ملة الإسلام

السورة 79 · 46 آية · Abubakar Mahmood Jummi

سورة النازعات باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة النازعات (1,353 قارئاً)
مكيةسورة النازعات٤٦ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلنَّٰزِعَٰتِ غَرۡقًا ١Ina rantsuwa da mala'iku mãsu fisgar rãyuka (na kafirai) da ƙarfi وَٱلنَّٰشِطَٰتِ نَشۡطًا ٢Da mãsu ɗibar rãyuka (na mũminai) da sauƙi a cikin nishãɗi وَٱلسَّٰبِحَٰتِ سَبۡحًا ٣Da mãsu sauka daga sama da umurnin Allah kamar suna iyo فَٱلسَّٰبِقَٰتِ سَبۡقًا ٤Sa'an nan, su zama mãsu gaugãwa (da umarnin Allah) kamar suna tsẽre فَٱلۡمُدَبِّرَٰتِ أَمۡرًا ٥Sa, an nan, su kasance masu shirya gudanar da umarni يَوۡمَ تَرۡجُفُ ٱلرَّاجِفَةُ ٦Rãnar da mai girgiza abũbuwa (bũsar farko) zã ta kaɗa تَتۡبَعُهَا ٱلرَّادِفَةُ ٧Mai biyar ta (bũsa ta biyu) nã biye قُلُوبٌ يَوۡمَئِذٍ وَاجِفَةٌ ٨Wasu zukãta, a rãnar nan, mãsu jin tsõro ne أَبۡصَٰرُهَا خَٰشِعَةٌ ٩Alhãli idãnunsu na ƙasƙantattu يَقُولُونَ أَءِنَّا لَمَرۡدُودُونَ فِي ٱلۡحَافِرَةِ ١٠Sunã cẽwa "Ashe lalle zã a iya mayar da mu a kan sãwunmu أَءِذَا كُنَّا عِظَٰمًا نَّخِرَةً ١١Ashe, idan muka zama ƙasusuwa rududdugaggu قَالُواْ تِلۡكَ إِذًا كَرَّةٌ خَاسِرَةٌ ١٢Suka ce: "Waccan kam kõmãwa ce, tãɓaɓɓiya فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٌ وَٰحِدَةٌ ١٣To, ita kam, tsãwa guda kawai ce فَإِذَا هُم بِٱلسَّاهِرَةِ ١٤Sai kawai gã su a bãyan ƙasa هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ مُوسَىٰٓ ١٥Shin, lãbãrin Mũsã ya zo maka إِذۡ نَادَىٰهُ رَبُّهُۥ بِٱلۡوَادِ ٱلۡمُقَدَّسِ طُوًى ١٦A lõkacin da Ubangijinsa Ya kirãye shi, a cikin kwari mai tsarki, wato Duwã ٱذۡهَبۡ إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ إِنَّهُۥ طَغَىٰ ١٧Ka tafi zuwa ga Fir'auna, lalle ne shi, ya ƙẽtare haddi فَقُلۡ هَل لَّكَ إِلَىٰٓ أَن تَزَكَّىٰ ١٨Sai ka ce masa, Kõ zã ka so ka tsarkaka وَأَهۡدِيَكَ إِلَىٰ رَبِّكَ فَتَخۡشَىٰ ١٩Kuma in shiryar da kai zuwa ga Ubangijinka domin ka ji tsoron Sa فَأَرَىٰهُ ٱلۡأٓيَةَ ٱلۡكُبۡرَىٰ ٢٠Sai ya nũna masa ãyar* nan mafi girma فَكَذَّبَ وَعَصَىٰ ٢١Sai ya ƙaryata, kuma ya sãɓa (umurni) ثُمَّ أَدۡبَرَ يَسۡعَىٰ ٢٢Sa'an nan ya jũya bãya, yanã tafiya da sauri فَحَشَرَ فَنَادَىٰ ٢٣Sai ya yi gayya, sa'an nan ya yi kira فَقَالَ أَنَا۠ رَبُّكُمُ ٱلۡأَعۡلَىٰ ٢٤Sai ya ce: "Nĩ ne Ubangijinku mafi ɗaudaka