ملة الإسلام

السورة 26 · 227 آية · Abubakar Mahmood Jummi

سورة الشعراء باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة الشعراء (1,209 قارئاً)
مكيةسورة الشعراء٢٢٧ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

طسٓمٓ ١S̃. M̃ تِلۡكَ ءَايَٰتُ ٱلۡكِتَٰبِ ٱلۡمُبِينِ ٢Waɗancan ãyõyin Littãfi ne bayyananne لَعَلَّكَ بَٰخِعٌ نَّفۡسَكَ أَلَّا يَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ ٣Tsammãninka kai mai zaka halakar da ranka ne, dõn ba su zamanto mũminai ba إِن نَّشَأۡ نُنَزِّلۡ عَلَيۡهِم مِّنَ ٱلسَّمَآءِ ءَايَةً فَظَلَّتۡ أَعۡنَٰقُهُمۡ لَهَا خَٰضِعِينَ ٤Idan Mun so zã Mu saukar, a kansu, da wata ãyã daga sama, sai wuyõyinsu su yini sabõda ita sunã mãsu ƙasƙantar da kai وَمَا يَأۡتِيهِم مِّن ذِكۡرٍ مِّنَ ٱلرَّحۡمَٰنِ مُحۡدَثٍ إِلَّا كَانُواْ عَنۡهُ مُعۡرِضِينَ ٥Kuma wata tunãtarwa ba ta jẽ musu ba, daga Mai rahama, sãbuwa, fãce sun kasance daga barinta sunã mãsu bijirẽwa فَقَدۡ كَذَّبُواْ فَسَيَأۡتِيهِمۡ أَنۢبَٰٓؤُاْ مَا كَانُواْ بِهِۦ يَسۡتَهۡزِءُونَ ٦To, lalle ne, sun ƙaryata, to, lãbãran abin da suka kasance sunã yi na izgili da shi zã ya je musu أَوَلَمۡ يَرَوۡاْ إِلَى ٱلۡأَرۡضِ كَمۡ أَنۢبَتۡنَا فِيهَا مِن كُلِّ زَوۡجٍ كَرِيمٍ ٧Shin, ba su dũba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ٨Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mũminai ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ٩Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai rahama وَإِذۡ نَادَىٰ رَبُّكَ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱئۡتِ ٱلۡقَوۡمَ ٱلظَّٰلِمِينَ ١٠Kuma a lõkacin da Ubangijinka Ya kirãyi Mũsã, "Ka je wa mutãnen nan azzãlumai قَوۡمَ فِرۡعَوۡنَۚ أَلَا يَتَّقُونَ ١١Mutãnen Fir'auna bã zã su yi taƙawa ba قَالَ رَبِّ إِنِّيٓ أَخَافُ أَن يُكَذِّبُونِ ١٢Ya ce: "Ya Ubangijĩna, nĩ inã tsõron su ƙaryata ni وَيَضِيقُ صَدۡرِي وَلَا يَنطَلِقُ لِسَانِي فَأَرۡسِلۡ إِلَىٰ هَٰرُونَ ١٣Kuma ƙirjĩna ya yi ƙunci* kuma harshẽna bã zai saku ba sabõda haka ka aika zuwa ga Harũna وَلَهُمۡ عَلَيَّ ذَنۢبٌ فَأَخَافُ أَن يَقۡتُلُونِ ١٤Kuma sunã da wani laifi a kaina, sabõda haka inã tsõron kada su kashe ni قَالَ كـَلَّاۖ فَٱذۡهَبَا بِـَٔايَٰتِنَآۖ إِنَّا مَعَكُم مُّسۡتَمِعُونَ ١٥Ya ce: "Kayya! Ku tafi, kũ biyu, da ÃyõyinMu. Lalle ne, Munã tãre da ku Munã Mãsu saurãre فَأۡتِيَا فِرۡعَوۡنَ فَقُولَآ إِنَّا رَسُولُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٦Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne أَنۡ أَرۡسِلۡ مَعَنَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ١٧Ka saki Banĩ Isrã'ila tãre da mu قَالَ أَلَمۡ نُرَبِّكَ فِينَا وَلِيدًا وَلَبِثۡتَ فِينَا مِنۡ عُمُرِكَ سِنِينَ ١٨Ya ce: "Shin, ba mu yi rẽnonka ba a cikinmu kanã jãrĩri, kuma ka zauna a cikinmu shẽkarudaga lõkacin rãyuwarka وَفَعَلۡتَ فَعۡلَتَكَ ٱلَّتِي فَعَلۡتَ وَأَنتَ مِنَ ٱلۡكَٰفِرِينَ ١٩Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhãli kai kanã daga butulai قَالَ فَعَلۡتُهَآ إِذًا وَأَنَا۠ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ ٢٠Ya ce: "Na aikata shi a lõkacin inã daga mãsu jãhilcin fushi فَفَرَرۡتُ مِنكُمۡ لَمَّا خِفۡتُكُمۡ فَوَهَبَ لِي رَبِّي حُكۡمًا وَجَعَلَنِي مِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ٢١Sabõda haka na gudu daga gãre ku a lõkacin da na ji tsõronku, sai Ubangijĩna Ya bã ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni وَتِلۡكَ نِعۡمَةٌ تَمُنُّهَا عَلَيَّ أَنۡ عَبَّدتَّ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٢٢Kuma waccan ni'ima ce, kanã gõrint a kaina, dõmin kã bautar da Banĩ Isrã'ĩla قَالَ فِرۡعَوۡنُ وَمَا رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٢٣Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu قَالَ رَبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُم مُّوقِنِينَ ٢٤Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu ƙarfin ĩmãni قَالَ لِمَنۡ حَوۡلَهُۥٓ أَلَا