Millat al-Islam

Chapter 75 · 40 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Qiyama in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Qiyama (1375 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

لَآ أُقۡسِمُ بِيَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ ١Bã sai Nã yi rantsuwa* da Rãnar ¡iyãma ba وَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلنَّفۡسِ ٱللَّوَّامَةِ ٢Bã sai Nã yi rantsuwa da rai mai yawan zargin* kansa ba أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَلَّن نَّجۡمَعَ عِظَامَهُۥ ٣Sin, mutum yana zaton cẽwa bã zã Mu tãra ƙasusuwansa ba بَلَىٰ قَٰدِرِينَ عَلَىٰٓ أَن نُّسَوِّيَ بَنَانَهُۥ ٤Na'am! Mãsu ĩkon yi Muke a kan Mu daidaita gaɓõɓin yãtsunsa بَلۡ يُرِيدُ ٱلۡإِنسَٰنُ لِيَفۡجُرَ أَمَامَهُۥ ٥Ba haka ba! Mutum so yake, ya yi fãjirci, ya ƙaryata abin da yake a gabansa يَسۡـَٔلُ أَيَّانَ يَوۡمُ ٱلۡقِيَٰمَةِ ٦Yanã tambaya: "Yaushe ne Rãnar ¡iyãma فَإِذَا بَرِقَ ٱلۡبَصَرُ ٧To, idan gani ya ɗimauta (ya yi ƙyalli) وَخَسَفَ ٱلۡقَمَرُ ٨Kuma, watã ya yi husũfi (haskensa ya dushe) وَجُمِعَ ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ ٩Aka tãra rãnã da watã يَقُولُ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذٍ أَيۡنَ ٱلۡمَفَرُّ ١٠Mutum zai ce a rãn nan "Ina wurin gudu كـَلَّا لَا وَزَرَ ١١A'aha! bãbu mafaka إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمُسۡتَقَرُّ ١٢zuwa ga Ubangijinka wurin tabbata, a rãnar nan, yake يُنَبَّؤُاْ ٱلۡإِنسَٰنُ يَوۡمَئِذِۭ بِمَا قَدَّمَ وَأَخَّرَ ١٣Ana gayã wa mutum, a rãnar nan, abin da ya gabatar da wanda ya jinkirtar بَلِ ٱلۡإِنسَٰنُ عَلَىٰ نَفۡسِهِۦ بَصِيرَةٌ ١٤Ba haka ba! Mutum, ga abin da ya shafi kansa, masani ne وَلَوۡ أَلۡقَىٰ مَعَاذِيرَهُۥ ١٥Kuma ko da yã jẽfa uzurorinsa (bã zã a saurãre shi ba) لَا تُحَرِّكۡ بِهِۦ لِسَانَكَ لِتَعۡجَلَ بِهِۦٓ ١٦Kada ka mõtsar* da harshenka game da shi dõmin ka yi gaugãwar riƙe shi (Alƙur'ãni) إِنَّ عَلَيۡنَا جَمۡعَهُۥ وَقُرۡءَانَهُۥ ١٧Lalle ne, wãjibi ne a gare Mu, Mu tãra shi. Mu (tsare maka) karãtunsa فَإِذَا قَرَأۡنَٰهُ فَٱتَّبِعۡ قُرۡءَانَهُۥ ١٨To idan Muka karanta shi sai ka bi karatunsa ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا بَيَانَهُۥ ١٩sa'an nan, lalle wãjibi ne a gare Mu, bayãninsa كـَلَّا بَلۡ تُحِبُّونَ ٱلۡعَاجِلَةَ ٢٠A'aha! Bã haka ba kunã son mai gaugawar nan (duniya) ne وَتَذَرُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ ٢١Kunã barin ta ƙarshen (Lãhira) وُجُوهٌ يَوۡمَئِذٍ نَّاضِرَةٌ ٢٢Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu annuri ne إِلَىٰ رَبِّهَا نَاظِرَةٌ ٢٣Zuwa ga Ubangijinsu mãsu kallo ne وَوُجُوهٌ يَوۡمَئِذِۭ بَاسِرَةٌ ٢٤Wasu huskõki, a rãnar nan, mãsu gintsẽwa ne تَظُنُّ أَن يُفۡعَلَ بِهَا فَاقِرَةٌ ٢٥Sunã zaton a sako musu masĩfa mai karya tsatso كـَلَّآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلتَّرَاقِيَ ٢٦A'aha! Iadan (rai) ya kai ga karankarmai وَقِيلَ مَنۡۜ رَاقٍ ٢٧kuma aka ce: "Wãne ne mai tawada وَظَنَّ أَنَّهُ ٱلۡفِرَاقُ ٢٨Kuma ya tabbata cẽwa rabuwa dai ce وَٱلۡتَفَّتِ ٱلسَّاقُ بِٱلسَّاقِ ٢٩Kuma ƙwabri ya lauye da wani ƙwabri إِلَىٰ رَبِّكَ يَوۡمَئِذٍ ٱلۡمَسَاقُ ٣٠Zuwa ga Ubangijinka, a rãnar nan, magargaɗa* take فَلَا صَدَّقَ وَلَا صَلَّىٰ ٣١To, bai gaskatã ba, kuma bai yi salla ba وَلَٰكِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ٣٢Amma dai ya ƙaryata, kuma ya jũya baya ثُمَّ ذَهَبَ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ يَتَمَطَّىٰٓ ٣٣Sa'an nan, ya tafi zuwa ga mutãnensa, yana tãƙama أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰ ٣٤Halaka tã tabbata a gare ka, sa'an nan ita ce mafi dãcewa ثُمَّ أَوۡلَىٰ لَكَ فَأَوۡلَىٰٓ ٣٥Sa'an nan, wata halaka tã tabbata a gare ka dõmin tã fi dãce wa أَيَحۡسَبُ ٱلۡإِنسَٰنُ أَن يُتۡرَكَ سُدًى ٣٦Shin, mutum nã zaton a bar shi sagaga (wãto bãbu nufin kõme game da shi) أَلَمۡ يَكُ نُطۡفَةً مِّن مَّنِيٍّ يُمۡنَىٰ ٣٧Bai kasance ɗigo na maniyyi ba, wanda ake jefarwa (a cikin mahaifa) ثُمَّ كَانَ عَلَقَةً فَخَلَقَ فَسَوَّىٰ ٣٨Sa'an nan, ya zama gudan jini, sa'an nan Allah Ya halitta shi, sa'an nan Ya daidaita gaɓõɓinsa فَجَعَلَ مِنۡهُ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ ٣٩Sa'an nan, Ya sanya daga gare shi, nau'i biyu: namiji damace أَلَيۡسَ ذَٰلِكَ بِقَٰدِرٍ عَلَىٰٓ أَن يُحۡـِۧيَ ٱلۡمَوۡتَىٰ ٤٠Ashẽ wannan bai zama Mai iko ba bisa ga rãyar da matattu

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.