Millat al-Islam

Chapter 86 · 17 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah At-Tariq in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah At-Tariq (1312 reciters)
Meccanسورة الطارق17 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلسَّمَآءِ وَٱلطَّارِقِ ١Inã rantsuwa da sama da mai aukõwa da dare وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلطَّارِقُ ٢To, mẽ yã sanar da kai abin da ake cẽwa mai aukõwa da dare ٱلنَّجۡمُ ٱلثَّاقِبُ ٣Shi ne taurãron nan mai tsananin haske إِن كُلُّ نَفۡسٍ لَّمَّا عَلَيۡهَا حَافِظٌ ٤Bãbu wani rai fãce a kansa akwai wani mai tsaro فَلۡيَنظُرِ ٱلۡإِنسَٰنُ مِمَّ خُلِقَ ٥To, mutum ya dũba, daga mẽ aka halittã shi خُلِقَ مِن مَّآءٍ دَافِقٍ ٦An halittã shi daga wani ruwa mai tunkuɗar jũna يَخۡرُجُ مِنۢ بَيۡنِ ٱلصُّلۡبِ وَٱلتَّرَآئِبِ ٧Yanã fita daga tsakanin tsatso da karankarman ƙirji إِنَّهُۥ عَلَىٰ رَجۡعِهِۦ لَقَادِرٌ ٨Lalle ne Shi (Allah), ga mayar da shi (mutum), tabbas Mai iyãwa ne يَوۡمَ تُبۡلَى ٱلسَّرَآئِرُ ٩Rãnar da ake jarrabawar asirai فَمَا لَهُۥ مِن قُوَّةٍ وَلَا نَاصِرٍ ١٠Saboda haka, bã shi da wani ƙarfi, kuma bã shi da wani mai taimako (da zai iya kãre shi daga azãbar Allah) وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلرَّجۡعِ ١١Ina rantsuwa da sama ma'abũciyar ruwa mai kõmãwa yana yankẽwa وَٱلۡأَرۡضِ ذَاتِ ٱلصَّدۡعِ ١٢Da ƙasa ma'abociyar tsãgẽwa إِنَّهُۥ لَقَوۡلٌ فَصۡلٌ ١٣Lalle ne shĩ (Alƙur'ãni), haƙĩƙa magana ce daki-daki وَمَا هُوَ بِٱلۡهَزۡلِ ١٤Kuma shĩ bã bananci* bane إِنَّهُمۡ يَكِيدُونَ كَيۡدًا ١٥Lalle ne sũ, suna ƙulla kaidi na sõsai وَأَكِيدُ كَيۡدًا ١٦Kuma Ni, Ina mayar da kaidi (gare su) kamar yadda suke ƙulla kaidi فَمَهِّلِ ٱلۡكَٰفِرِينَ أَمۡهِلۡهُمۡ رُوَيۡدَۢا ١٧Saboda haka, ka yi wa kafirai jinkiri, ka dakata musu, sannu-sannu

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.