تَسۡتَمِعُونَ ٢٥Ya ce wa waɗanda suke a gẽfensa, "Bã za ku saurãra ba قَالَ رَبُّكُمۡ وَرَبُّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٢٦Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko قَالَ إِنَّ رَسُولَكُمُ ٱلَّذِيٓ أُرۡسِلَ إِلَيۡكُمۡ لَمَجۡنُونٌ ٢٧Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne قَالَ رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقِ وَٱلۡمَغۡرِبِ وَمَا بَيۡنَهُمَآۖ إِن كُنتُمۡ تَعۡقِلُونَ ٢٨Ya ce: "Ubangijin mafitar rãnã da maɓũyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kunã hankalta قَالَ لَئِنِ ٱتَّخَذۡتَ إِلَٰهًا غَيۡرِي لَأَجۡعَلَنَّكَ مِنَ ٱلۡمَسۡجُونِينَ ٢٩Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautãwa wanĩna haƙĩƙa, inã sanyã ka daga ɗaurarru قَالَ أَوَلَوۡ جِئۡتُكَ بِشَيۡءٍ مُّبِينٍ ٣٠Ya ce: "Ashe, kuma kõ dã nã zõ maka da wani, abu mai bayyanãwa قَالَ فَأۡتِ بِهِۦٓ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ ٣١Ya ce: "To, ka zõ da shi idan ka kasance daga, mãsu gaskiya فَأَلۡقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعۡبَانٌ مُّبِينٌ ٣٢Sai ya jẽfa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne وَنَزَعَ يَدَهُۥ فَإِذَا هِيَ بَيۡضَآءُ لِلنَّٰظِرِينَ ٣٣Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu kallo قَالَ لِلۡمَلَإِ حَوۡلَهُۥٓ إِنَّ هَٰذَا لَسَٰحِرٌ عَلِيمٌ ٣٤(Fir'auna) ya ce ga mashãwarta a gẽfensa, "Lalle ne, wannan haƙĩƙa, masihirci ne, mai ilmi يُرِيدُ أَن يُخۡرِجَكُم مِّنۡ أَرۡضِكُم بِسِحۡرِهِۦ فَمَاذَا تَأۡمُرُونَ ٣٥Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mẽne ne kuke shãwartãwa قَالُوٓاْ أَرۡجِهۡ وَأَخَاهُ وَٱبۡعَثۡ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ ٣٦Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika mãsu gayya a cikin birãne يَأۡتُوكَ بِكُلِّ سَحَّارٍ عَلِيمٍ ٣٧Zã su zõ maka da dukkan mai yawan sihiri masani فَجُمِعَ ٱلسَّحَرَةُ لِمِيقَٰتِ يَوۡمٍ مَّعۡلُومٍ ٣٨Sai aka tãra masihirta dõmin ajalin yini sananne وَقِيلَ لِلنَّاسِ هَلۡ أَنتُم مُّجۡتَمِعُونَ ٣٩Kuma aka ce wa mutãne "Kõ kũ mãsu tãruwã ne لَعَلَّنَا نَتَّبِعُ ٱلسَّحَرَةَ إِن كَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ ٤٠Tsammãninmu mu bi masihirta, idan sun kasance sũ ne marinjãya فَلَمَّا جَآءَ ٱلسَّحَرَةُ قَالُواْ لِفِرۡعَوۡنَ أَئِنَّ لَنَا لَأَجۡرًا إِن كُنَّا نَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبِينَ ٤١To, a lõkacin da masihirta suka jẽ suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙĩƙa munã da ijãra idan mun kasance mũ ne marinjãya قَالَ نَعَمۡ وَإِنَّكُمۡ إِذًا لَّمِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ ٤٢Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, kũ ne a lõkacin haƙĩƙa muƙarrabai قَالَ لَهُم مُّوسَىٰٓ أَلۡقُواْ مَآ أَنتُم مُّلۡقُونَ ٤٣Mũsã ya ce musu, "Ku jẽfa abin da kuke mãsu jẽfãwa فَأَلۡقَوۡاْ حِبَالَهُمۡ وَعِصِيَّهُمۡ وَقَالُواْ بِعِزَّةِ فِرۡعَوۡنَ إِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡغَٰلِبُونَ ٤٤Sai suka jẽfa igiyõyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mũ, haƙĩƙa, mũ ne marinjãya فَأَلۡقَىٰ مُوسَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ تَلۡقَفُ مَا يَأۡفِكُونَ ٤٥Sai Mũsa ya jẽfa sandarsa, sai ga ta tanã harhaɗe abin da suke yi na ƙarya فَأُلۡقِيَ ٱلسَّحَرَةُ سَٰجِدِينَ ٤٦Sai aka jẽfar da masihirta sunã mãsu sujada قَالُوٓاْ ءَامَنَّا بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٤٧Suka ce: "Mun yi ĩmãni da Ubangijin halitta رَبِّ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ٤٨Ubangijin Mũsa da Hãrũna قَالَ ءَامَنتُمۡ لَهُۥ قَبۡلَ أَنۡ ءَاذَنَ لَكُمۡۖ إِنَّهُۥ لَكَبِيرُكُمُ ٱلَّذِي عَلَّمَكُمُ ٱلسِّحۡرَ فَلَسَوۡفَ تَعۡلَمُونَۚ لَأُقَطِّعَنَّ أَيۡدِيَكُمۡ وَأَرۡجُلَكُم مِّنۡ خِلَٰفٍ وَلَأُصَلِّبَنَّكُمۡ أَجۡمَعِينَ ٤٩Ya ce: "Ashe, kun yi ĩmãni sabõda shĩ, a gabãnin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙĩƙa