Millat al-Islam

Chapter 84 · 25 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Inshiqaq in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Inshiqaq (1262 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا ٱلسَّمَآءُ ٱنشَقَّتۡ ١Idan sama ta kẽce وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ ٢Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron وَإِذَا ٱلۡأَرۡضُ مُدَّتۡ ٣Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta وَأَلۡقَتۡ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتۡ ٤Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme وَأَذِنَتۡ لِرَبِّهَا وَحُقَّتۡ ٥Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren يَٰٓأَيُّهَا ٱلۡإِنسَٰنُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدۡحًا فَمُلَٰقِيهِ ٦Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne فَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ بِيَمِينِهِۦ ٧To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa فَسَوۡفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا ٨To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi وَيَنقَلِبُ إِلَىٰٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورًا ٩Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha وَأَمَّا مَنۡ أُوتِيَ كِتَٰبَهُۥ وَرَآءَ ظَهۡرِهِۦ ١٠Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa فَسَوۡفَ يَدۡعُواْ ثُبُورًا ١١To, zã shi dinga kiran halaka وَيَصۡلَىٰ سَعِيرًا ١٢Kuma ya shiga sa'ĩr إِنَّهُۥ كَانَ فِيٓ أَهۡلِهِۦ مَسۡرُورًا ١٣Lale ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha إِنَّهُۥ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ ١٤Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba بَلَىٰٓۚ إِنَّ رَبَّهُۥ كَانَ بِهِۦ بَصِيرًا ١٥Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi فَلَآ أُقۡسِمُ بِٱلشَّفَقِ ١٦To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba وَٱلَّيۡلِ وَمَا وَسَقَ ١٧Da dare, da abin da ya ƙunsa وَٱلۡقَمَرِ إِذَا ٱتَّسَقَ ١٨Da watã idan (haskensa) ya cika لَتَرۡكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ ١٩Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli فَمَا لَهُمۡ لَا يُؤۡمِنُونَ ٢٠To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni وَإِذَا قُرِئَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡقُرۡءَانُ لَا يَسۡجُدُونَۤ ۩ ٢١Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ يُكَذِّبُونَ ٢٢Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi وَٱللَّهُ أَعۡلَمُ بِمَا يُوعُونَ ٢٣Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa فَبَشِّرۡهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ ٢٤Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ أَجۡرٌ غَيۡرُ مَمۡنُونِۭ ٢٥Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.