فَأَخَذَهُ ٱللَّهُ نَكَالَ ٱلۡأٓخِرَةِ وَٱلۡأُولَىٰٓ ٢٥Sabõda haka Allah Ya kama shi, dõmin azãbar maganar ƙarshe da ta farko إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَعِبۡرَةً لِّمَن يَخۡشَىٰٓ ٢٦Lalle ne, a cikin wannan haƙiƙa akwai abin kula ga wanda yake tsõron Allah ءَأَنتُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَمِ ٱلسَّمَآءُۚ بَنَىٰهَا ٢٧Shin, kũ ne mafi wuyar halitta ko sama? Allah Ya gina ta رَفَعَ سَمۡكَهَا فَسَوَّىٰهَا ٢٨Ya ɗaukaka rufinta, sa'an nan Ya daidaita ta وَأَغۡطَشَ لَيۡلَهَا وَأَخۡرَجَ ضُحَىٰهَا ٢٩Kuma Ya duhuntar da darenta, kuma Ya fitar da hantsinta وَٱلۡأَرۡضَ بَعۡدَ ذَٰلِكَ دَحَىٰهَآ ٣٠Kuma, ƙasa a bayan haka Ya mulmula ta أَخۡرَجَ مِنۡهَا مَآءَهَا وَمَرۡعَىٰهَا ٣١Ya fitar da ruwanta daga gare ta da makiyãyarta وَٱلۡجِبَالَ أَرۡسَىٰهَا ٣٢Da duwatsu, Yã kafe ta مَتَٰعًا لَّكُمۡ وَلِأَنۡعَٰمِكُمۡ ٣٣Domin jiyarwa dãɗi a gare ku, kuma ga dabbõbinku فَإِذَا جَآءَتِ ٱلطَّآمَّةُ ٱلۡكُبۡرَىٰ ٣٤To, idan uwar masĩfu, mafi girma, ta zo يَوۡمَ يَتَذَكَّرُ ٱلۡإِنسَٰنُ مَا سَعَىٰ ٣٥Rãnar da mutum zai yi tunãnin abin da ya aikata وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِمَن يَرَىٰ ٣٦Kuma, a bayyana Jahĩm ga mai gani فَأَمَّا مَن طَغَىٰ ٣٧To, amma wanda ya yi girman kai وَءَاثَرَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا ٣٨Kuma, ya zãɓi rãyuwa ta kusa, (wato dũniya) فَإِنَّ ٱلۡجَحِيمَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ٣٩To, lalle ne Jahĩm, ita ce makõma وَأَمَّا مَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ وَنَهَى ٱلنَّفۡسَ عَنِ ٱلۡهَوَىٰ ٤٠Kuma, amma wanda ya ji tsõron tsayi a gaba ga Ubangijinsa, kuma ya kange kansa daga son rai فَإِنَّ ٱلۡجَنَّةَ هِيَ ٱلۡمَأۡوَىٰ ٤١To, lalle ne Aljanna ita ce makõma يَسۡـَٔلُونَكَ عَنِ ٱلسَّاعَةِ أَيَّانَ مُرۡسَىٰهَا ٤٢Sunã tambayar ka game da sa'a, wai yaushe ne matabbatarta فِيمَ أَنتَ مِن ذِكۡرَىٰهَآ ٤٣Me ya haɗã ka da ambatonta إِلَىٰ رَبِّكَ مُنتَهَىٰهَآ ٤٤Zuwa ga Ubangijinka ƙarshen al'amarinta yake إِنَّمَآ أَنتَ مُنذِرُ مَن يَخۡشَىٰهَا ٤٥Kai mai gargaɗi kawai ne ga mai tsõron ta كَأَنَّهُمۡ يَوۡمَ يَرَوۡنَهَا لَمۡ يَلۡبَثُوٓاْ إِلَّا عَشِيَّةً أَوۡ ضُحَىٰهَا ٤٦Kamar sũ a rãnar da zã su gan ta, ba su zauna ba fãce a lõkacin marẽce ko hantsinsa

الترجمة: Abubakar Mahmood Jummi.