babbanku ne wanda ya kõya muku sihirin, to, zã ku sani. Lalle ne haƙĩƙa, zan kakkãtse hannuwanku da kafãfunku a tarnaƙi, kuma haƙĩƙa, zan tsĩrẽ ku gabã ɗaya قَالُواْ لَا ضَيۡرَۖ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا مُنقَلِبُونَ ٥٠Suka ce: "Bãbu wata cũta! Lalle ne mũ mãsu jũyãwa ne zuwa ga Ubangijinmu إِنَّا نَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لَنَا رَبُّنَا خَطَٰيَٰنَآ أَن كُنَّآ أَوَّلَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٥١Lalle ne mu munã kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gãfarta mana kurakuranmu dõmin mun kasance farkon mãsu ĩmãni ۞ وَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنۡ أَسۡرِ بِعِبَادِيٓ إِنَّكُم مُّتَّبَعُونَ ٥٢Kuma Muka aika zuwa ga Mũsã cẽwa ka yi tafiyar dare da bãyiNa, lalle ne kũ waɗanda ake biyã* ne فَأَرۡسَلَ فِرۡعَوۡنُ فِي ٱلۡمَدَآئِنِ حَٰشِرِينَ ٥٣Sai Fir'auna ya aika mãsu gayya a cikin birãne إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَشِرۡذِمَةٌ قَلِيلُونَ ٥٤Lalle ne, waɗannan, haƙĩƙa, ƙungiya ce kaɗan وَإِنَّهُمۡ لَنَا لَغَآئِظُونَ ٥٥Kuma lalle ne sũ, a gare Mu, Mãsu fusãtarwa ne وَإِنَّا لَجَمِيعٌ حَٰذِرُونَ ٥٦Kuma lalle ne mũ haƙĩƙa gabã ɗaya mãsu sauna ne فَأَخۡرَجۡنَٰهُم مِّن جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ ٥٧Sai Muka fitar da su daga gonaki da marẽmari وَكُنُوزٍ وَمَقَامٍ كَرِيمٍ ٥٨Da taskõki da mazauni mai kyau كَذَٰلِكَۖ وَأَوۡرَثۡنَٰهَا بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ٥٩Kamar haka! Kuma Muka gãdar da su ga Banĩ Isrãĩla فَأَتۡبَعُوهُم مُّشۡرِقِينَ ٦٠Sai suka bĩ su sunã mãsu fita a lõkacin hũdõwar rãnã فَلَمَّا تَرَٰٓءَا ٱلۡجَمۡعَانِ قَالَ أَصۡحَٰبُ مُوسَىٰٓ إِنَّا لَمُدۡرَكُونَ ٦١Sa'an nan a lõkacin da jama'a biyu suka ga jũna, sai abõkan Mũsã suka ce: "Lalle ne mũ haƙĩ ƙa, waɗanda ake riska ne قَالَ كـَلَّآۖ إِنَّ مَعِيَ رَبِّي سَيَهۡدِينِ ٦٢Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yanã tare da ni, zai shiryar da ni فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَىٰ مُوسَىٰٓ أَنِ ٱضۡرِب بِّعَصَاكَ ٱلۡبَحۡرَۖ فَٱنفَلَقَ فَكَانَ كُلُّ فِرۡقٍ كَٱلطَّوۡدِ ٱلۡعَظِيمِ ٦٣Sai Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa "Ka dõki tẽku da sandarka." Sai tẽku ta tsãge,* kõwane tsãgi ya kasance kamar falalen dũtse mai girma وَأَزۡلَفۡنَا ثَمَّ ٱلۡأٓخَرِينَ ٦٤Kuma Muka kusantar da waɗansu mutãne a can وَأَنجَيۡنَا مُوسَىٰ وَمَن مَّعَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ ٦٥Kuma Muka tsĩrar da Mũsã da waɗanda suke tãre da shi gabã ɗaya ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ٦٦Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutãnen إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ٦٧Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ٦٨Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙĩƙa, Shĩ ne Mabũwayi, Mai jin ƙai وَٱتۡلُ عَلَيۡهِمۡ نَبَأَ إِبۡرَٰهِيمَ ٦٩Kuma ka karanta, a kansu, lãbãrin Ibrãhĩm إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَا تَعۡبُدُونَ ٧٠A sã'ilin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bauta wa قَالُواْ نَعۡبُدُ أَصۡنَامًا فَنَظَلُّ لَهَا عَٰكِفِينَ ٧١Suka ce: "Munã bauta wa gumãka, sabõda haka munã yini mãsu lazimta a gare su قَالَ هَلۡ يَسۡمَعُونَكُمۡ إِذۡ تَدۡعُونَ ٧٢Ya ce: "Shin, sunã jin ku, a lõkacin da kuke kira أَوۡ يَنفَعُونَكُمۡ أَوۡ يَضُرُّونَ ٧٣Kõ kuwa sunã amfãnin ku, kõ sunã cũtar ku قَالُواْ بَلۡ وَجَدۡنَآ ءَابَآءَنَا كَذَٰلِكَ يَفۡعَلُونَ ٧٤Suka ce: "Ã'a mun sãmĩ ubanninmu, kamar haka ne suke aikatãwa قَالَ أَفَرَءَيۡتُم مَّا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ ٧٥Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kunã bautã wa أَنتُمۡ وَءَابَآؤُكُمُ ٱلۡأَقۡدَمُونَ ٧٦Kũ da ubanninku mafi daɗẽwa فَإِنَّهُمۡ عَدُوٌّ لِّيٓ إِلَّا رَبَّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٧٧To