بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلصَّٰٓفَّٰتِ صَفًّا ١Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi) فَٱلزَّٰجِرَٰتِ زَجۡرًا ٢Sa'an nan mãsu yin tsãwa dõmin gargaɗi فَٱلتَّٰلِيَٰتِ ذِكۡرًا ٣Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa إِنَّ إِلَٰهَكُمۡ لَوَٰحِدٌ ٤Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne رَّبُّ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا بَيۡنَهُمَا وَرَبُّ ٱلۡمَشَٰرِقِ ٥Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã إِنَّا زَيَّنَّا ٱلسَّمَآءَ ٱلدُّنۡيَا بِزِينَةٍ ٱلۡكَوَاكِبِ ٦Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri وَحِفۡظًا مِّن كُلِّ شَيۡطَٰنٍ مَّارِدٍ ٧Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai لَّا يَسَّمَّعُونَ إِلَى ٱلۡمَلَإِ ٱلۡأَعۡلَىٰ وَيُقۡذَفُونَ مِن كُلِّ جَانِبٍ ٨Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe دُحُورًاۖ وَلَهُمۡ عَذَابٌ وَاصِبٌ ٩Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya إِلَّا مَنۡ خَطِفَ ٱلۡخَطۡفَةَ فَأَتۡبَعَهُۥ شِهَابٌ ثَاقِبٌ ١٠Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَهُمۡ أَشَدُّ خَلۡقًا أَم مَّنۡ خَلَقۡنَآۚ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّن طِينٍ لَّازِبِۭ ١١Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri بَلۡ عَجِبۡتَ وَيَسۡخَرُونَ ١٢Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili وَإِذَا ذُكِّرُواْ لَا يَذۡكُرُونَ ١٣Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa وَإِذَا رَأَوۡاْ ءَايَةً يَسۡتَسۡخِرُونَ ١٤Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili وَقَالُوٓاْ إِنۡ هَٰذَآ إِلَّا سِحۡرٌ مُّبِينٌ ١٥Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ ١٦Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ ١٧Ashe kõ da ubanninmu na farko قُلۡ نَعَمۡ وَأَنتُمۡ دَٰخِرُونَ ١٨Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu فَإِنَّمَا هِيَ زَجۡرَةٌ وَٰحِدَةٌ فَإِذَا هُمۡ يَنظُرُونَ ١٩Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi وَقَالُواْ يَٰوَيۡلَنَا هَٰذَا يَوۡمُ ٱلدِّينِ ٢٠Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako هَٰذَا يَوۡمُ ٱلۡفَصۡلِ ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ٢١Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa ۞ ٱحۡشُرُواْ ٱلَّذِينَ ظَلَمُواْ وَأَزۡوَٰجَهُمۡ وَمَا كَانُواْ يَعۡبُدُونَ ٢٢Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa مِن دُونِ ٱللَّهِ فَٱهۡدُوهُمۡ إِلَىٰ صِرَٰطِ ٱلۡجَحِيمِ ٢٣Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm وَقِفُوهُمۡۖ إِنَّهُم مَّسۡـُٔولُونَ ٢٤Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne مَا لَكُمۡ لَا تَنَاصَرُونَ ٢٥Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna بَلۡ هُمُ ٱلۡيَوۡمَ مُسۡتَسۡلِمُونَ ٢٦Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne وَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ يَتَسَآءَلُونَ ٢٧Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna قَالُوٓاْ إِنَّكُمۡ كُنتُمۡ تَأۡتُونَنَا عَنِ ٱلۡيَمِينِ ٢٨Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince) قَالُواْ بَل لَّمۡ تَكُونُواْ مُؤۡمِنِينَ ٢٩Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيۡكُم مِّن سُلۡطَٰنِۭۖ بَلۡ كُنتُمۡ قَوۡمًا طَٰغِينَ ٣٠Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka فَحَقَّ عَلَيۡنَا قَوۡلُ رَبِّنَآۖ إِنَّا لَذَآئِقُونَ ٣١Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne فَأَغۡوَيۡنَٰكُمۡ إِنَّا كُنَّا غَٰوِينَ ٣٢Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu فَإِنَّهُمۡ يَوۡمَئِذٍ فِي ٱلۡعَذَابِ مُشۡتَرِكُونَ ٣٣To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفۡعَلُ بِٱلۡمُجۡرِمِينَ ٣٤Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi إِنَّهُمۡ كَانُوٓاْ إِذَا قِيلَ لَهُمۡ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا ٱللَّهُ يَسۡتَكۡبِرُونَ ٣٥Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُوٓاْ ءَالِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجۡنُونِۭ ٣٦Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci بَلۡ جَآءَ بِٱلۡحَقِّ وَصَدَّقَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ٣٧Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni إِنَّكُمۡ لَذَآئِقُواْ ٱلۡعَذَابِ ٱلۡأَلِيمِ ٣٨Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne وَمَا تُجۡزَوۡنَ إِلَّا مَا كُنتُمۡ تَعۡمَلُونَ ٣٩Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ٤٠Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake أُوْلَٰٓئِكَ لَهُمۡ رِزۡقٌ مَّعۡلُومٌ ٤١Waɗannan sunã da abinci sananne فَوَٰكِهُ وَهُم مُّكۡرَمُونَ ٤٢Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ ٤٣A cikin gidãjen Aljannar ni'ima عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَٰبِلِينَ ٤٤A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna يُطَافُ عَلَيۡهِم بِكَأۡسٍ مِّن مَّعِينِۭ ٤٥Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari بَيۡضَآءَ لَذَّةٍ لِّلشَّٰرِبِينَ ٤٦Farã mai dãɗi ga mashãyan لَا فِيهَا غَوۡلٌ وَلَا هُمۡ عَنۡهَا يُنزَفُونَ ٤٧A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba وَعِندَهُمۡ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ عِينٌ ٤٨Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu كَأَنَّهُنَّ بَيۡضٌ مَّكۡنُونٌ ٤٩Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ يَتَسَآءَلُونَ ٥٠Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna قَالَ قَآئِلٌ مِّنۡهُمۡ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌ ٥١Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya) يَقُولُ أَءِنَّكَ لَمِنَ ٱلۡمُصَدِّقِينَ ٥٢Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne أَءِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَدِينُونَ ٥٣Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne قَالَ هَلۡ أَنتُم مُّطَّلِعُونَ ٥٤(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi) فَٱطَّلَعَ فَرَءَاهُ فِي سَوَآءِ ٱلۡجَحِيمِ ٥٥Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim قَالَ تَٱللَّهِ إِن كِدتَّ لَتُرۡدِينِ ٥٦Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni وَلَوۡلَا نِعۡمَةُ رَبِّي لَكُنتُ مِنَ ٱلۡمُحۡضَرِينَ ٥٧Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã) أَفَمَا نَحۡنُ بِمَيِّتِينَ ٥٨Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba إِلَّا مَوۡتَتَنَا ٱلۡأُولَىٰ وَمَا نَحۡنُ بِمُعَذَّبِينَ ٥٩Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡعَظِيمُ ٦٠Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma لِمِثۡلِ هَٰذَا فَلۡيَعۡمَلِ ٱلۡعَٰمِلُونَ ٦١Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa أَذَٰلِكَ خَيۡرٌ نُّزُلًا أَمۡ شَجَرَةُ ٱلزَّقُّومِ ٦٢Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm إِنَّا جَعَلۡنَٰهَا فِتۡنَةً لِّلظَّٰلِمِينَ ٦٣Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai إِنَّهَا شَجَرَةٌ تَخۡرُجُ فِيٓ أَصۡلِ ٱلۡجَحِيمِ ٦٤Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm طَلۡعُهَا كَأَنَّهُۥ رُءُوسُ ٱلشَّيَٰطِينِ ٦٥Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne فَإِنَّهُمۡ لَأٓكِلُونَ مِنۡهَا فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ ٦٦To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta ثُمَّ إِنَّ لَهُمۡ عَلَيۡهَا لَشَوۡبًا مِّنۡ حَمِيمٍ ٦٧Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi ثُمَّ إِنَّ مَرۡجِعَهُمۡ لَإِلَى ٱلۡجَحِيمِ ٦٨Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take إِنَّهُمۡ أَلۡفَوۡاْ ءَابَآءَهُمۡ ضَآلِّينَ ٦٩Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu فَهُمۡ عَلَىٰٓ ءَاثَٰرِهِمۡ يُهۡرَعُونَ ٧٠Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa وَلَقَدۡ ضَلَّ قَبۡلَهُمۡ أَكۡثَرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ٧١Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu وَلَقَدۡ أَرۡسَلۡنَا فِيهِم مُّنذِرِينَ ٧٢Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu فَٱنظُرۡ كَيۡفَ كَانَ عَٰقِبَةُ ٱلۡمُنذَرِينَ ٧٣Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ٧٤Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake وَلَقَدۡ نَادَىٰنَا نُوحٌ فَلَنِعۡمَ ٱلۡمُجِيبُونَ ٧٥Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu وَنَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥ مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ ٧٦Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba وَجَعَلۡنَا ذُرِّيَّتَهُۥ هُمُ ٱلۡبَاقِينَ ٧٧Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ٧٨Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe سَلَٰمٌ عَلَىٰ نُوحٍ فِي ٱلۡعَٰلَمِينَ ٧٩Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ٨٠Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ٨١Lalle shi, yanã daga bãyinMu mũminai ثُمَّ أَغۡرَقۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ٨٢Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu ۞ وَإِنَّ مِن شِيعَتِهِۦ لَإِبۡرَٰهِيمَ ٨٣Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake إِذۡ جَآءَ رَبَّهُۥ بِقَلۡبٍ سَلِيمٍ ٨٤A lõkacin da ya je wa dangijinsa da zũciya kuɓutacciya إِذۡ قَالَ لِأَبِيهِ وَقَوۡمِهِۦ مَاذَا تَعۡبُدُونَ ٨٥A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa أَئِفۡكًا ءَالِهَةً دُونَ ٱللَّهِ تُرِيدُونَ ٨٦Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa فَمَا ظَنُّكُم بِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٨٧To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu فَنَظَرَ نَظۡرَةً فِي ٱلنُّجُومِ ٨٨Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri فَقَالَ إِنِّي سَقِيمٌ ٨٩Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne فَتَوَلَّوۡاْ عَنۡهُ مُدۡبِرِينَ ٩٠Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya فَرَاغَ إِلَىٰٓ ءَالِهَتِهِمۡ فَقَالَ أَلَا تَأۡكُلُونَ ٩١Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba مَا لَكُمۡ لَا تَنطِقُونَ ٩٢Me ya sãme ku, bã ku magana فَرَاغَ عَلَيۡهِمۡ ضَرۡبَۢا بِٱلۡيَمِينِ ٩٣Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma فَأَقۡبَلُوٓاْ إِلَيۡهِ يَزِفُّونَ ٩٤Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa قَالَ أَتَعۡبُدُونَ مَا تَنۡحِتُونَ ٩٥Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa وَٱللَّهُ خَلَقَكُمۡ وَمَا تَعۡمَلُونَ ٩٦Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa قَالُواْ ٱبۡنُواْ لَهُۥ بُنۡيَٰنًا فَأَلۡقُوهُ فِي ٱلۡجَحِيمِ ٩٧Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm فَأَرَادُواْ بِهِۦ كَيۡدًا فَجَعَلۡنَٰهُمُ ٱلۡأَسۡفَلِينَ ٩٨Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci وَقَالَ إِنِّي ذَاهِبٌ إِلَىٰ رَبِّي سَيَهۡدِينِ ٩٩Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni رَبِّ هَبۡ لِي مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ ١٠٠Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne فَبَشَّرۡنَٰهُ بِغُلَٰمٍ حَلِيمٍ ١٠١Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro mai haƙuri فَلَمَّا بَلَغَ مَعَهُ ٱلسَّعۡيَ قَالَ يَٰبُنَيَّ إِنِّيٓ أَرَىٰ فِي ٱلۡمَنَامِ أَنِّيٓ أَذۡبَحُكَ فَٱنظُرۡ مَاذَا تَرَىٰۚ قَالَ يَٰٓأَبَتِ ٱفۡعَلۡ مَا تُؤۡمَرُۖ سَتَجِدُنِيٓ إِن شَآءَ ٱللَّهُ مِنَ ٱلصَّٰبِرِينَ ١٠٢To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri فَلَمَّآ أَسۡلَمَا وَتَلَّهُۥ لِلۡجَبِينِ ١٠٣To, a lõkacin da suka yi sallama, (Ibrahĩm) ya kãyar da shi ga gẽfen gõshinsa وَنَٰدَيۡنَٰهُ أَن يَٰٓإِبۡرَٰهِيمُ ١٠٤Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm قَدۡ صَدَّقۡتَ ٱلرُّءۡيَآۚ إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ١٠٥Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ ٱلۡبَلَٰٓؤُاْ ٱلۡمُبِينُ ١٠٦Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna وَفَدَيۡنَٰهُ بِذِبۡحٍ عَظِيمٍ ١٠٧Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ١٠٨Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِبۡرَٰهِيمَ ١٠٩Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ١١٠Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١١١Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai