ملة الإسلام

السورة 23 · 118 آية · Abubakar Mahmoud Gumi

سورة المؤمنون باللغة الهوسا

السورة بالعربية مع التفسير استمع إلى سورة المؤمنون (1,265 قارئاً)
مكيةسورة المؤمنون١١٨ آية

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

قَدۡ أَفۡلَحَ ٱلۡمُؤۡمِنُونَ ١Lalle ne, Mũminai sun sãmi babban rabõ ٱلَّذِينَ هُمۡ فِي صَلَاتِهِمۡ خَٰشِعُونَ ٢Waɗanda suke a cikin sallarsu mãsu tawãli'u ne وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَنِ ٱللَّغۡوِ مُعۡرِضُونَ ٣Kuma waɗanda suke, sũdaga barin yasassar magana, mãsu kau da kai ne وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِلزَّكَوٰةِ فَٰعِلُونَ ٤Kuma waɗanda suke ga zakka mãsu aikatãwa ne وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ ٥Kuma waɗanda suke ga farjõjinsu mãsu tsarẽwa ne إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ ٦Fãce a kan mãtan aurensu, kõ kuwa abin da hannayen dãmansu suka mallaka to lalle sũ bã waɗanda ake zargi, ba, ne فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ ٧Sabõda haka wanda ya nẽmi abin da ke bãyan wancan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙẽtarẽwar haddi وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ ٨Kuma waɗanda suke, sũga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَوَٰتِهِمۡ يُحَافِظُونَ ٩Kuma da waɗanda suke, sũ a kan sallõlinsu sunã tsarẽwa أُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡوَٰرِثُونَ ١٠Waɗannan, sũ ne magãda ٱلَّذِينَ يَرِثُونَ ٱلۡفِرۡدَوۡسَ هُمۡ فِيهَا خَٰلِدُونَ ١١Waɗanda suke gãdõn (Aljannar) Firdausi, su a cikinta madawwama ne وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا ٱلۡإِنسَٰنَ مِن سُلَٰلَةٍ مِّن طِينٍ ١٢Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga lãka ثُمَّ جَعَلۡنَٰهُ نُطۡفَةً فِي قَرَارٍ مَّكِينٍ ١٣Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya ثُمَّ خَلَقۡنَا ٱلنُّطۡفَةَ عَلَقَةً فَخَلَقۡنَا ٱلۡعَلَقَةَ مُضۡغَةً فَخَلَقۡنَا ٱلۡمُضۡغَةَ عِظَٰمًا فَكَسَوۡنَا ٱلۡعِظَٰمَ لَحۡمًا ثُمَّ أَنشَأۡنَٰهُ خَلۡقًا ءَاخَرَۚ فَتَبَارَكَ ٱللَّهُ أَحۡسَنُ ٱلۡخَٰلِقِينَ ١٤Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsõka, sa'an nan Muka halitta tsõkar ta zama ƙasũsuwa, sa'an nan Muka tufãtar da ƙasũsuwan da wani nãma sa'an nan kuma Muka ƙãga shi wata halitta dabam. Sabõda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyaun mãsu halittawa ثُمَّ إِنَّكُم بَعۡدَ ذَٰلِكَ لَمَيِّتُونَ ١٥Sa'an nan kuma ku, bãyan wannan, lalle ne masu mutuwa ne ثُمَّ إِنَّكُمۡ يَوۡمَ ٱلۡقِيَٰمَةِ تُبۡعَثُونَ ١٦Sa'an nan kuma lalle ne kũ a Rãnar ¡iyãma, za a iãyar da ku وَلَقَدۡ خَلَقۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعَ طَرَآئِقَ وَمَا كُنَّا عَنِ ٱلۡخَلۡقِ غَٰفِلِينَ ١٧Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun halitta, a samanku, hanyõyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Mãsu shagala ba وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلسَّمَآءِ مَآءَۢ بِقَدَرٍ فَأَسۡكَنَّٰهُ فِي ٱلۡأَرۡضِۖ وَإِنَّا عَلَىٰ ذَهَابِۭ بِهِۦ لَقَٰدِرُونَ ١٨Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhãli, lalle ne Mũ, a kan tafiyar da