Millat al-Islam

Chapter 83 · 36 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Mutaffifin in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Mutaffifin (1304 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَيۡلٌ لِّلۡمُطَفِّفِينَ ١Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa ٱلَّذِينَ إِذَا ٱكۡتَالُواْ عَلَى ٱلنَّاسِ يَسۡتَوۡفُونَ ٢Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu وَإِذَا كَالُوهُمۡ أَو وَّزَنُوهُمۡ يُخۡسِرُونَ ٣Kuma idan sun auna musu da zakka* ko da sikẽli, suna ragẽwa أَلَا يَظُنُّ أُوْلَٰٓئِكَ أَنَّهُم مَّبۡعُوثُونَ ٤Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba لِيَوۡمٍ عَظِيمٍ ٥Domin yini mai girma يَوۡمَ يَقُومُ ٱلنَّاسُ لِرَبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٦Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta كـَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡفُجَّارِ لَفِي سِجِّينٍ ٧Haƙĩƙa lalle ne littãfin fãjirai dãhir, yana a cikin Sijjĩn وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا سِجِّينٌ ٨Kuma, mẽ ya sanar da kai abin da akẽ cẽ wa Sijjĩn كِتَٰبٌ مَّرۡقُومٌ ٩Wani ittãfi ne rubũtacce وَيۡلٌ يَوۡمَئِذٍ لِّلۡمُكَذِّبِينَ ١٠Bone yã tabbata a rãnar nan ga mãsu ƙaryatãwa ٱلَّذِينَ يُكَذِّبُونَ بِيَوۡمِ ٱلدِّينِ ١١Waɗanda suke ƙaryatãwa game da rãnar sakamako وَمَا يُكَذِّبُ بِهِۦٓ إِلَّا كُلُّ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ ١٢Babũ mai ƙaryatãwa gare shi fãce dukan mai ƙẽtare haddi mai yawan zunubi إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٣Idan ana karãtun ãyõyinmu, a kansa, sai ya ce: tãtsũniyõyin mutãnen farko ne كـَلَّاۖ بَلۡۜ رَانَ عَلَىٰ قُلُوبِهِم مَّا كَانُواْ يَكۡسِبُونَ ١٤A'aha! Bã haka ba, abin da suka kasance suna aikatãwa dai, yã yi tsãtsa a cikin zukãtãnsu كـَلَّآ إِنَّهُمۡ عَن رَّبِّهِمۡ يَوۡمَئِذٍ لَّمَحۡجُوبُونَ ١٥A'aha! Haƙĩƙa, lalle ne sũ daga Ubangijinsu, rãnar nan, waɗanda ake shãmakancẽwa ne ثُمَّ إِنَّهُمۡ لَصَالُواْ ٱلۡجَحِيمِ ١٦Sa'an nan, lalle ne, sũ mãsu shiga cikin Jahĩm ne ثُمَّ يُقَالُ هَٰذَا ٱلَّذِي كُنتُم بِهِۦ تُكَذِّبُونَ ١٧Sa'an nan a ce: "Wannan shi ne abin da kuka kasance kuna ƙaryatãwa game da shi كـَلَّآ إِنَّ كِتَٰبَ ٱلۡأَبۡرَارِ لَفِي عِلِّيِّينَ ١٨A'aha! Haƙĩƙa lalle ne littãfin mãsu ɗã'ã yana a cikin Illiyyĩna وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا عِلِّيُّونَ ١٩Kuma mẽne ne yã sanar da kai abin da ake cẽwa Illiyyũna كِتَٰبٌ مَّرۡقُومٌ ٢٠Wani littãfi ne rubũtacce يَشۡهَدُهُ ٱلۡمُقَرَّبُونَ ٢١Muƙarrabai* suke halarta shi إِنَّ ٱلۡأَبۡرَارَ لَفِي نَعِيمٍ ٢٢Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah tabbas suna cikin ni'ima عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ٢٣A kan karagu, suna ta kallo تَعۡرِفُ فِي وُجُوهِهِمۡ نَضۡرَةَ ٱلنَّعِيمِ ٢٤Kana sani a cikin fuskõkinsu, akwai kwarjinin ni'ima يُسۡقَوۡنَ مِن رَّحِيقٍ مَّخۡتُومٍ ٢٥Ana shãyar da sũ daga wata giya wadda aka yunƙe a kan rufinta خِتَٰمُهُۥ مِسۡكٌۚ وَفِي ذَٰلِكَ فَلۡيَتَنَافَسِ ٱلۡمُتَنَٰفِسُونَ ٢٦¡arshen kurɓinta miski ne. To, a cikin wannan, mãsu gwagwarmaya su yi ta gwagwarmayar nẽma وَمِزَاجُهُۥ مِن تَسۡنِيمٍ ٢٧Kuma abin da ake gauraya ta da shi, daga tasnĩm yake عَيۡنًا يَشۡرَبُ بِهَا ٱلۡمُقَرَّبُونَ ٢٨(Wato) wani marmaro ne wanda muƙarrabai ke sha daga gare shi إِنَّ ٱلَّذِينَ أَجۡرَمُواْ كَانُواْ مِنَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ يَضۡحَكُونَ ٢٩Lalle ne, waɗanda suka kãfirta sun kasance (a dũniya) suna yi wa waɗanda suka yi ĩmãni dãriya وَإِذَا مَرُّواْ بِهِمۡ يَتَغَامَزُونَ ٣٠Kuma idan sun shuɗe su sai su dinga yin zunɗe وَإِذَا ٱنقَلَبُوٓاْ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِمُ ٱنقَلَبُواْ فَكِهِينَ ٣١Kuma idan suka jũya zuwa ga iyãlansu, sai su tafi suna kãkãci وَإِذَا رَأَوۡهُمۡ قَالُوٓاْ إِنَّ هَٰٓؤُلَآءِ لَضَآلُّونَ ٣٢Kuma idan sun gan su sai su ce: "Lalle waɗannan ɓatattu ne وَمَآ أُرۡسِلُواْ عَلَيۡهِمۡ حَٰفِظِينَ ٣٣Alhãli kuwa, ba a aike su ba dõmin su zama mãsu tsaro a kansu فَٱلۡيَوۡمَ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ مِنَ ٱلۡكُفَّارِ يَضۡحَكُونَ ٣٤To, yau fa (a Lãhira] waɗanda suka yi ĩmãni, sũ ke yi wa kãfirai dãriya عَلَى ٱلۡأَرَآئِكِ يَنظُرُونَ ٣٥A kan karagu, suna ta kallo هَلۡ ثُوِّبَ ٱلۡكُفَّارُ مَا كَانُواْ يَفۡعَلُونَ ٣٦Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.