بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
عَمَّ يَتَسَآءَلُونَ ١A kan mẽ suke tambayar jũna عَنِ ٱلنَّبَإِ ٱلۡعَظِيمِ ٢A kan muhimmin lãbãri mai girma (Alƙur'ãni) ٱلَّذِي هُمۡ فِيهِ مُخۡتَلِفُونَ ٣Wanda suke sãɓa wa jũna a cikinsa كـَلَّا سَيَعۡلَمُونَ ٤A'aha! Zã su sani ثُمَّ كـَلَّا سَيَعۡلَمُونَ ٥Kuma, a'aha! Zã su sani أَلَمۡ نَجۡعَلِ ٱلۡأَرۡضَ مِهَٰدًا ٦Ashe, ba Mu sanya ƙasa shimfiɗa ba وَٱلۡجِبَالَ أَوۡتَادًا ٧Da duwãtsu turaku (ga riƙe ƙasa) وَخَلَقۡنَٰكُمۡ أَزۡوَٰجًا ٨Kuma, Mun halitta ku mazã da mãtã وَجَعَلۡنَا نَوۡمَكُمۡ سُبَاتًا ٩Kuma, Muka sanya barcinku hũtãwa وَجَعَلۡنَا ٱلَّيۡلَ لِبَاسًا ١٠Kuma, Muka sanya dare (ya zama) sutura وَجَعَلۡنَا ٱلنَّهَارَ مَعَاشًا ١١Kuma, Muka sanya yini (yazama) lõkacin nẽman abinci وَبَنَيۡنَا فَوۡقَكُمۡ سَبۡعًا شِدَادًا ١٢Kuma, Muka gina, a samanku, sammai bakwai mãsu ƙarfi وَجَعَلۡنَا سِرَاجًا وَهَّاجًا ١٣Kuma, Muka sanya fitila mai tsanin haske (rãnã) وَأَنزَلۡنَا مِنَ ٱلۡمُعۡصِرَٰتِ مَآءً ثَجَّاجًا ١٤Kuma, Muka saukar daga cikakkun girãgizai, ruwa mai yawan zuba لِّنُخۡرِجَ بِهِۦ حَبًّا وَنَبَاتًا ١٥Dõmin, Mu fitar da ƙwaya da tsiri game da shi وَجَنَّٰتٍ أَلۡفَافًا ١٦Da itãcen lambuna mãsu lillibniya إِنَّ يَوۡمَ ٱلۡفَصۡلِ كَانَ مِيقَٰتًا ١٧Lalle ne, rãnar rarrabẽwa tã kasance abin ƙayyadẽ wa lõkaci يَوۡمَ يُنفَخُ فِي ٱلصُّورِ فَتَأۡتُونَ أَفۡوَاجًا ١٨Rãnar da zã a yi bũsa a cikin ƙaho, sai ku zo, jama'a jama'a وَفُتِحَتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ أَبۡوَٰبًا ١٩Kuma, aka buɗe sama, sai ta kasance ƙõfõfi وَسُيِّرَتِ ٱلۡجِبَالُ فَكَانَتۡ سَرَابًا ٢٠Kuma, aka tafiyar da duwãtsu, sai suka kasance ƙũra إِنَّ جَهَنَّمَ كَانَتۡ مِرۡصَادًا ٢١Lalle ne, Jahannama tã kasance madãkata لِّلطَّٰغِينَ مَـَٔابًا ٢٢Ga mãsu ƙẽtare iyãkõki, tã zama makõma لَّٰبِثِينَ فِيهَآ أَحۡقَابًا ٢٣Sunã, mãsu zama a cikinta, zãmunna لَّا يَذُوقُونَ فِيهَا بَرۡدًا وَلَا شَرَابًا ٢٤Bã su ɗanɗanãwar wani sanyi a cikinta, kuma bã su ɗanɗana abin sha إِلَّا حَمِيمًا وَغَسَّاقًا ٢٥Fãce tafasasshen ruwa da ruɓaɓɓen jini جَزَآءً وِفَاقًا ٢٦Sakamako mai dãcẽwa إِنَّهُمۡ كَانُواْ لَا يَرۡجُونَ حِسَابًا ٢٧Lalle ne, sũ, sun kasance bã su fãtar sauƙin wani hisãbi وَكَذَّبُواْ بِـَٔايَٰتِنَا كِذَّابًا ٢٨Kuma, suka ƙaryata game da ãyõyinMu, ƙaryatãwa وَكُلَّ شَيۡءٍ أَحۡصَيۡنَٰهُ كِتَٰبًا ٢٩Alhãli, kõwane abu Mun ƙididdigẽ shi, a rubũce فَذُوقُواْ فَلَن نَّزِيدَكُمۡ إِلَّا عَذَابًا ٣٠Sabõda haka, ku ɗanɗana domin haka, bã zã Mu ƙara muku kõme ba fãce azãba إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ مَفَازًا ٣١Lalle ne, mãsu taƙawã nã da wani wurin sãmun babban rabo حَدَآئِقَ وَأَعۡنَٰبًا ٣٢Lambuna da inabõbi وَكَوَاعِبَ أَتۡرَابًا ٣٣Da cikakkun 'yammata, tsãrar jũna وَكَأۡسًا دِهَاقًا ٣٤Da hinjãlan giya cikakku لَّا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوًا وَلَا كِذَّٰبًا ٣٥Bã su jin yãsassar magana, a cikinta, kuma bã su jin ƙaryatãwa جَزَآءً مِّن رَّبِّكَ عَطَآءً حِسَابًا ٣٦Dõmin sakamako daga Ubangijinka, kyautã mai yawa رَّبِّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا ٱلرَّحۡمَٰنِۖ لَا يَمۡلِكُونَ مِنۡهُ خِطَابًا ٣٧Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakãninsu, Mai rahama, bã su da ikon yin wata magana daga gare Shi يَوۡمَ يَقُومُ ٱلرُّوحُ وَٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ صَفًّاۖ لَّا يَتَكَلَّمُونَ إِلَّا مَنۡ أَذِنَ لَهُ ٱلرَّحۡمَٰنُ وَقَالَ صَوَابًا ٣٨Rãnar da Rũhi da malã'iku zã su tsaya a cikin safu, bã su magana, sai wanda Allah Ya yi masa izni, kuma ya faɗi abin da ke daidai ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلۡحَقُّۖ فَمَن شَآءَ ٱتَّخَذَ إِلَىٰ رَبِّهِۦ مَـَٔابًا ٣٩Wancan, shi ne yini na gaskiya; to wanda ya so, ya riƙa makõma zuwa ga Ubangijinsa إِنَّآ أَنذَرۡنَٰكُمۡ عَذَابًا قَرِيبًا يَوۡمَ يَنظُرُ ٱلۡمَرۡءُ مَا قَدَّمَتۡ يَدَاهُ وَيَقُولُ ٱلۡكَافِرُ يَٰلَيۡتَنِي كُنتُ تُرَٰبَۢا ٤٠Lalle ne, Mũ, Mun yi muku gargaɗin azãba makusanciya, rãnar da mutum ke dũbi zuwa ga abin da hannãyensa suka aikata, kuma kafiri ya ce: "Kaitona, dã dai nã zama turɓãya