بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
إِذَا ٱلشَّمۡسُ كُوِّرَتۡ ١Idan rãna aka shafe haskenta وَإِذَا ٱلنُّجُومُ ٱنكَدَرَتۡ ٢Kuma idan taurãri suka gurɓãce (wani ya shiga a cikin wani) وَإِذَا ٱلۡجِبَالُ سُيِّرَتۡ ٣Kuma idan duwãtsu aka tafiyar da su وَإِذَا ٱلۡعِشَارُ عُطِّلَتۡ ٤Kuma idan rãƙuma mãsu cikunna* aka sakẽ su wãwai, bã ga kõwa ba وَإِذَا ٱلۡوُحُوشُ حُشِرَتۡ ٥Kuma idan dabbõbin dãji aka tattara su وَإِذَا ٱلۡبِحَارُ سُجِّرَتۡ ٦Kuma idan tẽkuna aka mayar da su wuta وَإِذَا ٱلنُّفُوسُ زُوِّجَتۡ ٧Kuma idan rãyuka aka haɗa* su da jikunkunansu وَإِذَا ٱلۡمَوۡءُۥدَةُ سُئِلَتۡ ٨Kuma idan wadda aka turbuɗe* ta da rai aka tambaye ta بِأَيِّ ذَنۢبٍ قُتِلَتۡ ٩Sabõda wane laifi ne aka kashe ta وَإِذَا ٱلصُّحُفُ نُشِرَتۡ ١٠Idan takardun ayyuka aka wãtsa su (ga mãsu su) وَإِذَا ٱلسَّمَآءُ كُشِطَتۡ ١١Kuma idan sama aka fẽɗe ta وَإِذَا ٱلۡجَحِيمُ سُعِّرَتۡ ١٢Kuma idan Jahĩm aka hũra ta وَإِذَا ٱلۡجَنَّةُ أُزۡلِفَتۡ ١٣Kuma idan Aljanna aka kusantar da ita عَلِمَتۡ نَفۡسٌ مَّآ أَحۡضَرَتۡ ١٤Rai ya san abin da ya halartar (a rãnar nan) فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلۡخُنَّسِ ١٥To, ba sai Na yi rantsuwa da taurãri matafã* ba ٱلۡجَوَارِ ٱلۡكُنَّسِ ١٦Mãsu gudu suna ɓũya وَٱلَّيۡلِ إِذَا عَسۡعَسَ ١٧Da dare idan ya bãyar da bãya وَٱلصُّبۡحِ إِذَا تَنَفَّسَ ١٨Da sãfiya idan ta yi lumfashi إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ ١٩Lalle ne shi (Alƙur'ãni) haƙƙan, maganar wani manzon (Allah) ne mai girma ga Allah ذِي قُوَّةٍ عِندَ ذِي ٱلۡعَرۡشِ مَكِينٍ ٢٠Mai ƙarfi, mai daraja a wurin Mai Al'arshi مُّطَاعٍ ثَمَّ أَمِينٍ ٢١Wanda ake yi wa ɗã'a (wato shugaban malã'iku) ne a can, amintacce وَمَا صَاحِبُكُم بِمَجۡنُونٍ ٢٢Kuma abokinku ba mahaukaci ba ne وَلَقَدۡ رَءَاهُ بِٱلۡأُفُقِ ٱلۡمُبِينِ ٢٣Kuma lalle ne, yã gan shi* a cikin sararin sama mabayyani وَمَا هُوَ عَلَى ٱلۡغَيۡبِ بِضَنِينٍ ٢٤Kuma shi, ga gaibi* bã mai rowa ba ne وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَيۡطَٰنٍ رَّجِيمٍ ٢٥Kuma shi (Alƙur'ani) bã maganar shaiɗani, wanda aka la'ana, ba ce فَأَيۡنَ تَذۡهَبُونَ ٢٦Shin, a inã zã ku tafi إِنۡ هُوَ إِلَّا ذِكۡرٌ لِّلۡعَٰلَمِينَ ٢٧Lalle ne shi (Alƙur'ãni), bã kõme ba ne fãce gargaɗi ga talikai لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَسۡتَقِيمَ ٢٨Ga wanda ya so, daga cikinku, ya shiryu وَمَا تَشَآءُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُ رَبُّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٢٩Kuma bã zã ku so ba sai idan Allah Ubangijin halitta Yã yarda