ملة الإسلام

السورة 96 · 19 آية · Abubakar Mahmood Jummi

سورة العلق باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة العلق (1,283 قارئاً)
مكيةسورة العلق١٩ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱقۡرَأۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلَّذِي خَلَقَ ١Ka yi karatu da sunan Ubangijinka, wanda Ya yi halitta خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِنۡ عَلَقٍ ٢Ya hahitta mutum daga gudan jini ٱقۡرَأۡ وَرَبُّكَ ٱلۡأَكۡرَمُ ٣Ka yi karatu, kuma Ubangijinka shi ne Mafi karimci ٱلَّذِي عَلَّمَ بِٱلۡقَلَمِ ٤Wanda Ya sanar (da mutum) game da alƙalami عَلَّمَ ٱلۡإِنسَٰنَ مَا لَمۡ يَعۡلَمۡ ٥Ya sanar da mutum abin da bai sani ba كـَلَّآ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ لَيَطۡغَىٰٓ ٦A'aha! Lalle, ne mutum haƙĩƙa, yana girman kai (ya ƙi karatu) أَن رَّءَاهُ ٱسۡتَغۡنَىٰٓ ٧Dõmin yã ga kansa, yã wadãta إِنَّ إِلَىٰ رَبِّكَ ٱلرُّجۡعَىٰٓ ٨Lalle ne zuwa ga Ubangijinka makoma take أَرَءَيۡتَ ٱلَّذِي يَنۡهَىٰ ٩Shin, kã ga wanda ke hana عَبۡدًا إِذَا صَلَّىٰٓ ١٠Bãwã idan yã yi salla أَرَءَيۡتَ إِن كَانَ عَلَى ٱلۡهُدَىٰٓ ١١Ashe, kã gani, idan (shi bãwan) ya kasance a kan shiriya أَوۡ أَمَرَ بِٱلتَّقۡوَىٰٓ ١٢Ko ya yi umurni da taƙawa أَرَءَيۡتَ إِن كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰٓ ١٣Ashe, kã gani, idan (shi mai hanin) ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya أَلَمۡ يَعۡلَم بِأَنَّ ٱللَّهَ يَرَىٰ ١٤Ashe, bai sani ba cewa Allah Yanã gani كـَلَّا لَئِن لَّمۡ يَنتَهِ لَنَسۡفَعَۢا بِٱلنَّاصِيَةِ ١٥A'aha! Lalle ne, idan bai hanu ba, lalle ne zã Mu ja gãshin makwarkwaɗa نَاصِيَةٍ كَٰذِبَةٍ خَاطِئَةٍ ١٦Makwarkwaɗa maƙaryaciya, mai laifi فَلۡيَدۡعُ نَادِيَهُۥ ١٧Sai ya kirayi ƙungiyarsa سَنَدۡعُ ٱلزَّبَانِيَةَ ١٨Zã Mu kirayi zabaniyãwa (mala'iku mãsu girma) كـَلَّا لَا تُطِعۡهُ وَٱسۡجُدۡۤ وَٱقۡتَرِب ۩ ١٩A'aha kada ka bĩ shi. Kuma ka yi tawali'u,* kuma ka nemi kusanta (zuwa ga Ubangijinka)

الترجمة: Abubakar Mahmood Jummi.