Millat al-Islam

Chapter 53 · 62 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah An-Najm in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah An-Najm (1285 reciters)
Meccanسورة النجم62 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلنَّجۡمِ إِذَا هَوَىٰ ١Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمۡ وَمَا غَوَىٰ ٢Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba وَمَا يَنطِقُ عَنِ ٱلۡهَوَىٰٓ ٣Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa إِنۡ هُوَ إِلَّا وَحۡيٌ يُوحَىٰ ٤(Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa عَلَّمَهُۥ شَدِيدُ ٱلۡقُوَىٰ ٥(Malã'ika) mai tsananin ƙarfi *ya sanar da shi ذُو مِرَّةٍ فَٱسۡتَوَىٰ ٦Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita وَهُوَ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡأَعۡلَىٰ ٧Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi daukaka ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ ٨Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa فَكَانَ قَابَ قَوۡسَيۡنِ أَوۡ أَدۡنَىٰ ٩Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa فَأَوۡحَىٰٓ إِلَىٰ عَبۡدِهِۦ مَآ أَوۡحَىٰ ١٠Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa) مَا كَذَبَ ٱلۡفُؤَادُ مَا رَأَىٰٓ ١١Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba أَفَتُمَٰرُونَهُۥ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ ١٢Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani وَلَقَدۡ رَءَاهُ نَزۡلَةً أُخۡرَىٰ ١٣Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa عِندَ سِدۡرَةِ ٱلۡمُنتَهَىٰ ١٤A wurin da magaryar tuƙẽwa take عِندَهَا جَنَّةُ ٱلۡمَأۡوَىٰٓ ١٥A inda taken, nan Aljannar makoma take إِذۡ يَغۡشَى ٱلسِّدۡرَةَ مَا يَغۡشَىٰ ١٦Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta مَا زَاغَ ٱلۡبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ ١٧Ganinsa* bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba لَقَدۡ رَأَىٰ مِنۡ ءَايَٰتِ رَبِّهِ ٱلۡكُبۡرَىٰٓ ١٨Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma* daga ãyõyin Ubangijinsa أَفَرَءَيۡتُمُ ٱللَّٰتَ وَٱلۡعُزَّىٰ ١٩Shin, kun ga Lãta da uzza وَمَنَوٰةَ ٱلثَّالِثَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰٓ ٢٠Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu أَلَكُمُ ٱلذَّكَرُ وَلَهُ ٱلۡأُنثَىٰ ٢١Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace تِلۡكَ إِذًا قِسۡمَةٌ ضِيزَىٰٓ ٢٢Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe إِنۡ هِيَ إِلَّآ أَسۡمَآءٌ سَمَّيۡتُمُوهَآ أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُم مَّآ أَنزَلَ ٱللَّهُ بِهَا مِن سُلۡطَٰنٍۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّ وَمَا تَهۡوَى ٱلۡأَنفُسُۖ وَلَقَدۡ جَآءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ ٱلۡهُدَىٰٓ ٢٣Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar* ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton) أَمۡ لِلۡإِنسَٰنِ مَا تَمَنَّىٰ ٢٤Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri فَلِلَّهِ ٱلۡأٓخِرَةُ وَٱلۡأُولَىٰ ٢٥To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure) ۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ لَا تُغۡنِي شَفَٰعَتُهُمۡ شَيۡـًٔا إِلَّا مِنۢ بَعۡدِ أَن يَأۡذَنَ ٱللَّهُ لِمَن يَشَآءُ وَيَرۡضَىٰٓ ٢٦Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda إِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ لَيُسَمُّونَ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ تَسۡمِيَةَ ٱلۡأُنثَىٰ ٢٧Lalle waɗannan da bã su yin ĩmãni da Lãhira, haƙĩƙa sunã kiran malã'iku da sũnan mace وَمَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍۖ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا ٱلظَّنَّۖ وَإِنَّ ٱلظَّنَّ لَا يُغۡنِي مِنَ ٱلۡحَقِّ شَيۡـًٔا ٢٨Kuma bã su da wani ilmi game da shi, bã su bin kõme fãce zato alhãli kuwa lalle zato bã ya amfãnar da kõme daga gaskiya فَأَعۡرِضۡ عَن مَّن تَوَلَّىٰ عَن ذِكۡرِنَا وَلَمۡ يُرِدۡ إِلَّا ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا ٢٩Sabõda haka sai ka kau da kai daga wanda ya jũya bãya daga ambaton Mu kuma bai yi nufin kõme ba fãce rãyuwar kusa (dũniya) ذَٰلِكَ مَبۡلَغُهُم مِّنَ ٱلۡعِلۡمِۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱهۡتَدَىٰ ٣٠Wannan ita ce iyãkar abin da suke iya kai gare shi na ilmi. lalle Ubangijinka Shĩ ne Mafi sanin wanda ya