shi, Mãsu iyãwa ne فَأَنشَأۡنَا لَكُم بِهِۦ جَنَّٰتٍ مِّن نَّخِيلٍ وَأَعۡنَٰبٍ لَّكُمۡ فِيهَا فَوَٰكِهُ كَثِيرَةٌ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ ١٩Sai Muka ƙãga muku, game da shi (ruwan), gõnaki daga daĩnai da inabõbi, kunã da, a cikinsu, 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, kuma daga gare su kuke ci وَشَجَرَةً تَخۡرُجُ مِن طُورِ سَيۡنَآءَ تَنۢبُتُ بِٱلدُّهۡنِ وَصِبۡغٍ لِّلۡأٓكِلِينَ ٢٠Da wata itãciya, tanã fita daga dũtsin Sainã'a, tanã tsira da man shãfãwa, da man miya dõmin masu cĩ وَإِنَّ لَكُمۡ فِي ٱلۡأَنۡعَٰمِ لَعِبۡرَةًۖ نُّسۡقِيكُم مِّمَّا فِي بُطُونِهَا وَلَكُمۡ فِيهَا مَنَٰفِعُ كَثِيرَةٌ وَمِنۡهَا تَأۡكُلُونَ ٢١Kuma lalle ne kunã da abin lũra a cikin dabbõbin ni'imõmi Munã shãyar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kunã da a cikinsu abũbuwan amfãni mãsu yawa, kuma daga gare su kuke cĩ وَعَلَيۡهَا وَعَلَى ٱلۡفُلۡكِ تُحۡمَلُونَ ٢٢Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا نُوحًا إِلَىٰ قَوۡمِهِۦ فَقَالَ يَٰقَوۡمِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ ٢٣Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun aika Nũhu zuwa ga mutãnensa, sai ya ce: "Yã mutãnẽna! Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa waninsa. Shin, to, bã za ku yi taƙawa ba فَقَالَ ٱلۡمَلَؤُاْ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ مِن قَوۡمِهِۦ مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٌ مِّثۡلُكُمۡ يُرِيدُ أَن يَتَفَضَّلَ عَلَيۡكُمۡ وَلَوۡ شَآءَ ٱللَّهُ لَأَنزَلَ مَلَٰٓئِكَةً مَّا سَمِعۡنَا بِهَٰذَا فِيٓ ءَابَآئِنَا ٱلۡأَوَّلِينَ ٢٤Sai mashãwarta waɗanda suka kãfirta daga mutãnensa, suka ce: "Wannan ba kõwa ba ne, fãce mutum misãlinku, yanã nufin ya ɗaukaka a kanku. Dã Allah Yã so, lalle ne dã Yã saukar da Malã'iku, Ba muji (kõme) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلُۢ بِهِۦ جِنَّةٌ فَتَرَبَّصُواْ بِهِۦ حَتَّىٰ حِينٍ ٢٥Shi bai zamo kõwa ba fãce wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lõkaci قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ ٢٦Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimakeni sabõda sun ƙaryatani فَأَوۡحَيۡنَآ إِلَيۡهِ أَنِ ٱصۡنَعِ ٱلۡفُلۡكَ بِأَعۡيُنِنَا وَوَحۡيِنَا فَإِذَا جَآءَ أَمۡرُنَا وَفَارَ ٱلتَّنُّورُ فَٱسۡلُكۡ فِيهَا مِن كُلٍّ زَوۡجَيۡنِ ٱثۡنَيۡنِ وَأَهۡلَكَ إِلَّا مَن سَبَقَ عَلَيۡهِ ٱلۡقَوۡلُ مِنۡهُمۡۖ وَلَا تُخَٰطِبۡنِي فِي ٱلَّذِينَ ظَلَمُوٓاْ إِنَّهُم مُّغۡرَقُونَ ٢٧Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idonMu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya jẽ, kuma tandã ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kõme, ma'aura biyu, da iyãlanka, sai wanda Magana ta gabãta a kansa, daga gare su, kuma kada ka rõƙẽ Ni (sabõda wani) a cikin waɗanda suka yi zãlunci, lalle ne sũ waɗanda ake nutsarwa ne فَإِذَا ٱسۡتَوَيۡتَ أَنتَ وَمَن مَّعَكَ عَلَى ٱلۡفُلۡكِ فَقُلِ ٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ ٱلَّذِي نَجَّىٰنَا مِنَ ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ ٢٨Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tãre da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsĩrar damu daga mutãne azzãlumai وَقُل رَّبِّ أَنزِلۡنِي مُنزَلًا مُّبَارَكًا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلۡمُنزِلِينَ ٢٩Kuma ka ce: 'Ya Ubangijĩna! