ملة الإسلام

السورة 77 · 50 آية · Abubakar Mahmood Jummi

سورة المرسلات باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة المرسلات (1,226 قارئاً)
مكيةسورة المرسلات٥٠ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلۡمُرۡسَلَٰتِ عُرۡفًا ١Ina rantsuwa da iskõkin da ake sakõwa jẽre, sunã bin jũna فَٱلۡعَٰصِفَٰتِ عَصۡفًا ٢Sa'an nan, su zamã iskõki mãsu ƙarfi suna kaɗãwa da ƙarfi وَٱلنَّٰشِرَٰتِ نَشۡرًا ٣Kuma, mãsu watsa rahama wãtsãwa فَٱلۡفَٰرِقَٰتِ فَرۡقًا ٤sa'an nan, da ãyõyi* mãsu rarrabe gaskiya da ƙarya rarrabẽwa فَٱلۡمُلۡقِيَٰتِ ذِكۡرًا ٥Sa'an nan da malã'iku mãsu jẽfa tunãtarwa ga Manzanni عُذۡرًا أَوۡ نُذۡرًا ٦Domin yanke hamzari ko dõmin gargadi إِنَّمَا تُوعَدُونَ لَوَٰقِعٌ ٧Lalle ne, abin da ake yi muku wa'adi da shi tabbas mai aukuwa ne فَإِذَا ٱلنُّجُومُ طُمِسَتۡ ٨To, idan taurãri aka shãfe haskensu وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ فُرِجَتۡ ٩Kuma, idan sama aka tsãge ta وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ نُسِفَتۡ ١٠Kuma, idan duwãtsu aka nike su وَإِذَا ٱلرُّسُلُ أُقِّتَتۡ ١١Kuma, idan manzanni aka ƙayyade lõkacin tãra su لِأَيِّ يَوۡمٍ أُجِّلَتۡ ١٢Domin babbar rãnar da aka yi wa ajali لِيَوۡمِ ٱلۡفَصۡلِ ١٣Domin rãnar rarrabẽwa وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ١٤Kuma, me ya sanar da kai rãnar rarrabẽwa وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ١٥Bone yã tabbata a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa أَلَمۡ نُهۡلِكِ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٦Ashe, ba Mu halakar da (mãsu ƙaryatãw) na farko ba ثُمَّ نُتۡبِعُهُمُ ٱلۡأٓخِرِينَ ١٧Sa'an nan, kuma zã Mu biyar musu da na ƙarshe كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ ١٨Haka nan, Muke aikatãwa da mãsu yin laifi وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ١٩Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa أَلَمۡ نَخۡلُقكُّم مِّن مَّآءٍ مَّهِينٍ ٢٠Ashe, ba Mu halitta ku daga wani ruwa wulakantacce ba فَجَعَلۡنَٰهُ فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ ٢١Sa'an nan Muka sanya shi a cikin wani wurin natsuwa amintacce إِلَىٰ قَدَرٍ مَّعۡلُومٍ ٢٢Zuwa ga wani gwargwadon mudda sananna فَقَدَرۡنَا فَنِعۡمَ ٱلۡقَٰدِرُونَ ٢٣Sa'an nan, Muka nũna iyãwar Mu? Madalla da Mu, Mãsu nũna iyãwa وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٢٤Bone ya tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ كِفَاتًا ٢٥Ashe, ba Mu sanya ƙasa matattarã ba أَحۡيَآءً وَأَمۡوَٰتًا ٢٦Ga rãyayyu da matattu وَجَعَلۡنَا فِيهَا رَوَٰسِيَ شَٰمِخَٰتٍ وَأَسۡقَيۡنَٰكُم مَّآءً فُرَاتًا ٢٧Kuma, Muka sanya, a cikinta, kafaffun duwãtsu maɗaukaka, kuma Muka shayar da ku ruwa mai dãɗi وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٢٨Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ مَا كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ٢٩Ku tafi zuwa ga abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi ٱنطَلِقُوٓاْ إِلَىٰ ظِلٍّ ذِي ثَلَٰثِ شُعَبٍ ٣٠Ku tafi zuwa ga wata inuwa mai rassa uku لَّا ظَلِيلٍ وَلَا يُغۡنِي مِنَ ٱللَّهَبِ ٣١Ita ba inuwar ba, kuma ba ta wadãtarwa daga harshen wuta إِنَّهَا تَرۡمِي بِشَرَرٍ كَٱلۡقَصۡرِ ٣٢Lalle ne, ita, tanã jifã da tartsatsi kamar sõraye كَأَنَّهُۥ جِمَٰلَتٌ صُفۡرٌ ٣٣Kamar dai su raƙumma ne baƙãƙe وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٣٤Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa هَٰذَا يَوۡمُ لَا يَنطِقُونَ ٣٥Wannan, yini ne da bã zã su iya yin magana ba وَلَا يُؤۡذَنُ لَهُمۡ فَيَعۡتَذِرُونَ ٣٦Bã zã a yi musu izni ba, balle su kãwo hanzari وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٣٧Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِۖ جَمَعۡنَٰكُمۡ وَٱلۡأَوَّلِينَ ٣٨Wannan rãnar rarrabẽwa ce, Mun tattara ku tare da mutãnen farko فَإِن كَانَ لَكُمۡ كَيۡدٌ فَكِيدُونِ ٣٩To, idan akwai wata dabara gare ku, sai ku yi ma Ni ita وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٤٠Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa إِنَّ ٱلۡمُتَّقِينَ فِي ظِلَٰلٍ وَعُيُونٍ ٤١Lalle ne, mãsu taƙawa suna a cikin inuwõwi da marẽmari وَفَوَٰكِهَ مِمَّا يَشۡتَهُونَ ٤٢Da wasu 'ya'yan itãce irin waɗanda suke marmari كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ٤٣(A ce musu) "Ku ci ku sha cikin ni'ima sabõda abin da kuka kasance kuna aikatãwa إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ٤٤Lalle ne, Mũ haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٤٥Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa كُلُواْ وَتَمَتَّعُواْ قَلِيلًا إِنَّكُم مُّجۡرِمُونَ ٤٦(Ana ce musu) "Ku ci ku ji ɗan dãdi kaɗan, lalle ne dai ku mãsu laifi ne وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٤٧Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa وَإِذَا قِيلَ لَهُمُ ٱرۡكَعُواْ لَا يَرۡكَعُونَ ٤٨Kuma, idan an ce musu: "Ku yi rukũ'i; bã zã su yi rukũ'in (salla) ba وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ٤٩Bone ya tabbata, a rãnar nan, ga mãsu ƙaryatãwa فَبِأَيِّ حَدِيثِۭ بَعۡدَهُۥ يُؤۡمِنُونَ ٥٠To, da wane lãbãri (Littãfi), waninsa (Alƙur'ãni) zã su yi ĩmãni

الترجمة: Abubakar Mahmood Jummi.