بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡغَٰشِيَةِ ١Lalle ne labãrin (¡iyãma) mai rufe mutãne da tsoronta yã zo maka وُجُوهٌ يَوۡمَئِذٍ خَٰشِعَةٌ ٢Wasu huskõki a rãnar nan ƙasƙantattu ne عَامِلَةٌ نَّاصِبَةٌ ٣Mãsu aikin wahala ne, mãsu gajiya تَصۡلَىٰ نَارًا حَامِيَةً ٤Zã su shiga wata wuta mai zãfi تُسۡقَىٰ مِنۡ عَيۡنٍ ءَانِيَةٍ ٥Ana shãyar da su daga wani marmaro mai zãfin ruwa لَّيۡسَ لَهُمۡ طَعَامٌ إِلَّا مِن ضَرِيعٍ ٦Ba su da wani abinci fãce dai daga danyi لَّا يُسۡمِنُ وَلَا يُغۡنِي مِن جُوعٍ ٧Bã ya sanya ƙiba, kuma bã zai wadãtar daga yunwa ba وُجُوهٌ يَوۡمَئِذٍ نَّاعِمَةٌ ٨Wasu huskõki a rãnar nan mãsu ni'ima ne لِّسَعۡيِهَا رَاضِيَةٌ ٩Game da aikinsu, masu yarda ne فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ ١٠(Suna) a cikin Aljanna maɗaukakiya لَّا تَسۡمَعُ فِيهَا لَٰغِيَةً ١١Bã zã su ji yãsassar magana ba, a cikinta فِيهَا عَيۡنٌ جَارِيَةٌ ١٢A cikinta akwai marmaro mai gudãna فِيهَا سُرُرٌ مَّرۡفُوعَةٌ ١٣A cikinta akwai gadãje maɗaukaka وَأَكۡوَابٌ مَّوۡضُوعَةٌ ١٤Da kõfuna ar'aje وَنَمَارِقُ مَصۡفُوفَةٌ ١٥Da filõli* jẽre وَزَرَابِيُّ مَبۡثُوثَةٌ ١٦Da katifu shimfiɗe أَفَلَا يَنظُرُونَ إِلَى ٱلۡإِبِلِ كَيۡفَ خُلِقَتۡ ١٧Ashe to bã zã su dũbãwa ba ga rãƙumã yadda aka halitta su وَإِلَى ٱلسَّمَآءِ كَيۡفَ رُفِعَتۡ ١٨Da zuwa ga sama yadda aka ɗaukaka ta وَإِلَى ٱلۡجِبَالِ كَيۡفَ نُصِبَتۡ ١٩Da zuwa ga duwãtsu yadda aka kafa su وَإِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَيۡفَ سُطِحَتۡ ٢٠Da zuwa ga ƙasa yadda aka shimfiɗã ta فَذَكِّرۡ إِنَّمَآ أَنتَ مُذَكِّرٌ ٢١sabõda haka, ka yi wa'azi, kai mai yin wa'azi ne kawai لَّسۡتَ عَلَيۡهِم بِمُصَيۡطِرٍ ٢٢Ba ka zama mai ĩkon tanƙwasãwa a kansu ba إِلَّا مَن تَوَلَّىٰ وَكَفَرَ ٢٣Fãce dai duk wanda ya jũya bãya, kuma ya kãfirta فَيُعَذِّبُهُ ٱللَّهُ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَكۡبَرَ ٢٤To, Allah zai yi masa azãba, azãbar nan da take mafi girma إِنَّ إِلَيۡنَآ إِيَابَهُمۡ ٢٥Lalle ne, zuwa gare Mu kõmõwarsu take ثُمَّ إِنَّ عَلَيۡنَا حِسَابَهُم ٢٦Sa'an nan lalle ne aikinMu ne Mu yi musu hisãbi