lalle ne, sũ maƙiya ne a gare ni, fãce Ubangijin halittu ٱلَّذِي خَلَقَنِي فَهُوَ يَهۡدِينِ ٧٨Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yanã shiryar da ni وَٱلَّذِي هُوَ يُطۡعِمُنِي وَيَسۡقِينِ ٧٩Kuma Wanda Yake Shĩ ne Yake ciyar da ni, kuma Yanã shãyar da ni وَإِذَا مَرِضۡتُ فَهُوَ يَشۡفِينِ ٨٠Kuma idan na yi jiyya, to, Shĩ ne Yake warkar da ni وَٱلَّذِي يُمِيتُنِي ثُمَّ يُحۡيِينِ ٨١Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rãyar da ni وَٱلَّذِيٓ أَطۡمَعُ أَن يَغۡفِرَ لِي خَطِيٓـَٔتِي يَوۡمَ ٱلدِّينِ ٨٢Kuma wanda Yake inã kwaɗayin Ya gãfarta mini kurãkuraina, a rãnar sãkamako رَبِّ هَبۡ لِي حُكۡمًا وَأَلۡحِقۡنِي بِٱلصَّٰلِحِينَ ٨٣Ya Ubangijĩna! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga sãlihai وَٱجۡعَل لِّي لِسَانَ صِدۡقٍ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ٨٤Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutãnen ƙarshe وَٱجۡعَلۡنِي مِن وَرَثَةِ جَنَّةِ ٱلنَّعِيمِ ٨٥Kuma Ka sanya ni daga magãdan Aljannar ni'ima وَٱغۡفِرۡ لِأَبِيٓ إِنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلضَّآلِّينَ ٨٦Kuma Ka gãfarta wa ubãna, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu وَلَا تُخۡزِنِي يَوۡمَ يُبۡعَثُونَ ٨٧Kuma kada Ka kunyata ni a rãnar da ake tãyar da su يَوۡمَ لَا يَنفَعُ مَالٌ وَلَا بَنُونَ ٨٨A rãnar da dũkiya bã ta amfãni, kuma ɗiya bã su yi إِلَّا مَنۡ أَتَى ٱللَّهَ بِقَلۡبٍ سَلِيمٍ ٨٩Fãce wanda ya jẽ wa Allah da zũciya mai tsarki وَأُزۡلِفَتِ ٱلۡجَنَّةُ لِلۡمُتَّقِينَ ٩٠Kuma aka kusantar da Aljanna ga mãsu taƙawa وَبُرِّزَتِ ٱلۡجَحِيمُ لِلۡغَاوِينَ ٩١Kuma aka fitar da wutã babba dõmin halakakku وَقِيلَ لَهُمۡ أَيۡنَ مَا كُنتُمۡ تَعۡبُدُونَ ٩٢Kuma aka ce musu, "Inã abin da kuka kasance kunã bautawa مِن دُونِ ٱللَّهِ هَلۡ يَنصُرُونَكُمۡ أَوۡ يَنتَصِرُونَ ٩٣Baicin Allah? Shin sunã tamakon ku kõ kuwa sunã tsare kansu فَكُبۡكِبُواْ فِيهَا هُمۡ وَٱلۡغَاوُۥنَ ٩٤Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun وَجُنُودُ إِبۡلِيسَ أَجۡمَعُونَ ٩٥Da rundunar Ibilĩsa gabã ɗaya قَالُواْ وَهُمۡ فِيهَا يَخۡتَصِمُونَ ٩٦Suka ce: alhãli sunã a cikinta sunã yin husũma تَٱللَّهِ إِن كُنَّا لَفِي ضَلَٰلٍ مُّبِينٍ ٩٧Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙĩƙa, a cikin ɓata bayyananna إِذۡ نُسَوِّيكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٩٨A lõkacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu وَمَآ أَضَلَّنَآ إِلَّا ٱلۡمُجۡرِمُونَ ٩٩Kuma bãbu abin da ya ɓatar da mu fãce mãsu laifi فَمَا لَنَا مِن شَٰفِعِينَ ١٠٠Sabõda haka bã mu da waɗansu macẽta وَلَا صَدِيقٍ حَمِيمٍ ١٠١Kuma bã mu da abõki, masõyi فَلَوۡ أَنَّ لَنَا كَرَّةً فَنَكُونَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١٠٢Sabõda haka dã lalle munã da (dãmar) kõmawa, dõmin mu kasance daga mũminai إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٠٣Lalle ne, a cikin wancan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, bã su kasance mũminai ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٠٤Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai كَذَّبَتۡ قَوۡمُ نُوحٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٠٥Mutãnen Nũhu sun ƙaryata Manzanni إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ نُوحٌ أَلَا تَتَّقُونَ ١٠٦A lõkacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Bã zã ku ji tsoron Allah ba إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٌ ١٠٧Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٠٨To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٠٩Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãtã ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١١٠Sabõda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã ۞ قَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لَكَ وَٱتَّبَعَكَ ٱلۡأَرۡذَلُونَ ١١١Suka ce: "Ashe, zã mu yi ĩmãni sabõda kai alhãli kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka قَالَ وَمَا عِلۡمِي بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ١١٢Ya ce: "Kuma bã ni da sani ga abin da suka kasance sanã aikatãwa إِنۡ حِسَابُهُمۡ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّيۖ لَوۡ تَشۡعُرُونَ ١١٣Hisãbinsu bai zama ba fãce ga Ubangijina, dã kunã sansancẽwa وَمَآ أَنَا۠ بِطَارِدِ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١١٤Ban zama mai kõre mũminai ba إِنۡ أَنَا۠ إِلَّا نَذِيرٌ مُّبِينٌ ١١٥Nĩ ba kõwa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanãwa قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰنُوحُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمَرۡجُومِينَ ١١٦Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, yã Nũhu, (daga maganarka,) haƙĩƙa, kanã kasancẽwa daga waɗanda ake jẽfewa قَالَ رَبِّ إِنَّ قَوۡمِي كَذَّبُونِ ١١٧Ya ce: "Yã Ubangijĩna! Lalle ne mutãnena sun ƙaryatã ni فَٱفۡتَحۡ بَيۡنِي وَبَيۡنَهُمۡ فَتۡحًا وَنَجِّنِي وَمَن مَّعِيَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١١٨Sai ka yi hukunci, a tsakãnĩna da tsakãninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsĩrar da ni, da waɗanda suke tãre da ni daga mũminai فَأَنجَيۡنَٰهُ وَمَن مَّعَهُۥ فِي ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ ١١٩Sai Muka tsĩrar da shi, shi da waɗanda suke tãre da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lõdi ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا بَعۡدُ ٱلۡبَاقِينَ ١٢٠Sa'an nan Muka nutsar a bãyan haka, da sauran إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٢١Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٢٢Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai Rahama كَذَّبَتۡ عَادٌ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٢٣Ãdãwa sun ƙaryata Manzanni إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ هُودٌ أَلَا تَتَّقُونَ ١٢٤A lõkacin da ɗan'uwansu, Hũdu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٌ ١٢٥Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙĩƙa, Manzo ne, amintacce فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٢٦Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٢٧Kuma bã ni tambayar wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba, fãce daga Ubangijin halittu أَتَبۡنُونَ بِكُلِّ رِيعٍ ءَايَةً تَعۡبَثُونَ ١٢٨Shin, kunã yin ginin sitadiyo* a kõwane tsauni ne, kunã yin wãsa وَتَتَّخِذُونَ مَصَانِعَ لَعَلَّكُمۡ تَخۡلُدُونَ ١٢٩Kuma kunã riƙon matsãrar ruwa, tsammãninku, ku dawwama وَإِذَا بَطَشۡتُم بَطَشۡتُمۡ جَبَّارِينَ ١٣٠Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kunã mãsu tanƙwasãwa فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٣١To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِيٓ أَمَدَّكُم بِمَا تَعۡلَمُونَ ١٣٢Ku ji tsõron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani أَمَدَّكُم بِأَنۡعَٰمٍ وَبَنِينَ ١٣٣Ya taimake ku da dabbõbin ni'ima da ɗiya وَجَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ ١٣٤Da gõnaki da marẽmari إِنِّيٓ أَخَافُ عَلَيۡكُمۡ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ ١٣٥Lalle ne nĩ, inã ji muku tsõron azãbar wani yini mai girma قَالُواْ سَوَآءٌ عَلَيۡنَآ أَوَعَظۡتَ أَمۡ لَمۡ تَكُن مِّنَ ٱلۡوَٰعِظِينَ ١٣٦Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Kã yi wa'azi kõ ba ka kasance daga mãsu wa'azi ba إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا خُلُقُ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٣٧Wannan abu bai zamõ ba fãce hãlãyen* mutãnen farko وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ ١٣٨Kuma mũ ba mu zama waɗanda ake yi wa azãba ba فَكَذَّبُوهُ فَأَهۡلَكۡنَٰهُمۡۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٣٩Sabõda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da sũ. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٤٠Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙĩƙa, Shi ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai كَذَّبَتۡ ثَمُودُ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٤١Samũdãwa sun ƙaryata Manzanni إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ صَٰلِحٌ أَلَا تَتَّقُونَ ١٤٢A lõkacin da ɗan'uwansu Sãlihu ya ce: "Shin, bã zã ku bi Allah da taƙawa ba إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٌ ١٤٣Lalle ne nĩ zuwã gare ku, Manzo ne, amintacce فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٤٤Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٤٥Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrãta ba ta zama ba fãce da a Ubangijin halittu أَتُتۡرَكُونَ فِي مَا هَٰهُنَآ ءَامِنِينَ ١٤٦Shin, anã barin ku* a cikin abin da yake a nan, kunã amintattu فِي جَنَّٰتٍ وَعُيُونٍ ١٤٧A cikin gõnaki da marẽmari وَزُرُوعٍ وَنَخۡلٍ طَلۡعُهَا هَضِيمٌ ١٤٨Da shuke-shuke da dabĩ nai, 'ya'yan itãcensu hirtsi* mãsu narkẽwa a ciki وَتَنۡحِتُونَ مِنَ ٱلۡجِبَالِ بُيُوتًا فَٰرِهِينَ ١٤٩Kuma kunã sassaƙa gidãje daga duwãtsu, kunã mãsu alfãhari فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٥٠Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَلَا تُطِيعُوٓاْ أَمۡرَ ٱلۡمُسۡرِفِينَ ١٥١Kada ku yi ɗã'ã ga umurnin maɓarnata ٱلَّذِينَ يُفۡسِدُونَ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَلَا يُصۡلِحُونَ ١٥٢Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma bã su kyautatãwa قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ ١٥٣Suka ce: "Kai daga mãsu sihiri kurum kake مَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثۡلُنَا فَأۡتِ بِـَٔايَةٍ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ ١٥٤Bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu. To, kã zo da wata ãyã idan kã kasance daga mãsu gaskiya قَالَ هَٰذِهِۦ نَاقَةٌ لَّهَا شِرۡبٌ وَلَكُمۡ شِرۡبُ يَوۡمٍ مَّعۡلُومٍ ١٥٥Ya ce: "Wannan rãkuma ce tanã da shan* yini, kuma kunã da shan yini sasanne وَلَا تَمَسُّوهَا بِسُوٓءٍ فَيَأۡخُذَكُمۡ عَذَابُ يَوۡمٍ عَظِيمٍ ١٥٦Kada ku shãfe ta da cũta har azãbar yini mai girmã ta shãfe ku فَعَقَرُوهَا فَأَصۡبَحُواْ نَٰدِمِينَ ١٥٧Sai suka sõke ta sa'an nan suka wãyi gari sunã mãsu nadãma فَأَخَذَهُمُ ٱلۡعَذَابُۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٥٨Sabõda haka azãba ta kãma su. Lalle ne a cikin wannan akwai ãyã, kuma mafi yawansu, ba su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٥٩Lalle ne Ubangijinka, haƙĩ ƙa, Shĩ ne Mabuwayi, Mai jin ƙai كَذَّبَتۡ قَوۡمُ لُوطٍ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٦٠Mutãnen Lũɗu sun ƙaryata Manzanni إِذۡ قَالَ لَهُمۡ أَخُوهُمۡ لُوطٌ أَلَا تَتَّقُونَ ١٦١A lõkacin da ɗan'uwansu,* Lũɗu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٌ ١٦٢Lalle ne nĩ, zuwa gare ku, Manzõ ne, amintacce فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٦٣Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'ã وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٦٤Kuma bã ni tambayar ku wata ijãra, Ijãrãta ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu أَتَأۡتُونَ ٱلذُّكۡرَانَ مِنَ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٦٥Shin kunã jẽ wa maza daga cikin talikai وَتَذَرُونَ مَا خَلَقَ لَكُمۡ رَبُّكُم مِّنۡ أَزۡوَٰجِكُمۚ بَلۡ أَنتُمۡ قَوۡمٌ عَادُونَ ١٦٦Kuma kunã barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga mãtanku? Ã'a, ku mutãne ne mãsu ƙẽtarẽwa قَالُواْ لَئِن لَّمۡ تَنتَهِ يَٰلُوطُ لَتَكُونَنَّ مِنَ ٱلۡمُخۡرَجِينَ ١٦٧Suka ce: "Lalle ne haƙĩƙa idan ba ka hanu ba, yã Lũɗu! Tĩlas ne kanã kasancẽwa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari) قَالَ إِنِّي لِعَمَلِكُم مِّنَ ٱلۡقَالِينَ ١٦٨Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙĩƙa, inã daga mãsu ƙinsa رَبِّ نَجِّنِي وَأَهۡلِي مِمَّا يَعۡمَلُونَ ١٦٩Ya Ubangijina! Ka tsĩrar da ni da