Millat al-Islam

Chapter 87 · 19 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Ala in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Ala (1421 reciters)
Meccanسورة الأعلى19 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

سَبِّحِ ٱسۡمَ رَبِّكَ ٱلۡأَعۡلَى ١Ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mafi ɗaukaka ٱلَّذِي خَلَقَ فَسَوَّىٰ ٢Wanda Yã yi halitta sa'an nan Ya daidaita abin halittar وَٱلَّذِي قَدَّرَ فَهَدَىٰ ٣Kuma Wanda Ya ƙaddara (abin da Ya so) sannan Ya shiryar, (da mutum ga hanyar alhẽri da ta sharri) وَٱلَّذِيٓ أَخۡرَجَ ٱلۡمَرۡعَىٰ ٤Kuma Wanda Ya fitar da makiyãyã فَجَعَلَهُۥ غُثَآءً أَحۡوَىٰ ٥Sa'an nan Ya mayar da ita ƙeƙasassa, baƙa سَنُقۡرِئُكَ فَلَا تَنسَىٰٓ ٦Za mu karantar da kai (Alƙur'ãni) sabõda haka bã zã ka mantã (shi) ba إِلَّا مَا شَآءَ ٱللَّهُۚ إِنَّهُۥ يَعۡلَمُ ٱلۡجَهۡرَ وَمَا يَخۡفَىٰ ٧Fãce abin da Allah Ya so, lalle ne Shi (Allah) Ya san bayyane da abin da yake bõye وَنُيَسِّرُكَ لِلۡيُسۡرَىٰ ٨Kuma za Mu sauƙaƙe maka (al'amari) zuwa ga (Shari'a) mai sauƙi فَذَكِّرۡ إِن نَّفَعَتِ ٱلذِّكۡرَىٰ ٩Sabõda baka, ka tunãtar, idan tunatarwa zã ta yi amfãni سَيَذَّكَّرُ مَن يَخۡشَىٰ ١٠Wanda yake tsõron (Allah) Zai tuna وَيَتَجَنَّبُهَا ٱلۡأَشۡقَى ١١Kuma shaƙiyyi, zai nisanceta ٱلَّذِي يَصۡلَى ٱلنَّارَ ٱلۡكُبۡرَىٰ ١٢Wanda zai shiga wutar da tã fi girma ثُمَّ لَا يَمُوتُ فِيهَا وَلَا يَحۡيَىٰ ١٣Sa'an nan bã zai mutu ba a cikinta, kuma bã zai rãyu ba قَدۡ أَفۡلَحَ مَن تَزَكَّىٰ ١٤Lalle ne wanda ya tsarkaka (da ĩmãni) yã sãmu babban rabo وَذَكَرَ ٱسۡمَ رَبِّهِۦ فَصَلَّىٰ ١٥Kuma ya ambaci sũnan* Ubangijinsa, sa'an nan yã yi salla بَلۡ تُؤۡثِرُونَ ٱلۡحَيَوٰةَ ٱلدُّنۡيَا ١٦Ba haka ba! Kunã zãɓin rãyuwa ta kusa dũniya وَٱلۡأٓخِرَةُ خَيۡرٌ وَأَبۡقَىٰٓ ١٧Alhãli Lãhira ita ce mafi alheri kuma mafi wanzuwa إِنَّ هَٰذَا لَفِي ٱلصُّحُفِ ٱلۡأُولَىٰ ١٨Lalle ne, wannan* yanã a cikin littafan farko صُحُفِ إِبۡرَٰهِيمَ وَمُوسَىٰ ١٩Littaffan Ibrãhĩm da Mũsã

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.