وَبَشَّرۡنَٰهُ بِإِسۡحَٰقَ نَبِيًّا مِّنَ ٱلصَّٰلِحِينَ ١١٢Kuma Muka yi masa bushãra Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne وَبَٰرَكۡنَا عَلَيۡهِ وَعَلَىٰٓ إِسۡحَٰقَۚ وَمِن ذُرِّيَّتِهِمَا مُحۡسِنٌ وَظَالِمٌ لِّنَفۡسِهِۦ مُبِينٌ ١١٣Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin) وَلَقَدۡ مَنَنَّا عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ١١٤Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna وَنَجَّيۡنَٰهُمَا وَقَوۡمَهُمَا مِنَ ٱلۡكَرۡبِ ٱلۡعَظِيمِ ١١٥Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma وَنَصَرۡنَٰهُمۡ فَكَانُواْ هُمُ ٱلۡغَٰلِبِينَ ١١٦Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya وَءَاتَيۡنَٰهُمَا ٱلۡكِتَٰبَ ٱلۡمُسۡتَبِينَ ١١٧Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni وَهَدَيۡنَٰهُمَا ٱلصِّرَٰطَ ٱلۡمُسۡتَقِيمَ ١١٨Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِمَا فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ١١٩Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe سَلَٰمٌ عَلَىٰ مُوسَىٰ وَهَٰرُونَ ١٢٠Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ١٢١Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa إِنَّهُمَا مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١٢٢Lalle, sunã daga bãyinMu mũminai وَإِنَّ إِلۡيَاسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٢٣Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni إِذۡ قَالَ لِقَوۡمِهِۦٓ أَلَا تَتَّقُونَ ١٢٤A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba أَتَدۡعُونَ بَعۡلًا وَتَذَرُونَ أَحۡسَنَ ٱلۡخَٰلِقِينَ ١٢٥Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta ٱللَّهَ رَبَّكُمۡ وَرَبَّ ءَابَآئِكُمُ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٢٦Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko فَكَذَّبُوهُ فَإِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ ١٢٧Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã) إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ١٢٨Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake وَتَرَكۡنَا عَلَيۡهِ فِي ٱلۡأٓخِرِينَ ١٢٩Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe سَلَٰمٌ عَلَىٰٓ إِلۡ يَاسِينَ ١٣٠Aminci ya tabbata ga Ilyãs إِنَّا كَذَٰلِكَ نَجۡزِي ٱلۡمُحۡسِنِينَ ١٣١Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa إِنَّهُۥ مِنۡ عِبَادِنَا ٱلۡمُؤۡمِنِينَ ١٣٢Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai وَإِنَّ لُوطًا لَّمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٣٣Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni إِذۡ نَجَّيۡنَٰهُ وَأَهۡلَهُۥٓ أَجۡمَعِينَ ١٣٤A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya إِلَّا عَجُوزًا فِي ٱلۡغَٰبِرِينَ ١٣٥Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba) ثُمَّ دَمَّرۡنَا ٱلۡأٓخَرِينَ ١٣٦Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen وَإِنَّكُمۡ لَتَمُرُّونَ عَلَيۡهِم مُّصۡبِحِينَ ١٣٧Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci وَبِٱلَّيۡلِۚ أَفَلَا تَعۡقِلُونَ ١٣٨Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba وَإِنَّ يُونُسَ لَمِنَ ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٣٩Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni إِذۡ أَبَقَ إِلَى ٱلۡفُلۡكِ ٱلۡمَشۡحُونِ ١٤٠A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi فَسَاهَمَ فَكَانَ مِنَ ٱلۡمُدۡحَضِينَ ١٤١Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya فَٱلۡتَقَمَهُ ٱلۡحُوتُ وَهُوَ مُلِيمٌ ١٤٢Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi فَلَوۡلَآ أَنَّهُۥ كَانَ مِنَ ٱلۡمُسَبِّحِينَ ١٤٣To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba لَلَبِثَ فِي بَطۡنِهِۦٓ إِلَىٰ يَوۡمِ يُبۡعَثُونَ ١٤٤Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su ۞ فَنَبَذۡنَٰهُ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ سَقِيمٌ ١٤٥Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya وَأَنۢبَتۡنَا عَلَيۡهِ شَجَرَةً