ɓace daga hanyar Sa, kuma Shi ne Mafi sani ga wanda ya nẽmi shiriya وَلِلَّهِ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِ لِيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَسَٰٓـُٔواْ بِمَا عَمِلُواْ وَيَجۡزِيَ ٱلَّذِينَ أَحۡسَنُواْ بِٱلۡحُسۡنَى ٣١Kuma abin da ke cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã na Allah kawai ne, dõmin Yã sãka wa waɗanda suka mũnana da abin da suka aikata, kuma Ya sãka wa waɗanda suki kyautata da sakamakon da ya fi kyau ٱلَّذِينَ يَجۡتَنِبُونَ كَبَٰٓئِرَ ٱلۡإِثۡمِ وَٱلۡفَوَٰحِشَ إِلَّا ٱللَّمَمَۚ إِنَّ رَبَّكَ وَٰسِعُ ٱلۡمَغۡفِرَةِۚ هُوَ أَعۡلَمُ بِكُمۡ إِذۡ أَنشَأَكُم مِّنَ ٱلۡأَرۡضِ وَإِذۡ أَنتُمۡ أَجِنَّةٌ فِي بُطُونِ أُمَّهَٰتِكُمۡۖ فَلَا تُزَكُّوٓاْ أَنفُسَكُمۡۖ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَنِ ٱتَّقَىٰٓ ٣٢Waɗanda ke nĩsantar manyan zunubai da abũbuwan alfãsha, fãce ƙanãnan laifuffuka, lalle Ubangijinka Mai yalwatattar gãfara ne, Shĩ ne Ya fi sani ga abinda ke gare ku a lõkacin da Ya ƙãga halittarku daga ƙasa, kuma a lõkacin da kuke tãyuna a cikin cikannan uwãyenku. Sabõda haka, kada ku tsarkake* kanku, Shĩ ne Mafi sani ga wanda ya yi taƙawa أَفَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي تَوَلَّىٰ ٣٣Shin, ka ga wannan da ya jũya baya وَأَعۡطَىٰ قَلِيلًا وَأَكۡدَىٰٓ ٣٤Ya yi kyauta kaɗan, kuma ya yi rowa أَعِندَهُۥ عِلۡمُ ٱلۡغَيۡبِ فَهُوَ يَرَىٰٓ ٣٥Shin, akwai ilmin gaibi a wurinsa, Sabõda haka yanã ganin gaibin أَمۡ لَمۡ يُنَبَّأۡ بِمَا فِي صُحُفِ مُوسَىٰ ٣٦Ko kuwa ba a ba shi lãbãri ba ga abin da yake a cikin Littafan Mũsã وَإِبۡرَٰهِيمَ ٱلَّذِي وَفَّىٰٓ ٣٧Da Ibrãhĩm wanda ya cika alkawari أَلَّا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزۡرَ أُخۡرَىٰ ٣٨Cẽwa wani rai mai kãyan laifi bã ya ɗaukar kãyan laifin wani وَأَن لَّيۡسَ لِلۡإِنسَٰنِ إِلَّا مَا سَعَىٰ ٣٩Kuma mutum bã shi da kõme fãce abin da ya aikata وَأَنَّ سَعۡيَهُۥ سَوۡفَ يُرَىٰ ٤٠Kuma lalle, aikinsa zã a gan shi ثُمَّ يُجۡزَىٰهُ ٱلۡجَزَآءَ ٱلۡأَوۡفَىٰ ٤١Sa'an nan a sãka masa da sakamako wanda yake mafi cikar ma'auni وَأَنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلۡمُنتَهَىٰ ٤٢Kuma lalle, makõmar zuwa Ubangijinka kawai take وَأَنَّهُۥ هُوَ أَضۡحَكَ وَأَبۡكَىٰ ٤٣Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya sanya dariya, kuma Ya sanya kũka وَأَنَّهُۥ هُوَ أَمَاتَ وَأَحۡيَا ٤٤Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya kashe, kuma Ya rãyar وَأَنَّهُۥ خَلَقَ ٱلزَّوۡجَيۡنِ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰ ٤٥Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace مِن نُّطۡفَةٍ إِذَا تُمۡنَىٰ ٤٦Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa وَأَنَّ عَلَيۡهِ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُخۡرَىٰ ٤٧Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take وَأَنَّهُۥ هُوَ أَغۡنَىٰ وَأَقۡنَىٰ ٤٨Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar وَأَنَّهُۥ هُوَ رَبُّ ٱلشِّعۡرَىٰ ٤٩Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira وَأَنَّهُۥٓ أَهۡلَكَ عَادًا ٱلۡأُولَىٰ ٥٠Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko وَثَمُودَاْ فَمَآ أَبۡقَىٰ ٥١Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba وَقَوۡمَ نُوحٍ مِّن قَبۡلُۖ إِنَّهُمۡ كَانُواْ هُمۡ أَظۡلَمَ وَأَطۡغَىٰ ٥٢Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai وَٱلۡمُؤۡتَفِكَةَ أَهۡوَىٰ ٥٣Da waɗanda aka birkice *ƙasarsu, Ya kãyar da su فَغَشَّىٰهَا مَا غَشَّىٰ ٥٤Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ ٥٥To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake *yin shakka هَٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ ٱلنُّذُرِ ٱلۡأُولَىٰٓ ٥٦wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko أَزِفَتِ ٱلۡأٓزِفَةُ ٥٧Makusanciya* fa, tã yi kusa لَيۡسَ لَهَا مِن دُونِ ٱللَّهِ كَاشِفَةٌ ٥٨Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta أَفَمِنۡ هَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ تَعۡجَبُونَ ٥٩Shin, kuma daga wannan *lãbãri kuke mãmãki وَتَضۡحَكُونَ وَلَا تَبۡكُونَ ٦٠Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka وَأَنتُمۡ سَٰمِدُونَ ٦١Alhãli kunã mãsu wãsã فَٱسۡجُدُواْۤ لِلَّهِۤ وَٱعۡبُدُواْ ۩ ٦٢To, ku yi tawãli'u *ga Allah, kuma ku bauta (masa)

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.