بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
لَآ أُقۡسِمُ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ١Bã sai Na yi rantsuwa da wannan gari* ba وَأَنتَ حِلُّۢ بِهَٰذَا ٱلۡبَلَدِ ٢Alhãli kai kanã mai sauka a cikin wannan gari وَوَالِدٍ وَمَا وَلَدَ ٣Da mahaifi da abin da ya haifa لَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ فِي كَبَدٍ ٤Lalle ne, Mun halitta mutum cikin wahala أَيَحۡسَبُ أَن لَّن يَقۡدِرَ عَلَيۡهِ أَحَدٌ ٥Kõ yanã zaton bãbu wani mai iya sãmun iko, a kansa يَقُولُ أَهۡلَكۡتُ مَالًا لُّبَدًا ٦Yana cẽwa "Na* halakarda dũkiya mai yawa أَيَحۡسَبُ أَن لَّمۡ يَرَهُۥٓ أَحَدٌ ٧Shin, yana zaton cewa wani bai gan shi ba أَلَمۡ نَجۡعَل لَّهُۥ عَيۡنَيۡنِ ٨Shin, ba Mu sanya masa idãnu biyu ba وَلِسَانًا وَشَفَتَيۡنِ ٩Da harshe, da leɓɓa biyu وَهَدَيۡنَٰهُ ٱلنَّجۡدَيۡنِ ١٠Kuma ba Mu shiryar da shi ga hanyõyi* biyu ba فَلَا ٱقۡتَحَمَ ٱلۡعَقَبَةَ ١١To, don mene ne bai shiga Aƙabã ba وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡعَقَبَةُ ١٢Kuma mene ne ya sanar da kai abin da ake cẽ wa Aƙabã فَكُّ رَقَبَةٍ ١٣Ita ce fansar wuyan bãwa أَوۡ إِطۡعَٰمٌ فِي يَوۡمٍ ذِي مَسۡغَبَةٍ ١٤Ko kuwa ciyarwa, a cikin yini ma'abũcin yunwa يَتِيمًا ذَا مَقۡرَبَةٍ ١٥Ga marãya ma'abũcin zumunta أَوۡ مِسۡكِينًا ذَا مَتۡرَبَةٍ ١٦Ko kuwa wani matalauci ma'abũcin turɓãya ثُمَّ كَانَ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلصَّبۡرِ وَتَوَاصَوۡاْ بِٱلۡمَرۡحَمَةِ ١٧Sa'an nan kuma ya kasance daga waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi wa jũna wasiyya da yin haƙuri, kuma suka yi wa jũna wasiyya da tausayi أُوْلَٰٓئِكَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ ١٨Waɗannan ne ma'abũta albarka وَٱلَّذِينَ كَفَرُواْ بِـَٔايَٰتِنَا هُمۡ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ ١٩Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Mu, sũ ne ma'abũta shu'umci عَلَيۡهِمۡ نَارٌ مُّؤۡصَدَةُۢ ٢٠A kansu akwai wata wuta abar kullewa