Millat al-Islam

Chapter 89 · 30 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Fajr in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Fajr (1331 reciters)
Meccanسورة الفجر30 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلۡفَجۡرِ ١Inã rantsuwa da alfijiri وَلَيَالٍ عَشۡرٍ ٢Da darũruwa gõma وَٱلشَّفۡعِ وَٱلۡوَتۡرِ ٣Da (adadi na) cikã da (na) mãrã وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَسۡرِ ٤Da dare idan yana shũɗewa هَلۡ فِي ذَٰلِكَ قَسَمٌ لِّذِي حِجۡرٍ ٥Ko a cikin waɗannan akwai abin rantsuwa ga mai hankali (da yake kange shi daga zunubi) أَلَمۡ تَرَ كَيۡفَ فَعَلَ رَبُّكَ بِعَادٍ ٦Ba ka ga yadda Ubangijinka Ya aikata da Ãdãwa ba إِرَمَ ذَاتِ ٱلۡعِمَادِ ٧Iramawa mãsu sakon* ƙĩrar jiki ٱلَّتِي لَمۡ يُخۡلَقۡ مِثۡلُهَا فِي ٱلۡبِلَٰدِ ٨Waɗanda ba a halitta kwatankwacinsu ba a cikin garũruwa (na dũniya) وَثَمُودَ ٱلَّذِينَ جَابُواْ ٱلصَّخۡرَ بِٱلۡوَادِ ٩Da samũdãwa waɗanda suka fasa duwãtsu a cikin Wadi* suka yi gidãje وَفِرۡعَوۡنَ ذِي ٱلۡأَوۡتَادِ ١٠Da Fir'auna mai turãku ٱلَّذِينَ طَغَوۡاْ فِي ٱلۡبِلَٰدِ ١١Waɗanda suka ƙẽtare iyãkarsu, a cikin garũruwa فَأَكۡثَرُواْ فِيهَا ٱلۡفَسَادَ ١٢Sabõda haka, suka yawaita yin ɓarna a cikinsu فَصَبَّ عَلَيۡهِمۡ رَبُّكَ سَوۡطَ عَذَابٍ ١٣Sabõda haka Ubangijinka Ya zuba musu bũlãlar azãba إِنَّ رَبَّكَ لَبِٱلۡمِرۡصَادِ ١٤Lalle ne, Ubangijinka Yana nan a mafaka فَأَمَّا ٱلۡإِنسَٰنُ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ رَبُّهُۥ فَأَكۡرَمَهُۥ وَنَعَّمَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَكۡرَمَنِ ١٥To, amma fa mutum idan Ubangijibsa Ya jarraba shi, wãto Yã girmama shi kuma Ya yi masa ni'ima, sai ya ce: "Ubangijina Ya girmama ni وَأَمَّآ إِذَا مَا ٱبۡتَلَىٰهُ فَقَدَرَ عَلَيۡهِ رِزۡقَهُۥ فَيَقُولُ رَبِّيٓ أَهَٰنَنِ ١٦Kuma idan Ya jarraba shi, wãto Ya ƙuntata masa abincinsa, sai ya ce: "Ubangijina Ya walãkanta ni كـَلَّاۖ بَل لَّا تُكۡرِمُونَ ٱلۡيَتِيمَ ١٧A'aha! Bari wannan, ai bã ku girmama marãya وَلَا تَحَٰٓضُّونَ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ ١٨Bã ku kwaɗaitã wa jũnanku ga (tattalin) abincin matalauci وَتَأۡكُلُونَ ٱلتُّرَاثَ أَكۡلًا لَّمًّا ١٩Kuma kuna cin dũkiyar gãdo, ci na tãrãwa وَتُحِبُّونَ ٱلۡمَالَ حُبًّا جَمًّا ٢٠Kuma kuna son dũkiya, so mai yawa كـَلَّآۖ إِذَا دُكَّتِ ٱلۡأَرۡضُ دَكًّا دَكًّا ٢١A'aha! Idan aka niƙa ƙasa niƙewa sosai وَجَآءَ رَبُّكَ وَٱلۡمَلَكُ صَفًّا صَفًّا ٢٢Kuma Ubangijinka Ya zo, alhãli malã'iku na jẽre, sahu- sahu وَجِاْيٓءَ يَوۡمَئِذِۭ بِجَهَنَّمَۚ يَوۡمَئِذٍ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ وَأَنَّىٰ لَهُ ٱلذِّكۡرَىٰ ٢٣Kuma a ranar nan aka zo da Jahannama. A ranar nan mutum zai yi tunãni. To, inã fa tunãni yake a gare shi يَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي قَدَّمۡتُ لِحَيَاتِي ٢٤Yana dinga cẽwa, "Kaitona, dã na gabatar (da aikin ƙwarai) domin rãyuwata فَيَوۡمَئِذٍ لَّا يُعَذِّبُ عَذَابَهُۥٓ أَحَدٌ ٢٥To, a rãnar nan bãbu wani mai yin azãba irin azãbar Allah وَلَا يُوثِقُ وَثَاقَهُۥٓ أَحَدٌ ٢٦Kuma bãbu wani mai ɗauri irin ɗaurin Sa يَٰٓأَيَّتُهَا ٱلنَّفۡسُ ٱلۡمُطۡمَئِنَّةُ ٢٧Yã kai rai mai natsuwa ٱرۡجِعِيٓ إِلَىٰ رَبِّكِ رَاضِيَةً مَّرۡضِيَّةً ٢٨Ka koma zuwa ga Ubangijinka, alhãli kana mai yarda (da abin da Ya ƙaddara maka a dũniya) abar yardarwa (da sakamakon da zã a ba ka a Lãhira) فَٱدۡخُلِي فِي عِبَٰدِي ٢٩Sabõbda haka, ka shiga cikin bãyi Na (mãsu bin umurui a dũniya) وَٱدۡخُلِي جَنَّتِي ٣٠Kuma ka shiga AljannaTa (a Lãhira)

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.