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu saukarwa إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَأٓيَٰتٍ وَإِن كُنَّا لَمُبۡتَلِينَ ٣٠Lalle ne a cikin wancan akwai ãyõyi, ko da yake Mun kasance, haƙẽƙa' Mãsu jarrabãwa ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قَرۡنًا ءَاخَرِينَ ٣١Sa'an nan kuma Muka ƙãga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bãyansu فَأَرۡسَلۡنَا فِيهِمۡ رَسُولًا مِّنۡهُمۡ أَنِ ٱعۡبُدُواْ ٱللَّهَ مَا لَكُم مِّنۡ إِلَٰهٍ غَيۡرُهُۥٓۚ أَفَلَا تَتَّقُونَ ٣٢Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Bã ku da wani abin bautãwa, sai Shi. Shin to, bã zã ku yi taƙawa ba وَقَالَ ٱلۡمَلَأُ مِن قَوۡمِهِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ وَكَذَّبُواْ بِلِقَآءِ ٱلۡأٓخِرَةِ وَأَتۡرَفۡنَٰهُمۡ فِي ٱلۡحَيَوٰةِ ٱلدُّنۡيَا مَا هَٰذَآ إِلَّا بَشَرٌ مِّثۡلُكُمۡ يَأۡكُلُ مِمَّا تَأۡكُلُونَ مِنۡهُ وَيَشۡرَبُ مِمَّا تَشۡرَبُونَ ٣٣Mashãwarta daga mutãnensa, waɗanda suka kãfirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lãhira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rãyuwar dũniya, suka ce: "Wannan bã kõwa ba fãce wani mutum ne kamarku, yanã cĩ daga abin da kuke cĩ daga gare shi, kuma yanã shã daga abin da kuke shã وَلَئِنۡ أَطَعۡتُم بَشَرًا مِّثۡلَكُمۡ إِنَّكُمۡ إِذًا لَّخَٰسِرُونَ ٣٤Kuma lalle ne idan kun yi ɗã' a ga mutum misãlinku, lalle ne, a lõkacin nan, haƙĩƙa, kũ mãsu hasãra ne أَيَعِدُكُمۡ أَنَّكُمۡ إِذَا مِتُّمۡ وَكُنتُمۡ تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَنَّكُم مُّخۡرَجُونَ ٣٥Shin, yanã yi muku wa'adin (cẽwa) lalle kũ, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓãya da ɓasũsuwa lalle ne kũ waɗanda ake fitarwa ne ۞ هَيۡهَاتَ هَيۡهَاتَ لِمَا تُوعَدُونَ ٣٦Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi إِنۡ هِيَ إِلَّا حَيَاتُنَا ٱلدُّنۡيَا نَمُوتُ وَنَحۡيَا وَمَا نَحۡنُ بِمَبۡعُوثِينَ ٣٧Rãyuwa ba ta zama ba fãce rãyuwarmu ta dũniya, munã mutuwa kuma munã rãyuwa, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba إِنۡ هُوَ إِلَّا رَجُلٌ ٱفۡتَرَىٰ عَلَى ٱللَّهِ كَذِبًا وَمَا نَحۡنُ لَهُۥ بِمُؤۡمِنِينَ ٣٨Bai zama kõwa ba fãce namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, sabõda shi, mãsu ĩmãni ba قَالَ رَبِّ ٱنصُرۡنِي بِمَا كَذَّبُونِ ٣٩Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka taimake ni sabõda sun ƙaryatã ni قَالَ عَمَّا قَلِيلٍ لَّيُصۡبِحُنَّ نَٰدِمِينَ ٤٠Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne zã su wãyi gari sunã mãsu nadãma فَأَخَذَتۡهُمُ ٱلصَّيۡحَةُ بِٱلۡحَقِّ فَجَعَلۡنَٰهُمۡ غُثَآءًۚ فَبُعۡدًا لِّلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ ٤١Sai tsãwa ta kãma su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Sabõda haka nĩsa ya tabbataga mutãne azzãlumai ثُمَّ أَنشَأۡنَا مِنۢ بَعۡدِهِمۡ قُرُونًا ءَاخَرِينَ ٤٢Sa'an kuma Muka ƙãga halittar wasu ƙarnõni dabam daga bayãnsu مَا تَسۡبِقُ مِنۡ أُمَّةٍ أَجَلَهَا وَمَا يَسۡتَـٔۡخِرُونَ ٤٣Wata al'umma bã ta gabãtar ajalinta, kuma bã zã su jinkirta ba ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا رُسُلَنَا تَتۡرَاۖ كُلَّ مَا جَآءَ أُمَّةً رَّسُولُهَا كَذَّبُوهُۖ فَأَتۡبَعۡنَا بَعۡضَهُم بَعۡضًا وَجَعَلۡنَٰهُمۡ أَحَادِيثَۚ فَبُعۡدًا لِّقَوۡمٍ لَّا يُؤۡمِنُونَ ٤٤Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jẽre a kõda yaushe Manzon wata al'umma ya jẽ mata, sai su ƙaryata shi, sabõda haka Muka biyar da sãshensu ga sãshe, kuma Muka sanya su lãbãrun hĩra. To, nĩsa ya tabbata ga mutãne (waɗanda) bã su yin ĩmãni ثُمَّ أَرۡسَلۡنَا مُوسَىٰ وَأَخَاهُ هَٰرُونَ بِـَٔايَٰتِنَا وَسُلۡطَٰنٍ مُّبِينٍ ٤٥Sa'an nan kuma Muka aika Mũsã da ɗan'uwansa Hãrũna, game da ãyõyinMu da, dalĩli bayyananne إِلَىٰ فِرۡعَوۡنَ وَمَلَإِيْهِۦ فَٱسۡتَكۡبَرُواْ وَكَانُواْ قَوۡمًا عَالِينَ ٤٦Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhãli sun kasance mutãne ne marinjãya فَقَالُوٓاْ أَنُؤۡمِنُ لِبَشَرَيۡنِ مِثۡلِنَا وَقَوۡمُهُمَا لَنَا عَٰبِدُونَ ٤٧Sai suka ce: "Shin, zã Mu yi ĩmãni sabõda wasu mutãne biyu misãlinmu, alhãli kuwa mutãnensu a gare mu, mãsu bauta ne فَكَذَّبُوهُمَا فَكَانُواْ مِنَ ٱلۡمُهۡلَكِينَ ٤٨Sai suka ƙaryata su sabõda haka suka kasance halakakku وَلَقَدۡ ءَاتَيۡنَا مُوسَى ٱلۡكِتَٰبَ لَعَلَّهُمۡ يَهۡتَدُونَ ٤٩Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun bai wa Mũsã littãfi tsammaninsu zã su shiryu وَجَعَلۡنَا ٱبۡنَ مَرۡيَمَ وَأُمَّهُۥٓ ءَايَةً وَءَاوَيۡنَٰهُمَآ إِلَىٰ رَبۡوَةٍ ذَاتِ قَرَارٍ وَمَعِينٍ ٥٠Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata ãyã Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abũcin natsuwa da marẽmari يَٰٓأَيُّهَا ٱلرُّسُلُ كُلُواْ مِنَ ٱلطَّيِّبَٰتِ وَٱعۡمَلُواْ صَٰلِحًاۖ إِنِّي بِمَا تَعۡمَلُونَ عَلِيمٌ ٥١Yã ku Manzanni! Ku ci daga abũbuwa mãsu dãɗi kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Nĩga abin da kuke aikatãwa, Masani ne وَإِنَّ هَٰذِهِۦٓ أُمَّتُكُمۡ أُمَّةً وَٰحِدَةً وَأَنَا۠ رَبُّكُمۡ فَٱتَّقُونِ ٥٢Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Nĩ, Ubangijinku ne, sai ku bĩ Ni da taƙawa فَتَقَطَّعُوٓاْ أَمۡرَهُم بَيۡنَهُمۡ زُبُرًاۖ كُلُّ حِزۡبِۭ بِمَا لَدَيۡهِمۡ فَرِحُونَ ٥٣Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakãninsu guntu-guntu, kõwace ƙungiya sunã mãsu farin ciki da abin da yake a gare su فَذَرۡهُمۡ فِي غَمۡرَتِهِمۡ حَتَّىٰ حِينٍ ٥٤To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lõkaci أَيَحۡسَبُونَ أَنَّمَا نُمِدُّهُم بِهِۦ مِن مَّالٍ وَبَنِينَ ٥٥Shin, sunã zaton cẽwa abin da Muke taimakon su da shi daga dũkiya da ɗiya نُسَارِعُ لَهُمۡ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِۚ بَل لَّا يَشۡعُرُونَ ٥٦Munã yi musu gaggãwa ne a cikin alhẽrõri إِنَّ ٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ خَشۡيَةِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ ٥٧Lalle ne waɗanda suke mãsu sauna sabo da tsõron Ubangijinsu وَٱلَّذِينَ هُم بِـَٔايَٰتِ رَبِّهِمۡ يُؤۡمِنُونَ ٥٨Da waɗanda suke, game da ãyõyin Ubangijinsu sunã ĩmãni وَٱلَّذِينَ هُم بِرَبِّهِمۡ لَا يُشۡرِكُونَ ٥٩Da waɗanda suke