iyãlĩna daga abin da suke aikatãwa فَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ ١٧٠Sabõda haka Muka tsĩrar da shi, Shi da mutãnensa gabã ɗaya إِلَّا عَجُوزًا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ ١٧١Fãce wata tsõhuwa a cikin mãsu wanzuwa ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ١٧٢Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu وَأَمۡطَرۡنَا عَلَيۡهِم مَّطَرًاۖ فَسَآءَ مَطَرُ ٱلۡمُنذَرِينَ ١٧٣Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya mũnana إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٧٤Lalle ne ga wannan, akwai ãyã, kuma mafi yawansu bã su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٧٥Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai كَذَّبَ أَصۡحَٰبُ لۡـَٔيۡكَةِ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٧٦Ma'abũta ƙunci sun ƙaryata Manzanni إِذۡ قَالَ لَهُمۡ شُعَيۡبٌ أَلَا تَتَّقُونَ ١٧٧A lõkacin da Shu'aibu ya ce musu, "Bã zã ku yi taƙawa ba إِنِّي لَكُمۡ رَسُولٌ أَمِينٌ ١٧٨Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce فَٱتَّقُواْ ٱللَّهَ وَأَطِيعُونِ ١٧٩Sabõda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗã'ã وَمَآ أَسۡـَٔلُكُمۡ عَلَيۡهِ مِنۡ أَجۡرٍۖ إِنۡ أَجۡرِيَ إِلَّا عَلَىٰ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٨٠Kuma ba ni tambayar ku wata ijãra a kansa. Ijãrata ba ta zama ba fãce daga Ubangijin halittu ۞ أَوۡفُواْ ٱلۡكَيۡلَ وَلَا تَكُونُواْ مِنَ ٱلۡمُخۡسِرِينَ ١٨١Ku cika mũdu, kuma kada ku kasance daga mãsu sanyãwar hasãra (ga mutãne) وَزِنُواْ بِٱلۡقِسۡطَاسِ ٱلۡمُسۡتَقِيمِ ١٨٢Kuma ku yi awo da sikẽli daidaitacce وَلَا تَبۡخَسُواْ ٱلنَّاسَ أَشۡيَآءَهُمۡ وَلَا تَعۡثَوۡاْ فِي ٱلۡأَرۡضِ مُفۡسِدِينَ ١٨٣Kuma kada ku nakasa wa mutãne abũbuwansu kuma kada ku yi fasãdi a cikin ƙasa kuna mãsu ɓarna وَٱتَّقُواْ ٱلَّذِي خَلَقَكُمۡ وَٱلۡجِبِلَّةَ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٨٤Kuma ku ji tsõron Allah wanda Ya halitta ku, kũ da jama'ar farko قَالُوٓاْ إِنَّمَآ أَنتَ مِنَ ٱلۡمُسَحَّرِينَ ١٨٥Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne وَمَآ أَنتَ إِلَّا بَشَرٌ مِّثۡلُنَا وَإِن نَّظُنُّكَ لَمِنَ ٱلۡكَٰذِبِينَ ١٨٦Kuma bã kõwa kake ba, fãce mutum kamarmu kuma lalle ne munã zaton ka, haƙĩƙa, daga maƙaryata فَأَسۡقِطۡ عَلَيۡنَا كِسَفًا مِّنَ ٱلسَّمَآءِ إِن كُنتَ مِنَ ٱلصَّٰدِقِينَ ١٨٧To ka jẽfo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga mãsu gaskiya قَالَ رَبِّيٓ أَعۡلَمُ بِمَا تَعۡمَلُونَ ١٨٨Ya ce: "Ubangijĩna ne Mafi sani ga abin da kuke aikatãwa فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمۡ عَذَابُ يَوۡمِ ٱلظُّلَّةِۚ إِنَّهُۥ كَانَ عَذَابَ يَوۡمٍ عَظِيمٍ ١٨٩Sai suka ƙaiyatã shi, sabõda haka, azãbar rãnar girgije* ta kãma su. Lalle ne ita, tã kasance azãbar yini mai girma إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَةًۖ وَمَا كَانَ أَكۡثَرُهُم مُّؤۡمِنِينَ ١٩٠Lalle a cikin wancan haƙĩka akwai ãya, amma mafi yawansu ba su kasance mãsu ĩmãni ba وَإِنَّ رَبَّكَ لَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلرَّحِيمُ ١٩١Kuma lalle Ubangijĩnka, haƙĩƙa, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai وَإِنَّهُۥ لَتَنزِيلُ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٩٢Kuma lalle shi (Alƙur'ãni), haƙĩƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne نَزَلَ بِهِ ٱلرُّوحُ ٱلۡأَمِينُ ١٩٣Rũhi* amintacce ne ya sauka da shi عَلَىٰ قَلۡبِكَ لِتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُنذِرِينَ ١٩٤A kan zũciyarka, dõmin ka kasance daga mãsu gargaɗi بِلِسَانٍ عَرَبِيٍّ مُّبِينٍ ١٩٥Da harshe na Larabci mai bayãni وَإِنَّهُۥ لَفِي زُبُرِ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٩٦Kuma lalle shin, haƙĩƙa, yanã a cikin litattafan (Manzannin) farko أَوَلَمۡ يَكُن لَّهُمۡ ءَايَةً أَن يَعۡلَمَهُۥ عُلَمَٰٓؤُاْ بَنِيٓ إِسۡرَٰٓءِيلَ ١٩٧Ashe, bai kasance ãyã ba a gare su, ya zama