ملة الإسلام

السورة 74 · 56 آية · Abubakar Mahmoud Gumi

سورة المدثر باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة المدثر (1,220 قارئاً)
مكيةسورة المدثر٥٦ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡمُدَّثِّرُ ١Yã wanda ya lulluɓa da mayãfi قُمۡ فَأَنذِرۡ ٢Ka tãshi dõmin ka yi gargaɗi وَرَبَّكَ فَكَبِّرۡ ٣Kuma Ubangijinka, sai ka girmama Shi وَثِيَابَكَ فَطَهِّرۡ ٤Kuma tutãfinka, sai ka tsarkake su وَٱلرُّجۡزَ فَٱهۡجُرۡ ٥Kuma gumãka, sai ka ƙaurace musu وَلَا تَمۡنُن تَسۡتَكۡثِرُ ٦Kada ka yi kyauta kana nẽman ƙãri وَلِرَبِّكَ فَٱصۡبِرۡ ٧Kuma sabõda Ubangijinka? Sai ka yi haƙure فَإِذَا نُقِرَ فِي ٱلنَّاقُورِ ٨To, idan aka yi bũsa a cikin ƙaho فَذَٰلِكَ يَوۡمَئِذٍ يَوۡمٌ عَسِيرٌ ٩To, wannan, a rãnar nan, yini ne mai wuya عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ غَيۡرُ يَسِيرٍ ١٠A kan kãfirai, bã mai sauƙi ba ne ذَرۡنِي وَمَنۡ خَلَقۡتُ وَحِيدًا ١١Ka bar Ni da wanda Na halitta, yana shi kaɗai وَجَعَلۡتُ لَهُۥ مَالًا مَّمۡدُودًا ١٢Kuma Na sanya masa dũkiya shimfiɗaɗɗiya وَبَنِينَ شُهُودًا ١٣Da ɗiyã halartattu وَمَهَّدتُّ لَهُۥ تَمۡهِيدًا ١٤Kuma Na shimfiɗa? masa kõme shimfiɗãwa ثُمَّ يَطۡمَعُ أَنۡ أَزِيدَ ١٥Sa'an nan, yanã kwaɗayin in yi masa ƙãri كـَلَّآۖ إِنَّهُۥ كَانَ لِأٓيَٰتِنَا عَنِيدًا ١٦Faufau! Lalle ne, shĩ yã kasance, ga ãyõyinMu, mai tsaurin kai سَأُرۡهِقُهُۥ صَعُودًا ١٧Zã Ni kallafa masa wahala mai hauhawa إِنَّهُۥ فَكَّرَ وَقَدَّرَ ١٨Lalle ne, Shi, yã yi tunãni, kuma yã ƙaddara (abin da zai faɗã game da Alƙur'ãni) فَقُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ ١٩Sabõda haka, aka la'ane shi, kamar yadda ya ƙaddara ثُمَّ قُتِلَ كَيۡفَ قَدَّرَ ٢٠Sa'an nan, aka la'ane shi kamar yadda ya ƙaddara ثُمَّ نَظَرَ ٢١Sa'an nan, ya yi tunãni ثُمَّ عَبَسَ وَبَسَرَ ٢٢Sa'an nan, ya gintse huska? kuma ya yi murtuk ثُمَّ أَدۡبَرَ وَٱسۡتَكۡبَرَ ٢٣Sa'an nan, ya jũya bãya, kuma ya bunƙãsa فَقَالَ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٌ يُؤۡثَرُ ٢٤Sai ya ce: "Wannan abu dai bã kõme ba ne fãce wani sihiri, wanda aka ruwaito إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا قَوۡلُ ٱلۡبَشَرِ ٢٥Wannan maganar mutum dai ce سَأُصۡلِيهِ سَقَرَ ٢٦Zã Ni ƙõna shi da Saƙar وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سَقَرُ ٢٧Kuma mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽwa Saƙar لَا تُبۡقِي وَلَا تَذَرُ ٢٨Bã ta ragẽwa, kuma bã ta bari لَوَّاحَةٌ لِّلۡبَشَرِ ٢٩Mai nãcẽwa ga jiki ce (da (ƙũna) عَلَيۡهَا تِسۡعَةَ عَشَرَ ٣٠A kanta akwai (matsara) gõma shã tara وَمَا جَعَلۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلنَّارِ إِلَّا مَلَٰٓئِكَةًۖ وَمَا جَعَلۡنَا عِدَّتَهُمۡ إِلَّا فِتۡنَةً لِّلَّذِينَ كَفَرُواْ لِيَسۡتَيۡقِنَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَيَزۡدَادَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ إِيمَٰنًا وَلَا يَرۡتَابَ ٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَ وَلِيَقُولَ ٱلَّذِينَ فِي قُلُوبِهِم مَّرَضٌ وَٱلۡكَٰفِرُونَ مَاذَآ أَرَادَ ٱللَّهُ بِهَٰذَا مَثَلًاۚ كَذَٰلِكَ يُضِلُّ ٱللَّهُ مَن يَشَآءُ وَيَهۡدِي مَن يَشَآءُۚ وَمَا يَعۡلَمُ جُنُودَ رَبِّكَ إِلَّا هُوَۚ وَمَا هِيَ إِلَّا ذِكۡرَىٰ لِلۡبَشَرِ ٣١Kuma ba Mu sanya ma'abũta wutã (wãto matsaranta) ba, fãce malã'iku, kuma ba Mu sanya adadinsu (gõma sha tara) ba, fãce dõmin fitina ga waɗanda suka kãfirta domin waɗanda aka bai wa littãfi su sãmi yaƙĩni kuma waɗanda suka yi ĩmãni su ƙãra ĩmãni, kuma waɗanda aka bai wa littãfi da mũminai bã zã su yi shakka ba, kuma domin wa ɗanda a cikin zukatansu akwai wata cuta da kãfirai su ce: "Mẽ Allah Yake nufi da wannan, ya kasance misãli?" Haka dai Allah ke ɓatar da wanda Ya so, kuma Ya shiryar da wanda ya so. Kuma bãbu wanda ya san mayãƙan Ubangijinka fãce Shi, kuma ita (wutar) ba ta kasance ba fãce wata tunãtarwa ce ga mutum كـَلَّا وَٱلۡقَمَرِ ٣٢A'aha! Ina rantsuwa da watã وَٱلَّيۡلِ إِذۡ أَدۡبَرَ ٣٣Da dare a lõkacin da ya jũyar da baya وَٱلصُّبۡحِ إِذَآ أَسۡفَرَ ٣٤Da sãfiya idan ta wãye إِنَّهَا لَإِحۡدَى ٱلۡكُبَرِ ٣٥Ita (wutar) ɗayan manyan masĩfũ? ce نَذِيرًا لِّلۡبَشَرِ ٣٦Mai gargaɗĩ ce ga mutum لِمَن شَآءَ مِنكُمۡ أَن يَتَقَدَّمَ أَوۡ يَتَأَخَّرَ ٣٧Ga wanda ya so, daga cikinku, ya gabãta ko ya jinkirta كُلُّ نَفۡسِۭ بِمَا كَسَبَتۡ رَهِينَةٌ ٣٨Kõwane rai ga abin da ya aikata jingina ce إِلَّآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡيَمِينِ ٣٩Fãce mutãnen dãma فِي جَنَّٰتٍ يَتَسَآءَلُونَ ٤٠A cikin Aljanna suna tambayar jũna عَنِ ٱلۡمُجۡرِمِينَ ٤١Game da mãsu laifi مَا سَلَكَكُمۡ فِي سَقَرَ ٤٢(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin Saƙar قَالُواْ لَمۡ نَكُ مِنَ ٱلۡمُصَلِّينَ ٤٣Suka ce: "Ba mu kasance munã a cikin mãsu salla ba وَلَمۡ نَكُ نُطۡعِمُ ٱلۡمِسۡكِينَ ٤٤Kuma ba mu kasance muna ciyar da matalautã ba وَكُنَّا نَخُوضُ مَعَ ٱلۡخَآئِضِينَ ٤٥Kuma mun kasance muna kũtsãwa tãre da mãsu kũtsãwa وَكُنَّا نُكَذِّبُ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ٤٦Mun kasance munã ƙaryata rãnar sãkamako حَتَّىٰٓ أَتَىٰنَا ٱلۡيَقِينُ ٤٧Har gaskiya (wãto mutuwa) ta zo mana فَمَا تَنفَعُهُمۡ شَفَٰعَةُ ٱلشَّٰفِعِينَ ٤٨Sabõda haka cẽton mãsu cẽto bã zai amfãne su ba فَمَا لَهُمۡ عَنِ ٱلتَّذۡكِرَةِ مُعۡرِضِينَ ٤٩Haba! Me ya same su, suka zama mãsu bijirewa daga wa'azin gaskiya كَأَنَّهُمۡ حُمُرٌ مُّسۡتَنفِرَةٌ ٥٠Kamar dai sũ, jãkuna firgitattu ne فَرَّتۡ مِن قَسۡوَرَةِۭ ٥١Sun gudu daga zãki بَلۡ يُرِيدُ كُلُّ ٱمۡرِيٍٕ مِّنۡهُمۡ أَن يُؤۡتَىٰ صُحُفًا مُّنَشَّرَةً ٥٢A'aha! Kõwãne mutum daga cikinsu yanã son a zo masa da takardu (da sũnansa) ana wãtsãwa كـَلَّاۖ بَل لَّا يَخَافُونَ ٱلۡأٓخِرَةَ ٥٣A'aha! Kai dai, bã su jin tsõron Lãhira كـَلَّآ إِنَّهُۥ تَذۡكِرَةٌ ٥٤A'aha! Lalle ne, shi (Alƙur'ãni) tunãtarwa ce فَمَن شَآءَ ذَكَرَهُۥ ٥٥Dõmin wanda ya so, ya tuna وَمَا يَذۡكُرُونَ إِلَّآ أَن يَشَآءَ ٱللَّهُۚ هُوَ أَهۡلُ ٱلتَّقۡوَىٰ وَأَهۡلُ ٱلۡمَغۡفِرَةِ ٥٦Kuma bã zã su tuna ba fãce idan Allah Ya so, Shi ne Ya cancanta a bi Shi da taƙawa kuma Ya cancanta ga Ya yi gãfara

الترجمة: Abubakar Mahmoud Gumi.