game da Ubangijinsu bã su yin shirki وَٱلَّذِينَ يُؤۡتُونَ مَآ ءَاتَواْ وَّقُلُوبُهُمۡ وَجِلَةٌ أَنَّهُمۡ إِلَىٰ رَبِّهِمۡ رَٰجِعُونَ ٦٠Da waɗanda ke bãyar da abin da suka bãyar, alhãli kuwa zukãtansu sunã tsõrace dõmin sunã kõmãwa zuwa ga Ubangijinsu أُوْلَٰٓئِكَ يُسَٰرِعُونَ فِي ٱلۡخَيۡرَٰتِ وَهُمۡ لَهَا سَٰبِقُونَ ٦١Waɗancan sunã gaggãwar tsẽre a cikin ayyukan alhẽri, alhãli kuwa sunã mãsu tsẽrẽwa zuwa gare su (ayyukan alhẽri) وَلَا نُكَلِّفُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ وَلَدَيۡنَا كِتَٰبٌ يَنطِقُ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ لَا يُظۡلَمُونَ ٦٢Kuma bã Mu kallafa wa rai fãce abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littãfi wanda yake magana da gakiya, kuma sũ bã a zãluntar su بَلۡ قُلُوبُهُمۡ فِي غَمۡرَةٍ مِّنۡ هَٰذَا وَلَهُمۡ أَعۡمَٰلٌ مِّن دُونِ ذَٰلِكَ هُمۡ لَهَا عَٰمِلُونَ ٦٣Ã'a, zukãtansu sunã cikin jãhilci daga wannan (magana), kuma sunã da waɗansu ayyuka, baicin wancan, sũ a gare su, mãsu aikatãwa ne حَتَّىٰٓ إِذَآ أَخَذۡنَا مُتۡرَفِيهِم بِٱلۡعَذَابِ إِذَا هُمۡ يَجۡـَٔرُونَ ٦٤Har idan Mun kãma mani'imtansu da azãba, sai gã su sunã hargõwa لَا تَجۡـَٔرُواْ ٱلۡيَوۡمَۖ إِنَّكُم مِّنَّا لَا تُنصَرُونَ ٦٥Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne kũ, daga gare Mu bã a taimakon ku قَدۡ كَانَتۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُمۡ عَلَىٰٓ أَعۡقَٰبِكُمۡ تَنكِصُونَ ٦٦Lalle ne, ãyõyĩNa sun kasance anã karãtun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugãduganku, kunã kõmãwa bãya مُسۡتَكۡبِرِينَ بِهِۦ سَٰمِرًا تَهۡجُرُونَ ٦٧Kunã mãsu girman kai gare shi (Annabi), da hĩrã kunã alfãsha أَفَلَمۡ يَدَّبَّرُواْ ٱلۡقَوۡلَ أَمۡ جَآءَهُم مَّا لَمۡ يَأۡتِ ءَابَآءَهُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٦٨Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ãni) ba, kõ abin da bai jẽ wa ubanninsu na farko ba ne ya jẽ musu أَمۡ لَمۡ يَعۡرِفُواْ رَسُولَهُمۡ فَهُمۡ لَهُۥ مُنكِرُونَ ٦٩Kõ ba su san Manzonsu ba ne dõmin haka suke mãsu musu a gare shi أَمۡ يَقُولُونَ بِهِۦ جِنَّةُۢۚ بَلۡ جَآءَهُم بِٱلۡحَقِّ وَأَكۡثَرُهُمۡ لِلۡحَقِّ كَٰرِهُونَ ٧٠Kõ sunã cẽwa, "Akwai hauka gare shi?" Ã'a, yã zo musu da gaskiya, alhãli kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, mãsu ƙi ne وَلَوِ ٱتَّبَعَ ٱلۡحَقُّ أَهۡوَآءَهُمۡ لَفَسَدَتِ ٱلسَّمَٰوَٰتُ وَٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهِنَّۚ بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِذِكۡرِهِمۡ فَهُمۡ عَن ذِكۡرِهِم مُّعۡرِضُونَ ٧١Kuma dã gaskiya (Alƙur'ãni) yã bi son zuciyoyinsu, haƙĩƙa dã sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓãci. Ã'a, Mun tafo musu da ambaton (darajar) su, sa'an nan sũ daga barin ambaton su mãsu bijirẽwa ne, bijirẽwa أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ خَرۡجًا فَخَرَاجُ رَبِّكَ خَيۡرٌۖ وَهُوَ خَيۡرُ ٱلرَّٰزِقِينَ ٧٢Kõ kanã tambayar su wani harãji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harãjin Ubangijinka ne mafi alhẽri kuma Shĩ ne Mafi alhẽrin mãsu ciyarwa وَإِنَّكَ لَتَدۡعُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطٍ مُّسۡتَقِيمٍ ٧٣Kuma lalle ne kai haƙĩƙa kanã kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya وَإِنَّ ٱلَّذِينَ لَا يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡأٓخِرَةِ عَنِ ٱلصِّرَٰطِ لَنَٰكِبُونَ ٧٤Kuma lalle waɗanda ba su yi ĩmãni da Lãhira ba mãsu karkacẽwa daga hanya ne ۞ وَلَوۡ رَحِمۡنَٰهُمۡ وَكَشَفۡنَا مَا بِهِم مِّن ضُرٍّ لَّلَجُّواْ فِي طُغۡيَٰنِهِمۡ يَعۡمَهُونَ ٧٥Kuma dã Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tãre da su na cũta, lalle ne dã sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, sunã ɗimuwa وَلَقَدۡ أَخَذۡنَٰهُم بِٱلۡعَذَابِ فَمَا ٱسۡتَكَانُواْ لِرَبِّهِمۡ وَمَا يَتَضَرَّعُونَ ٧٦Kuma lalle ne haƙĩƙa Munã kãma su da azãba sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama bã su yin tawãli'u حَتَّىٰٓ إِذَا فَتَحۡنَا عَلَيۡهِم بَابًا ذَا عَذَابٍ شَدِيدٍ إِذَا هُمۡ فِيهِ مُبۡلِسُونَ ٧٧Har idan Mun bũɗe, akansu, wata ƙõfa mai azãba mai tsanani sai gã su a cikinta sunã mãsu mugi وَهُوَ ٱلَّذِيٓ أَنشَأَ لَكُمُ ٱلسَّمۡعَ وَٱلۡأَبۡصَٰرَ وَٱلۡأَفۡـِٔدَةَۚ قَلِيلًا مَّا تَشۡكُرُونَ ٧٨Kuma Shi ne Wanda Ya ƙãga halittar ji da gani da zukãta dominku. Kaɗan ƙwarai kuke gõdẽwa وَهُوَ ٱلَّذِي ذَرَأَكُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ وَإِلَيۡهِ تُحۡشَرُونَ ٧٩Kuma Shĩ ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tãyar da ku وَهُوَ ٱلَّذِي يُحۡيِۦ وَيُمِيتُ وَلَهُ ٱخۡتِلَٰفُ ٱلَّيۡلِ وَٱلنَّهَارِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ ٨٠Kuma Shĩ ne Wanda Yake rãyarwa, kuma Yanã matarwa, kuma a gare Shi ne sãɓawar dare da yini take. Shin, to, bã zã ku hankalta ba بَلۡ قَالُواْ مِثۡلَ مَا قَالَ ٱلۡأَوَّلُونَ ٨١Ã'a, sun faɗi misãlin abin da na farko suka faɗa قَالُوٓاْ أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ ٨٢Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasũsuwa shin lal1e ne mu haƙĩƙa waɗanda ake tãyarwa ne لَقَدۡ وُعِدۡنَا نَحۡنُ وَءَابَآؤُنَا هَٰذَا مِن قَبۡلُ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّآ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٨٣Lalle ne, haƙĩƙa, an yi mana wa'adi, mũ da ubanninmu ga wannan a gabãni, wannan abu bai zama kõme ba, fãce tãtsũniyõyin na farko قُل لِّمَنِ ٱلۡأَرۡضُ وَمَن فِيهَآ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ٨٤Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kunã sani سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَذَكَّرُونَ ٨٥Zã su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku yi tunãni ba قُلۡ مَن رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ ٱلسَّبۡعِ وَرَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡعَظِيمِ ٨٦Ka ce: "Wãne ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ أَفَلَا تَتَّقُونَ ٨٧Zã su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, bã zã ku bĩ Shi da taƙawa ba قُلۡ مَنۢ بِيَدِهِۦ مَلَكُوتُ كُلِّ شَيۡءٍ وَهُوَ يُجِيرُ وَلَا يُجَارُ عَلَيۡهِ إِن كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ٨٨Ka ce: "Wãne ne ga hannunsa mallakar kõwane abu take alhãli kuwa shi yanã tsarẽwar wani, kuma ba a tsare kõwa daga gare shi, idan kun kasance kunã sani سَيَقُولُونَ لِلَّهِۚ قُلۡ فَأَنَّىٰ تُسۡحَرُونَ ٨٩Zã su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yãya ake sihirce ku بَلۡ أَتَيۡنَٰهُم بِٱلۡحَقِّ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ ٩٠Ã'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne sũ, haƙĩƙa, maƙaryata ne مَا ٱتَّخَذَ ٱللَّهُ مِن وَلَدٍ وَمَا كَانَ مَعَهُۥ مِنۡ إِلَٰهٍۚ إِذًا لَّذَهَبَ كُلُّ إِلَٰهِۭ بِمَا خَلَقَ وَلَعَلَا بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ ٩١Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma bãbu wani abin bautãwa tãre da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne dã kõwane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, dã waɗansu sun rinjãya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantãwa عَٰلِمِ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِ فَتَعَٰلَىٰ عَمَّا يُشۡرِكُونَ ٩٢Masanin ɓõye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka قُل رَّبِّ إِمَّا تُرِيَنِّي مَا يُوعَدُونَ ٩٣Ka ce: "Yã Ubangijina! Ko dai Ka nũna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi رَبِّ فَلَا تَجۡعَلۡنِي فِي ٱلۡقَوۡمِ ٱلظَّٰلِمِينَ ٩٤Yã Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutãne azzãlumai وَإِنَّا عَلَىٰٓ أَن نُّرِيَكَ مَا نَعِدُهُمۡ لَقَٰدِرُونَ ٩٥Kuma lalle ne Mũ haƙĩƙa Mãsu iyawa ne a kan Mu nũna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi ٱدۡفَعۡ بِٱلَّتِي هِيَ أَحۡسَنُ ٱلسَّيِّئَةَۚ نَحۡنُ أَعۡلَمُ بِمَا يَصِفُونَ ٩٦Ka tunkuɗe cũta da wadda take ita ce mafi kyau. Mũ neMafi sani game da abin da suke siffantãwa وَقُل رَّبِّ أَعُوذُ بِكَ مِنۡ هَمَزَٰتِ ٱلشَّيَٰطِينِ ٩٧Ka ce: "Yã Ubangijĩna, inã nẽman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗãnu وَأَعُوذُ بِكَ رَبِّ أَن يَحۡضُرُونِ ٩٨Kuma inã nẽman tsari da Kai, ya Ubangijĩna! Dõmin kada su halarto ni حَتَّىٰٓ إِذَا جَآءَ أَحَدَهُمُ ٱلۡمَوۡتُ قَالَ رَبِّ ٱرۡجِعُونِ ٩٩Har idan mutuwa ta jẽ wa ɗayansu, sai ya ce: "Yã Ubangijina, Ku mayar da ni (dũniya) لَعَلِّيٓ أَعۡمَلُ صَٰلِحًا فِيمَا تَرَكۡتُۚ كـَلَّآۚ إِنَّهَا كَلِمَةٌ هُوَ قَآئِلُهَاۖ وَمِن وَرَآئِهِم بَرۡزَخٌ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ ١٠٠Tsammãnina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shĩ ne mafaɗinta, alhãli kuwa a bãya gare su akwai wani shãmaki har rãnar da zã a tãyar da su فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ فَلَآ أَنسَابَ بَيۡنَهُمۡ يَوۡمَئِذٍ وَلَا يَتَسَآءَلُونَ ١٠١Sa'an nan idan an yi bũsa a cikin ƙaho, to, bãbu dangantakõki a tsakãninsu a rãnar nan kuma bã zã su tambayi jũnansu ba فَمَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ١٠٢To, wadanda sikẽlinsu ya yi nauyi, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo وَمَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ فَأُوْلَٰٓئِكَ ٱلَّذِينَ خَسِرُوٓاْ أَنفُسَهُمۡ فِي جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ ١٠٣Kuma waɗanda sikẽlinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu sunã madawwama a cikin Jahannama تَلۡفَحُ وُجُوهَهُمُ ٱلنَّارُ وَهُمۡ فِيهَا كَٰلِحُونَ ١٠٤Fuskokinsu sunã balbalar wuta, kuma