بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلۡحَآقَّةُ ١Kiran gaskiya مَا ٱلۡحَآقَّةُ ٢Mẽne ne kiran gaskiya وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحَآقَّةُ ٣Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽwa kiran gaskiya كَذَّبَتۡ ثَمُودُ وَعَادُۢ بِٱلۡقَارِعَةِ ٤Samũdãwa da Ãdãwa sun ƙaryatar da kiran gaskiya mai dũkar zũciya فَأَمَّا ثَمُودُ فَأُهۡلِكُواْ بِٱلطَّاغِيَةِ ٥To, amma Samũdãwa to, an halakãsu da tsãwa mai tsanani وَأَمَّا عَادٌ فَأُهۡلِكُواْ بِرِيحٍ صَرۡصَرٍ عَاتِيَةٍ ٦Kuma amma Ãdãwa to, an halaka su da wata iska mai tsananin sauti wadda ta ƙẽtare haddi سَخَّرَهَا عَلَيۡهِمۡ سَبۡعَ لَيَالٍ وَثَمَٰنِيَةَ أَيَّامٍ حُسُومًاۖ فَتَرَى ٱلۡقَوۡمَ فِيهَا صَرۡعَىٰ كَأَنَّهُمۡ أَعۡجَازُ نَخۡلٍ خَاوِيَةٍ ٧(Allah) Ya hõre ta a kansu a cikin dare bakwai da yini takwas, biye da jũna, sabõda haka, kana ganin mutãne a cikinta kwance. Kamar sũ ƙirãruwan dabĩno ne, waɗanda suka fãɗi فَهَلۡ تَرَىٰ لَهُم مِّنۢ بَاقِيَةٍ ٨To, kõ kanã ganin abin da ya yi saurã daga cikinsu وَجَآءَ فِرۡعَوۡنُ وَمَن قَبۡلَهُۥ وَٱلۡمُؤۡتَفِكَٰتُ بِٱلۡخَاطِئَةِ ٩Kuma Fir'auna yã zo da waɗanda ke gabãninsa, da waɗannan da aka kife ƙasarsu, sabõda laifi فَعَصَوۡاْ رَسُولَ رَبِّهِمۡ فَأَخَذَهُمۡ أَخۡذَةً رَّابِيَةً ١٠Dõmin sun sãɓã wa manzon Ubangijinsu, sabõda haka ya kãmã su da wani irin kãmu mai ƙãruwar (tsanani) إِنَّا لَمَّا طَغَا ٱلۡمَآءُ حَمَلۡنَٰكُمۡ فِي ٱلۡجَارِيَةِ ١١Lalle ne, Mũ, a lõkacin da ruwa ya ƙẽtare haddi, Munɗauke aaku a cikin jirgin ruwan nan لِنَجۡعَلَهَا لَكُمۡ تَذۡكِرَةً وَتَعِيَهَآ أُذُنٌ وَٰعِيَةٌ ١٢Dõmin Mu sanya shi, gare ku abin tunãwa kuma wani kunne mai kiyayewa ya kiyaye (shi) فَإِذَا نُفِخَ فِي ٱلصُّورِ نَفۡخَةٌ وَٰحِدَةٌ ١٣To, idan an yi bũsa a cikin ƙaho, bũsa ɗaya وَحُمِلَتِ ٱلۡأَرۡضُ وَٱلۡجِبَالُ فَدُكَّتَا دَكَّةً وَٰحِدَةً ١٤Kuma aka ɗauki ƙasa da duwãtsu, kuma aka niƙa su niƙãwa ɗaya فَيَوۡمَئِذٍ وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ ١٥A ran nan, mai aukuwa zã ta auku وَٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَهِيَ يَوۡمَئِذٍ وَاهِيَةٌ ١٦Kuma sama zã ta tsãge, dõmin ita a ran nan, mai rauni ce وَٱلۡمَلَكُ عَلَىٰٓ أَرۡجَآئِهَاۚ وَيَحۡمِلُ عَرۡشَ رَبِّكَ فَوۡقَهُمۡ يَوۡمَئِذٍ ثَمَٰنِيَةٌ ١٧Kuma malã'iku (su bayyana) a kan sãsanninta, kuma wasu (malã'iku) takwas na ɗauke da Al'arshin Ubangijinka, a sama da su, a wannan rãnar يَوۡمَئِذٍ تُعۡرَضُونَ لَا تَخۡفَىٰ مِنكُمۡ خَافِيَةٌ ١٨A rãnar nan zã a bijirã ku (dõmin hisãbi), bãbu wani rai, mai ɓoyewa, daga cikinku, wanda zai iya ɓõyẽwa فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ فَيَقُولُ هَآؤُمُ ٱقۡرَءُواْ كِتَٰبِيَهۡ ١٩To, amma wanda aka bai wa littãfinsa a dãmansa, sai ya ce wa (makusantansa), "Ku karɓa, ku karanta littafina إِنِّي ظَنَنتُ أَنِّي مُلَٰقٍ حِسَابِيَهۡ ٢٠Lalle ne ni, nã tabbata cewa ni mai haɗuwa da hisãbina ne فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ ٢١Sabõda haka, shi yana cikin wata rãyuwa yardadda فِي جَنَّةٍ عَالِيَةٍ ٢٢A cikin Aljanna maɗaukakiya قُطُوفُهَا دَانِيَةٌ ٢٣Nunannun 'yã'yan