Millat al-Islam

Chapter 70 · 44 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Maarij in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Maarij (1275 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

سَأَلَ سَآئِلُۢ بِعَذَابٍ وَاقِعٍ ١Wani mai tambaya yã yi tambaya game da azãba, mai aukuwa لِّلۡكَٰفِرِينَ لَيۡسَ لَهُۥ دَافِعٌ ٢Ga kãfirai, bã ta da mai tunkuɗẽwa مِّنَ ٱللَّهِ ذِي ٱلۡمَعَارِجِ ٣Daga Allah Mai matãkala تَعۡرُجُ ٱلۡمَلَٰٓئِكَةُ وَٱلرُّوحُ إِلَيۡهِ فِي يَوۡمٍ كَانَ مِقۡدَارُهُۥ خَمۡسِينَ أَلۡفَ سَنَةٍ ٤Malã'iku da Ruhi (Jibrila) sunã tãkãwa zuwa gare Shi, a cikin yini wanda gwargwadonsa, shẽkara dubu hamsin ne فَٱصۡبِرۡ صَبۡرًا جَمِيلًا ٥Sabõda haka, ka yi haƙuri, haƙuri mai kyãwo إِنَّهُمۡ يَرَوۡنَهُۥ بَعِيدًا ٦Lalle ne su, sunã ganin ta mai nĩsa وَنَرَىٰهُ قَرِيبًا ٧Kuma Mu, Muna ganin ta a kusa يَوۡمَ تَكُونُ ٱلسَّمَآءُ كَٱلۡمُهۡلِ ٨Rãnar da sama zã ta kasance kamar narkakkar azurfa وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٩Kuma duwãtsu su zama kamar saɓin sũfi وَلَا يَسۡـَٔلُ حَمِيمٌ حَمِيمًا ١٠Kuma abõki bã ya tambayar inda wani abõki yake يُبَصَّرُونَهُمۡۚ يَوَدُّ ٱلۡمُجۡرِمُ لَوۡ يَفۡتَدِي مِنۡ عَذَابِ يَوۡمِئِذِۭ بِبَنِيهِ ١١Ana sanya su, su gajũna, mai laifi na gũrin dã zai iya yin fansa, daga azãbar rãnar nan, da ɗiyansa وَصَٰحِبَتِهِۦ وَأَخِيهِ ١٢Da matarsa da ɗan'uwansa وَفَصِيلَتِهِ ٱلَّتِي تُـٔۡوِيهِ ١٣Da danginsa, mãsu tattarã shi وَمَن فِي ٱلۡأَرۡضِ جَمِيعًا ثُمَّ يُنجِيهِ ١٤Da wanda ke a cikin dũniya duka gabã ɗaya, sa'an nan fansar, ta tsĩrar da shi كـَلَّآۖ إِنَّهَا لَظَىٰ ١٥A'aha! Lalle ne fa, ita ce Lazã نَزَّاعَةً لِّلشَّوَىٰ ١٦Mai twãle fãtar goshi تَدۡعُواْ مَنۡ أَدۡبَرَ وَتَوَلَّىٰ ١٧Tanã kiran wanda ya jũya bãya (daga addini) kuma ya kau da kai وَجَمَعَ فَأَوۡعَىٰٓ ١٨Ya tãra (dũkiya), kuma ya sanya ta a cikin jaka ۞ إِنَّ ٱلۡإِنسَٰنَ خُلِقَ هَلُوعًا ١٩Lalle ne mutum an halitta shi mai ciwon kwaɗayi إِذَا مَسَّهُ ٱلشَّرُّ جَزُوعًا ٢٠Idan sharri ya shãfe shi, ya kãsa haƙuri وَإِذَا مَسَّهُ ٱلۡخَيۡرُ مَنُوعًا ٢١Kuma idan alhẽri ya shãfe shi, ya yi rõwa إِلَّا ٱلۡمُصَلِّينَ ٢٢Sai mãsu yin salla ٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ دَآئِمُونَ ٢٣Waɗanda suke, a kan sallarsu, su, mãsu dawwama ne وَٱلَّذِينَ فِيٓ أَمۡوَٰلِهِمۡ حَقٌّ مَّعۡلُومٌ ٢٤Kuma waɗanda a cikin dũkiyarsu, akwai wani haƙƙi sananne لِّلسَّآئِلِ وَٱلۡمَحۡرُومِ ٢٥Ga (matalauci) mai rõƙo da wanda aka hanã wa roƙon وَٱلَّذِينَ يُصَدِّقُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ٢٦Da waɗannan da ke gaskata rãnar sakamako وَٱلَّذِينَ هُم مِّنۡ عَذَابِ رَبِّهِم مُّشۡفِقُونَ ٢٧Da waɗannan sabõda azãbar Ubangijinsu, suna jin tsõro إِنَّ عَذَابَ رَبِّهِمۡ غَيۡرُ مَأۡمُونٍ ٢٨Lalle ne, azãbar Ubangijinsu bã wadda ake iya amincẽwaba ce وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِفُرُوجِهِمۡ حَٰفِظُونَ ٢٩Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne إِلَّا عَلَىٰٓ أَزۡوَٰجِهِمۡ أَوۡ مَا مَلَكَتۡ أَيۡمَٰنُهُمۡ فَإِنَّهُمۡ غَيۡرُ مَلُومِينَ ٣٠Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka. To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne فَمَنِ ٱبۡتَغَىٰ وَرَآءَ ذَٰلِكَ فَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡعَادُونَ ٣١To, duk wanda ya nẽmi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka وَٱلَّذِينَ هُمۡ لِأَمَٰنَٰتِهِمۡ وَعَهۡدِهِمۡ رَٰعُونَ ٣٢Kuma da waɗannan da suke ga amãnõninsu da alkawarinsu mãsu tsarẽwa ne وَٱلَّذِينَ هُم بِشَهَٰدَٰتِهِمۡ قَآئِمُونَ ٣٣Kuma da waɗanda suke, ga shaidarsu, mãsu dãgẽwa ne وَٱلَّذِينَ هُمۡ عَلَىٰ صَلَاتِهِمۡ يُحَافِظُونَ ٣٤Kuma waɗanda suke, a kan sallarsu, mãsu tsarẽwa ne أُوْلَٰٓئِكَ فِي جَنَّٰتٍ مُّكۡرَمُونَ ٣٥Waɗannan, a cikin gidãjen Aljanna, waɗanda ake girmamãwa ne فَمَالِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ قِبَلَكَ مُهۡطِعِينَ ٣٦Mẽ yã sãmi waɗanda suka kãfirta, a wajenka, sunã gaugãwar (gudu) عَنِ ٱلۡيَمِينِ وَعَنِ ٱلشِّمَالِ عِزِينَ ٣٧Daga jihar dãma, kuma daga jihar hagu, jama'a-jama'a أَيَطۡمَعُ كُلُّ ٱمۡرِيٍٕ مِّنۡهُمۡ أَن يُدۡخَلَ جَنَّةَ نَعِيمٍ ٣٨Shin kõwane mutum daga cikinsu yana nẽman a shigar da shi a Aljannar ni'ima ne (ba da wani aiki ba) كـَلَّآۖ إِنَّا خَلَقۡنَٰهُم مِّمَّا يَعۡلَمُونَ ٣٩A'aha! Lalle Mũ, Mun halitta su, daga abin da suka sani فَلَآ أُقۡسِمُ بِرَبِّ ٱلۡمَشَٰرِقِ وَٱلۡمَغَٰرِبِ إِنَّا لَقَٰدِرُونَ ٤٠Sabõda haka ba sai Na yi rantsuwa da Ubangijin wurãren ɓullõwar rãna da wurãren fãɗuwarta ba, lalle Mũ, Mãsu iyãwa ne عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ خَيۡرًا مِّنۡهُمۡ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ ٤١Ga Mu musanya waɗanda suke mafi alhẽri, daga gare su. Kuma ba Mu kasance waɗanda ake rinjãya ba فَذَرۡهُمۡ يَخُوضُواْ وَيَلۡعَبُواْ حَتَّىٰ يُلَٰقُواْ يَوۡمَهُمُ ٱلَّذِي يُوعَدُونَ ٤٢Sabõda haka ka bar su, su dulmuya, kuma su yi wãsã, har su haɗu da rãnarsu wadda ake yi musu alkawari (da ita) يَوۡمَ يَخۡرُجُونَ مِنَ ٱلۡأَجۡدَاثِ سِرَاعًا كَأَنَّهُمۡ إِلَىٰ نُصُبٍ يُوفِضُونَ ٤٣Rãnar da suke fitowa daga kaburbura da gaugãwa, kamar sũ, zuwa ga wata kafaffiyar (tuta), suke yin gaugãwa خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٌۚ ذَٰلِكَ ٱلۡيَوۡمُ ٱلَّذِي كَانُواْ يُوعَدُونَ ٤٤Maƙaskanta ga idanunsu, wani walakanci yana rufe su. wannan shi ne yinin da suka kasance ana yi musa alkawari (a kansa)

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.