Mãlaman Banĩ Isrã'ĩla sun san shi وَلَوۡ نَزَّلۡنَٰهُ عَلَىٰ بَعۡضِ ٱلۡأَعۡجَمِينَ ١٩٨Kuma dã mun saukar da shi a kan sãshen Ajamãwa فَقَرَأَهُۥ عَلَيۡهِم مَّا كَانُواْ بِهِۦ مُؤۡمِنِينَ ١٩٩Ya karanta shi a kansu, ba su kasance sabõda shi mãsu ĩmãni ba كَذَٰلِكَ سَلَكۡنَٰهُ فِي قُلُوبِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ ٢٠٠Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukãtan mãsu laifi لَا يُؤۡمِنُونَ بِهِۦ حَتَّىٰ يَرَوُاْ ٱلۡعَذَابَ ٱلۡأَلِيمَ ٢٠١Bã zã su yi ĩmãni da shĩ ba sai sun ga azãbar nan mai raɗadi فَيَأۡتِيَهُم بَغۡتَةً وَهُمۡ لَا يَشۡعُرُونَ ٢٠٢Sai ta taho musu kwatsam, alhãli kuwa sũ, ba su sansance ba فَيَقُولُواْ هَلۡ نَحۡنُ مُنظَرُونَ ٢٠٣Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ ٢٠٤Ashe, to, da azãbar Mu suke nẽman gaggãwa أَفَرَءَيۡتَ إِن مَّتَّعۡنَٰهُمۡ سِنِينَ ٢٠٥Ashe, to, kã gani, idan Muka jĩshe su daɗi a shẽkaru ثُمَّ جَآءَهُم مَّا كَانُواْ يُوعَدُونَ ٢٠٦Sa'an nan abin da suka kasance anã yi musu wa'adi (da shi) ya jẽ musu مَآ أَغۡنَىٰ عَنۡهُم مَّا كَانُواْ يُمَتَّعُونَ ٢٠٧Abin da suka kasance anã jĩshe su dãɗin bã zai tunkuɗe azãba ba daga gare* su وَمَآ أَهۡلَكۡنَا مِن قَرۡيَةٍ إِلَّا لَهَا مُنذِرُونَ ٢٠٨Kuma bã Mu halakar da wata alƙarya ba fãce tanã da mãsu gargaɗi ذِكۡرَىٰ وَمَا كُنَّا ظَٰلِمِينَ ٢٠٩Dõmin tunãtarwa, kuma ba Mu kasance Mãsu zãlunci ba وَمَا تَنَزَّلَتۡ بِهِ ٱلشَّيَٰطِينُ ٢١٠Kuma (Alƙur'ãni) Shaiɗãnu ba su ɗõra sauka da shĩba وَمَا يَنۢبَغِي لَهُمۡ وَمَا يَسۡتَطِيعُونَ ٢١١Kuma bã ya kamãta a gare su (su Shaiɗãnu su sauka da shi), kuma ba su iyãwa إِنَّهُمۡ عَنِ ٱلسَّمۡعِ لَمَعۡزُولُونَ ٢١٢Lalle ne sũ, daga saurãre, haƙĩƙa, waɗanda aka nĩsantar ne فَلَا تَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ فَتَكُونَ مِنَ ٱلۡمُعَذَّبِينَ ٢١٣Sabõda haka, kada ka kira wani abin bautãwa na dabam tãre da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azãba وَأَنذِرۡ عَشِيرَتَكَ ٱلۡأَقۡرَبِينَ ٢١٤Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci وَٱخۡفِضۡ جَنَاحَكَ لِمَنِ ٱتَّبَعَكَ مِنَ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٢١٥Kuma ka sassauta fikãfikanka* ga wanda ya bĩ ka daga mũminai فَإِنۡ عَصَوۡكَ فَقُلۡ إِنِّي بَرِيٓءٌ مِّمَّا تَعۡمَلُونَ ٢١٦Sa'an nan idan suka sãɓã maka to ka ce: "Lalle nĩ, barrantacce ne daga abin da kuko aikatãwa وَتَوَكَّلۡ عَلَى ٱلۡعَزِيزِ ٱلرَّحِيمِ ٢١٧Kuma ka dõgara ga Mabuwãyi, Mai jin ƙai ٱلَّذِي يَرَىٰكَ حِينَ تَقُومُ ٢١٨Wanda Yake ganin ka a lõkacin da kake tãshi tsaye وَتَقَلُّبَكَ فِي ٱلسَّٰجِدِينَ ٢١٩Da jujjuyãwarka a cikin mãsu yin sujada إِنَّهُۥ هُوَ ٱلسَّمِيعُ ٱلۡعَلِيمُ ٢٢٠Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani هَلۡ أُنَبِّئُكُمۡ عَلَىٰ مَن تَنَزَّلُ ٱلشَّيَٰطِينُ ٢٢١Shin, (kunã so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗãnnu kan sauka تَنَزَّلُ عَلَىٰ كُلِّ أَفَّاكٍ أَثِيمٍ ٢٢٢Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi يُلۡقُونَ ٱلسَّمۡعَ وَأَكۡثَرُهُمۡ كَٰذِبُونَ ٢٢٣Sunã jẽfa (abin da suka) ji, alhãli kuwa mafi yawansu maƙaryata ne وَٱلشُّعَرَآءُ يَتَّبِعُهُمُ ٱلۡغَاوُۥنَ ٢٢٤Kuma mawãƙa* halakakku ne ke bin su أَلَمۡ تَرَ أَنَّهُمۡ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ ٢٢٥Shin, ba ku cẽwa, lalle ne sũ, cikin kõwane rango sunã yin ɗimuwa (su ƙẽtare haddi) ba وَأَنَّهُمۡ يَقُولُونَ مَا لَا يَفۡعَلُونَ ٢٢٦Kuma lalle ne, sũ, sunã faɗin abin da bã su aikatãwa إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ وَذَكَرُواْ ٱللَّهَ كَثِيرًا وَٱنتَصَرُواْ مِنۢ بَعۡدِ مَا ظُلِمُواْۗ وَسَيَعۡلَمُ ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ ٢٢٧Fãce waɗanda suka yi ĩmãni suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rãma zãlunci, daga bãyan an zãlunce su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci, zã su sani a wace majũya suke jũyãwa

الترجمة: Abubakar Mahmood Jummi.