itãcenta makusantã ne (ga mai son ɗĩba) كُلُواْ وَٱشۡرَبُواْ هَنِيٓـَٔۢا بِمَآ أَسۡلَفۡتُمۡ فِي ٱلۡأَيَّامِ ٱلۡخَالِيَةِ ٢٤(Ana ce musu) "Ku ci, kuma ku sha a cikin ni'ima, sabõda abin da kuka gabãtar a cikin kwãnukan da suka shige وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِشِمَالِهِۦ فَيَقُولُ يَٰلَيۡتَنِي لَمۡ أُوتَ كِتَٰبِيَهۡ ٢٥Kuma wanda aka bai wa littãfinsa ga hagunsa, sai ya ce: "Kaitona, ba a kãwo mini littãfina ba وَلَمۡ أَدۡرِ مَا حِسَابِيَهۡ ٢٦Kuma ban san abin da (ke sakamakon) hisãbina ba يَٰلَيۡتَهَا كَانَتِ ٱلۡقَاضِيَةَ ٢٧In dã dai ita, tã kasance mai halakã ni gabã ɗaya ce مَآ أَغۡنَىٰ عَنِّي مَالِيَهۡۜ ٢٨Dukiyãta ba ta wadatar da ni ba هَلَكَ عَنِّي سُلۡطَٰنِيَهۡ ٢٩Ĩkona ya ɓace mini خُذُوهُ فَغُلُّوهُ ٣٠(Sai a ce wa malã'iku) "Ku kãmã shi, sa'an nan ku sanyã shi a cikin ƙuƙumi ثُمَّ ٱلۡجَحِيمَ صَلُّوهُ ٣١Sa'an nan, a cikin Jahĩm, ku ƙõna shi ثُمَّ فِي سِلۡسِلَةٍ ذَرۡعُهَا سَبۡعُونَ ذِرَاعًا فَٱسۡلُكُوهُ ٣٢Sa'an nan, acikin sarƙa, tsawonta zirã'i saba'in, sai ku sanya shi إِنَّهُۥ كَانَ لَا يُؤۡمِنُ بِٱللَّهِ ٱلۡعَظِيمِ ٣٣Lalle ne, shi ya kasance ba ya yin ĩmãni da Allah, Mai girma وَلَا يَحُضُّ عَلَىٰ طَعَامِ ٱلۡمِسۡكِينِ ٣٤Kuma ba ya kwaɗaitarwa ga (bãyar da) abincin matalauci فَلَيۡسَ لَهُ ٱلۡيَوۡمَ هَٰهُنَا حَمِيمٌ ٣٥Sabõda haka, a yau, a nan, bã ya da masõyi وَلَا طَعَامٌ إِلَّا مِنۡ غِسۡلِينٍ ٣٦Kuma bãbu wani abinci, sai daga (itãcen) gislĩn لَّا يَأۡكُلُهُۥٓ إِلَّا ٱلۡخَٰطِـُٔونَ ٣٧Bãbu mai cin sa sai mãsu ganganci فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَا تُبۡصِرُونَ ٣٨To, ba sai Nã yi rantsuwa da abin da kuke iya gani ba وَمَا لَا تُبۡصِرُونَ ٣٩Da abin da bã ku iya gani إِنَّهُۥ لَقَوۡلُ رَسُولٍ كَرِيمٍ ٤٠Lalle ne, shi (Alƙur'ani) tabbas maganar wani manzo (Jibirilu) mai daraja ne وَمَا هُوَ بِقَوۡلِ شَاعِرٍۚ قَلِيلًا مَّا تُؤۡمِنُونَ ٤١Kuma shi ba maganar wani mawãƙi ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku gaskata وَلَا بِقَوۡلِ كَاهِنٍۚ قَلِيلًا مَّا تَذَكَّرُونَ ٤٢Kuma bã maganar bõka ba ne. Kaɗan ƙwarai zã ku iya tunãwa تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٤٣Abin saukarwã ne daga Ubangijin halitta duka وَلَوۡ تَقَوَّلَ عَلَيۡنَا بَعۡضَ ٱلۡأَقَاوِيلِ ٤٤Kuma dã (Muhammadu) yã faɗi wata maganã, yã jingina ta garẽ Mu لَأَخَذۡنَا مِنۡهُ بِٱلۡيَمِينِ ٤٥Dã Mun kãma shi da dãma ثُمَّ لَقَطَعۡنَا مِنۡهُ ٱلۡوَتِينَ ٤٦sa'an nan, lalle ne, dã Mun kãtse masa lakã فَمَا مِنكُم مِّنۡ أَحَدٍ عَنۡهُ حَٰجِزِينَ ٤٧Kuma daga cikinku bãbu wasu mãsu iya kãre (azãbar Mu) daga gare shi وَإِنَّهُۥ لَتَذۡكِرَةٌ لِّلۡمُتَّقِينَ ٤٨Kuma lalle ne shi (Alƙur'ãni) tanãtarwa ce ga mãsu taƙawa وَإِنَّا لَنَعۡلَمُ أَنَّ مِنكُم مُّكَذِّبِينَ ٤٩Kuma lalle, ne Mũ, wallahi Munã sane da cẽwa daga cikinku alwwai mãsu ƙaryatãwa وَإِنَّهُۥ لَحَسۡرَةٌ عَلَى ٱلۡكَٰفِرِينَ ٥٠Kuma lalle ne shi (Alƙarãni) wallahi baƙin ciki ne ga kãfirai وَإِنَّهُۥ لَحَقُّ ٱلۡيَقِينِ ٥١Kuma lalle, ne shi gaskiya ce ta yaƙini فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ ٥٢Sabõda haka, ka tsarkake sũnan Ubangjinka, mai girma