su a cikinta mãsu yãgaggun leɓɓa daga haƙõra ne أَلَمۡ تَكُنۡ ءَايَٰتِي تُتۡلَىٰ عَلَيۡكُمۡ فَكُنتُم بِهَا تُكَذِّبُونَ ١٠٥Shin, ayõyĩNa ba su kasance anã karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kunã ƙaryatãwa قَالُواْ رَبَّنَا غَلَبَتۡ عَلَيۡنَا شِقۡوَتُنَا وَكُنَّا قَوۡمًا ضَآلِّينَ ١٠٦Suka ce: "Yã Ubangijinmu, shaƙãwamiu ce ta rinjãya a kanmu, kuma mun kasance mutãne ɓatattu رَبَّنَآ أَخۡرِجۡنَا مِنۡهَا فَإِنۡ عُدۡنَا فَإِنَّا ظَٰلِمُونَ ١٠٧Yã Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun kõma, to, lalle ne, mũ ne mãsu zãlunci قَالَ ٱخۡسَـُٔواْ فِيهَا وَلَا تُكَلِّمُونِ ١٠٨Ya ce: "Ku tafi (da wulãkanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana إِنَّهُۥ كَانَ فَرِيقٌ مِّنۡ عِبَادِي يَقُولُونَ رَبَّنَآ ءَامَنَّا فَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَا وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰحِمِينَ ١٠٩Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bãyiNa sun kasance sunã cẽwa, "Yã Ubangijinmu! Mun yi ĩmãni, sai Ka gãfarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu tausayi فَٱتَّخَذۡتُمُوهُمۡ سِخۡرِيًّا حَتَّىٰٓ أَنسَوۡكُمۡ ذِكۡرِي وَكُنتُم مِّنۡهُمۡ تَضۡحَكُونَ ١١٠Sai kuka riƙe su lẽburõri har suka mantar da ku ambatõNa kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dãriya إِنِّي جَزَيۡتُهُمُ ٱلۡيَوۡمَ بِمَا صَبَرُوٓاْ أَنَّهُمۡ هُمُ ٱلۡفَآئِزُونَ ١١١Lalle ne Nĩ Inã sãka musu a yau, sabõda abin da suka yi wa haƙuri. Dõmin lalle ne sũ sũ ne mãsu sãmun babban rabo قَٰلَ كَمۡ لَبِثۡتُمۡ فِي ٱلۡأَرۡضِ عَدَدَ سِنِينَ ١١٢Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidãyar shẽkaru قَالُواْ لَبِثۡنَا يَوۡمًا أَوۡ بَعۡضَ يَوۡمٍ فَسۡـَٔلِ ٱلۡعَآدِّينَ ١١٣Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi mãsu ƙidãyãwa قَٰلَ إِن لَّبِثۡتُمۡ إِلَّا قَلِيلًاۖ لَّوۡ أَنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَعۡلَمُونَ ١١٤Ya ce: "Ba ku zauna ba fãce kaɗan, dã dai kun kasance kunã sani أَفَحَسِبۡتُمۡ أَنَّمَا خَلَقۡنَٰكُمۡ عَبَثًا وَأَنَّكُمۡ إِلَيۡنَا لَا تُرۡجَعُونَ ١١٥Shin, to, kun yi zaton cẽwa Mun halitta ku ne da wãsa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, bã zã ku kõmo ba فَتَعَٰلَى ٱللَّهُ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡحَقُّۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ رَبُّ ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡكَرِيمِ ١١٦Allah Mamallaki gaskiya, Yã ɗaukaka. Bãbu abin bautãwa, fãce Shi. Shĩ ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja وَمَن يَدۡعُ مَعَ ٱللَّهِ إِلَٰهًا ءَاخَرَ لَا بُرۡهَٰنَ لَهُۥ بِهِۦ فَإِنَّمَا حِسَابُهُۥ عِندَ رَبِّهِۦٓۚ إِنَّهُۥ لَا يُفۡلِحُ ٱلۡكَٰفِرُونَ ١١٧Kuma wanda ya kira, tãre da Allah, waɗansu abũbuwan bautãwa na dabam, bã yanã da wani dalĩli game da shĩ (kiran) ba, to hisãbinsa yanã wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kãfirai bã su cin nasara وَقُل رَّبِّ ٱغۡفِرۡ وَٱرۡحَمۡ وَأَنتَ خَيۡرُ ٱلرَّٰحِمِينَ ١١٨Kuma ka ce: "Yã Ubangijina! Ka yi gãfara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alhẽrin mãsu rahama

الترجمة: Abubakar Mahmoud Gumi.