shĩ yanã jin tsõrõn Allah فَأَنتَ عَنۡهُ تَلَهَّىٰ ١٠Kai kuma kã shagala ga barinsa كـَلَّآ إِنَّهَا تَذۡكِرَةٌ ١١A'aha! Lalle ne, wannan tunãtarwa ce فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ ١٢Sabõda wanda ya so ya tuna Shi (Allah) فِي صُحُفٍ مُّكَرَّمَةٍ ١٣(Tunãtarwa ce) ta cikin littafai abãban girmamãwa مَّرۡفُوعَةٍ مُّطَهَّرَةِۭ ١٤Abãban ɗaukakãwa, abãban tsarkakẽwa بِأَيۡدِي سَفَرَةٍ ١٥A cikin hannãyen mala'iku marubũta كِرَامِۭ بَرَرَةٍ ١٦Mãsu daraja, mãsu ɗã'a ga Allah قُتِلَ ٱلۡإِنسَٰنُ مَآ أَكۡفَرَهُۥ ١٧An la'ani mutum (kafiri). Mẽ yã yi kãfircinsa مِنۡ أَيِّ شَيۡءٍ خَلَقَهُۥ ١٨Daga wane abu, (Allah) Ya halitta shi مِن نُّطۡفَةٍ خَلَقَهُۥ فَقَدَّرَهُۥ ١٩Daga ɗigon maniyyi, Ya halitta shi sa'an nan Ya ƙaddarã shi (ga halaye) ثُمَّ ٱلسَّبِيلَ يَسَّرَهُۥ ٢٠Sa'an nan, hanyarsa ta fita Ya sauƙaƙe masa ثُمَّ أَمَاتَهُۥ فَأَقۡبَرَهُۥ ٢١Sa'an nan, Ya matar da shi sai Ya sanya shi a cikin kabari ثُمَّ إِذَا شَآءَ أَنشَرَهُۥ ٢٢Sa'an nan, idan Ya so lalle ne zai tãyar da shi كـَلَّا لَمَّا يَقۡضِ مَآ أَمَرَهُۥ ٢٣Haƙĩƙa bai i da aikata abin da Allah Ya umurce shi ba (lõkacin sanya shi a cikin kabari) فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ إِلَىٰ طَعَامِهِۦٓ ٢٤To, mutum ya dũba zuwa ga abincinsa أَنَّا صَبَبۡنَا ٱلۡمَآءَ صَبًّا ٢٥Lalle ne Mũ, Mun zuo ruwa, zubõwa ثُمَّ شَقَقۡنَا ٱلۡأَرۡضَ شَقًّا ٢٦Sa'an nan, Muka tsattsãge ƙasa tsattsagewa فَأَنۢبَتۡنَا فِيهَا حَبًّا ٢٧Sa'an nan, Muka tsirar da ƙwaya, a cikinta وَعِنَبًا وَقَضۡبًا ٢٨Da inabi da ciyãwa وَزَيۡتُونًا وَنَخۡلًا ٢٩Da zaitũni da itãcen dabĩno وَحَدَآئِقَ غُلۡبًا ٣٠Da lambuna, mãsu yawan itãce وَفَٰكِهَةً وَأَبًّا ٣١Da 'yã'yan itãcen marmari, da makiyãyã ta dabbõbi مَّتَٰعًا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ ٣٢Domin jin dãɗi a gare ku, ku da dabbobinku فَإِذَا جَآءَتِ ٱلصَّآخَّةُ ٣٣To, idan mai tsãwa (busa ta biyu) ta zo يَوۡمَ يَفِرُّ ٱلۡمَرۡءُ مِنۡ أَخِيهِ ٣٤Rãnar da mutum yake gudu daga ɗan'uwansa وَأُمِّهِۦ وَأَبِيهِ ٣٥Da uwarsa da ubansa وَصَٰحِبَتِهِۦ وَبَنِيهِ ٣٦Da mãtarsa da ɗiyansa لِكُلِّ ٱمۡرِيٍٕ مِّنۡهُمۡ يَوۡمَئِذٍ شَأۡنٌ يُغۡنِيهِ ٣٧Ga kõwane mutum daga cikinsu, a rãnar nan akwai wani sha'ani da ya ishe shi وُجُوهٌ يَوۡمَئِذٍ مُّسۡفِرَةٌ ٣٨Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu haske ne ضَاحِكَةٌ مُّسۡتَبۡشِرَةٌ ٣٩Mãsu dãriya ne, mãsu bushãra وَوُجُوهٌ يَوۡمَئِذٍ عَلَيۡهَا غَبَرَةٌ ٤٠Wasu huskõki, a rãnar nan, akwai ƙũra a kansu تَرۡهَقُهَا قَتَرَةٌ ٤١Baƙi zai rufe su أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡكَفَرَةُ ٱلۡفَجَرَةُ ٤٢Waɗannan sũ ne kãfirai fãjirai (ga ayyukansu)