مِّن يَقۡطِينٍ ١٤٦Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi وَأَرۡسَلۡنَٰهُ إِلَىٰ مِاْئَةِ أَلۡفٍ أَوۡ يَزِيدُونَ ١٤٧Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka) فَـَٔامَنُواْ فَمَتَّعۡنَٰهُمۡ إِلَىٰ حِينٍ ١٤٨Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci فَٱسۡتَفۡتِهِمۡ أَلِرَبِّكَ ٱلۡبَنَاتُ وَلَهُمُ ٱلۡبَنُونَ ١٤٩Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza أَمۡ خَلَقۡنَا ٱلۡمَلَٰٓئِكَةَ إِنَٰثًا وَهُمۡ شَٰهِدُونَ ١٥٠Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce أَلَآ إِنَّهُم مِّنۡ إِفۡكِهِمۡ لَيَقُولُونَ ١٥١To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa وَلَدَ ٱللَّهُ وَإِنَّهُمۡ لَكَٰذِبُونَ ١٥٢Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne أَصۡطَفَى ٱلۡبَنَاتِ عَلَى ٱلۡبَنِينَ ١٥٣Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ ١٥٤Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci) أَفَلَا تَذَكَّرُونَ ١٥٥Shin, bã ku tunãni أَمۡ لَكُمۡ سُلۡطَٰنٌ مُّبِينٌ ١٥٦Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne فَأۡتُواْ بِكِتَٰبِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ١٥٧To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya وَجَعَلُواْ بَيۡنَهُۥ وَبَيۡنَ ٱلۡجِنَّةِ نَسَبًاۚ وَلَقَدۡ عَلِمَتِ ٱلۡجِنَّةُ إِنَّهُمۡ لَمُحۡضَرُونَ ١٥٨Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã) سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ ١٥٩Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa إِلَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ١٦٠Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake فَإِنَّكُمۡ وَمَا تَعۡبُدُونَ ١٦١To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa مَآ أَنتُمۡ عَلَيۡهِ بِفَٰتِنِينَ ١٦٢Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi إِلَّا مَنۡ هُوَ صَالِ ٱلۡجَحِيمِ ١٦٣Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm وَمَا مِنَّآ إِلَّا لَهُۥ مَقَامٌ مَّعۡلُومٌ ١٦٤Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلصَّآفُّونَ ١٦٥Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda) وَإِنَّا لَنَحۡنُ ٱلۡمُسَبِّحُونَ ١٦٦Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi وَإِن كَانُواْ لَيَقُولُونَ ١٦٧Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa لَوۡ أَنَّ عِندَنَا ذِكۡرًا مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٦٨Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko لَكُنَّا عِبَادَ ٱللَّهِ ٱلۡمُخۡلَصِينَ ١٦٩Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake فَكَفَرُواْ بِهِۦۖ فَسَوۡفَ يَعۡلَمُونَ ١٧٠Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani وَلَقَدۡ سَبَقَتۡ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٧١Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni إِنَّهُمۡ لَهُمُ ٱلۡمَنصُورُونَ ١٧٢Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ ٱلۡغَٰلِبُونَ ١٧٣Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya فَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٍ ١٧٤Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci وَأَبۡصِرۡهُمۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ ١٧٥Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani أَفَبِعَذَابِنَا يَسۡتَعۡجِلُونَ ١٧٦Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمۡ فَسَآءَ صَبَاحُ ٱلۡمُنذَرِينَ ١٧٧To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana وَتَوَلَّ عَنۡهُمۡ حَتَّىٰ حِينٍ ١٧٨Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci وَأَبۡصِرۡ فَسَوۡفَ يُبۡصِرُونَ ١٧٩Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa سُبۡحَٰنَ رَبِّكَ رَبِّ ٱلۡعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ ١٨٠Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa وَسَلَٰمٌ عَلَى ٱلۡمُرۡسَلِينَ ١٨١Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni وَٱلۡحَمۡدُ لِلَّهِ رَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ١٨٢Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu