Millat al-Islam

Chapter 68 · 52 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Qalam in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Qalam (1262 reciters)
Meccanسورة القلم52 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

نٓۚ وَٱلۡقَلَمِ وَمَا يَسۡطُرُونَ ١Ñ. Na rantse da alƙalami da abin da (marubũta) suke rubũtãwa مَآ أَنتَ بِنِعۡمَةِ رَبِّكَ بِمَجۡنُونٍ ٢Kai, sabõda ni'imar Ubangijinka, bã mahaukaci kake ba وَإِنَّ لَكَ لَأَجۡرًا غَيۡرَ مَمۡنُونٍ ٣Kuma, lalle, haƙĩƙa kanã da lãdar da bã ta yankewa وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٍ ٤Kuma, lalle haƙiƙa kana a kan hãlãyen kirki, manya فَسَتُبۡصِرُ وَيُبۡصِرُونَ ٥Don haka, zã ka gani, sũ kuma zã su gani بِأَييِّكُمُ ٱلۡمَفۡتُونُ ٦Ga wanenku haukã take إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعۡلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعۡلَمُ بِٱلۡمُهۡتَدِينَ ٧Lalle Ubangijinka Shi ne Mafi sani ga wanda ya ɓace daga tafarkin Sa. Kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa فَلَا تُطِعِ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٨Saboda haka kada ka bi mãsu ƙaryatãwa وَدُّواْ لَوۡ تُدۡهِنُ فَيُدۡهِنُونَ ٩Sunã fatar ka sassauta, su kuma sũ sassauta وَلَا تُطِعۡ كُلَّ حَلَّافٍ مَّهِينٍ ١٠Kada ka bi dukkan mai yawan rantsuwa, walãkantacce هَمَّازٍ مَّشَّآءِۭ بِنَمِيمٍ ١١Mai zunɗe, mai yãwo da gulma مَّنَّاعٍ لِّلۡخَيۡرِ مُعۡتَدٍ أَثِيمٍ ١٢Mai hana alhẽri mai zãlunci, mai zunubi عُتُلِّۭ بَعۡدَ ذَٰلِكَ زَنِيمٍ ١٣Mai girman kai, bãyan haka kuma la'ĩmi (bã ya son alhẽri) أَن كَانَ ذَا مَالٍ وَبَنِينَ ١٤Sabõda yã kasance mai dũkiya da ɗiya إِذَا تُتۡلَىٰ عَلَيۡهِ ءَايَٰتُنَا قَالَ أَسَٰطِيرُ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٥Idan ana karanta masa ãyõyin Mu, sai ya ce: "Tatsũniyõyin mutãnen farko ne سَنَسِمُهُۥ عَلَى ٱلۡخُرۡطُومِ ١٦Zã Mu yi masa alãma a kan hanci إِنَّا بَلَوۡنَٰهُمۡ كَمَا بَلَوۡنَآ أَصۡحَٰبَ ٱلۡجَنَّةِ إِذۡ أَقۡسَمُواْ لَيَصۡرِمُنَّهَا مُصۡبِحِينَ ١٧Lalle Mun jarrabe su kamar yadda Muka jarrabi mãsu gonar lambu, a lokacin da suka yi rantsuwa, wai lalle zã su girbe amfãninta, suna mãsu asubanci وَلَا يَسۡتَثۡنُونَ ١٨Kuma (suka yi niyya), bã su kõ tõgẽwa فَطَافَ عَلَيۡهَا طَآئِفٌ مِّن رَّبِّكَ وَهُمۡ نَآئِمُونَ ١٩Wani mai kẽwayãwa daga Ubangijinka ya kẽwayã a kanta, (ya ƙone ta,) alhãli sunã barci فَأَصۡبَحَتۡ كَٱلصَّرِيمِ ٢٠Sai ta wãyi gari (baƙa ƙirin) kamar dare فَتَنَادَوۡاْ مُصۡبِحِينَ ٢١Sai suka kirãyi jũna, sunã mãsu yin asubanci أَنِ ٱغۡدُواْ عَلَىٰ حَرۡثِكُمۡ إِن كُنتُمۡ صَٰرِمِينَ ٢٢Cẽwa ku yi sammakõ ga amfãnin gõnarku, idan kun kasance mãsu girbewa فَٱنطَلَقُواْ وَهُمۡ يَتَخَٰفَتُونَ ٢٣Sai suka tafi sunã shãwara a ɓõye (sunã cẽwa) أَن لَّا يَدۡخُلَنَّهَا ٱلۡيَوۡمَ عَلَيۡكُم مِّسۡكِينٌ ٢٤Lalle kada wani miskĩni ya shigar muku ita a yau وَغَدَوۡاْ عَلَىٰ حَرۡدٍ قَٰدِرِينَ ٢٥Kuma suka yi sammako akan (niyyar) rõwa, matuƙar iyãwarsu فَلَمَّا رَأَوۡهَا قَالُوٓاْ إِنَّا لَضَآلُّونَ ٢٦Lõkacin da suka gan ta, sai suka ce: "Lalle, mun saki hanya (mun ɓace) بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ ٢٧Ba haka ba, mũ dai, an hana mu ne قَالَ أَوۡسَطُهُمۡ أَلَمۡ أَقُل لَّكُمۡ لَوۡلَا تُسَبِّحُونَ ٢٨Mafificinsu (hankali) ya ce: "Ban gaya muku ba, yã kamata ku tsarkake Allah قَالُواْ سُبۡحَٰنَ رَبِّنَآ إِنَّا كُنَّا ظَٰلِمِينَ ٢٩Suka ce: "Tsarki ya tabbata ga Ubangijinmu! Lalle, mu mun kasance azzãlumai فَأَقۡبَلَ بَعۡضُهُمۡ عَلَىٰ بَعۡضٍ يَتَلَٰوَمُونَ ٣٠Sai suka fuskanci jũna, sunã zargin kansu قَالُواْ يَٰوَيۡلَنَآ إِنَّا كُنَّا طَٰغِينَ ٣١Suka ce: "Kaitonmu! Lalle, mũ ne muka kasance mãsu ƙẽtare iyãka عَسَىٰ رَبُّنَآ أَن يُبۡدِلَنَا خَيۡرًا مِّنۡهَآ إِنَّآ إِلَىٰ رَبِّنَا رَٰغِبُونَ ٣٢Mai yiwuwa ne Ubangijinmu Ya musanya mana da wani abu da yã fi ta. Lalle, mũ (ba mu yanke ƙauna ba) zuwa ga Ubangijinmu, mãsu kwaɗayi ne كَذَٰلِكَ ٱلۡعَذَابُۖ وَلَعَذَابُ ٱلۡأٓخِرَةِ أَكۡبَرُۚ لَوۡ كَانُواْ يَعۡلَمُونَ ٣٣Haka dai azãbar* take, kuma lalle ne azãbar Lãhira ta fi girma, in da sun kasance zã su iya gãnẽwã إِنَّ لِلۡمُتَّقِينَ عِندَ رَبِّهِمۡ جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ ٣٤Lalle ne mãsu taƙawa nã da a wurin Ubangijinsu, gidãjen Aljanna na ni'ima أَفَنَجۡعَلُ ٱلۡمُسۡلِمِينَ كَٱلۡمُجۡرِمِينَ ٣٥Shin ko zã Mu sanya waɗanda ke bi da ɗa'a kamar mãsu laifi مَا لَكُمۡ كَيۡفَ تَحۡكُمُونَ ٣٦Me ya sãme ku, yãya kuke yin hukunci (da haka) أَمۡ لَكُمۡ كِتَٰبٌ فِيهِ تَدۡرُسُونَ ٣٧Ko kuna da wani littafi, wanda a cikinsa, kuke karantãwa إِنَّ لَكُمۡ فِيهِ لَمَا تَخَيَّرُونَ ٣٨Cẽwã kunã da, a cikinsa lalle (duk) abin da rãyukanku suka zãɓa أَمۡ لَكُمۡ أَيۡمَٰنٌ عَلَيۡنَا بَٰلِغَةٌ إِلَىٰ يَوۡمِ ٱلۡقِيَٰمَةِ إِنَّ لَكُمۡ لَمَا تَحۡكُمُونَ ٣٩Kõ kunã (riƙe) da wasu rantsuwõyin alkawari a kan Mu, har ya zuwa Rãnar ¡iyãma, cẽwa lalle ne kunã da abin da kuke hukuntã wa kanku سَلۡهُمۡ أَيُّهُم بِذَٰلِكَ زَعِيمٌ ٤٠Ka tambaye su, wãne, a cikinsu, ke lãmuncewã ga sãmun wannan (hukuncin) أَمۡ لَهُمۡ شُرَكَآءُ فَلۡيَأۡتُواْ بِشُرَكَآئِهِمۡ إِن كَانُواْ صَٰدِقِينَ ٤١Kõ sunã da abõkan tãrẽwa (ga wannan ra'ayi)? To, sai su kãwo abõkan tãrayyarsu, idan sun kasance mãsu gaskiya يَوۡمَ يُكۡشَفُ عَن سَاقٍ وَيُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ فَلَا يَسۡتَطِيعُونَ ٤٢Ranar da zã a kuranye ƙwabri, kuma a kira su zuwa ga yin sujada, sai bã zã su iyãwa ba خَٰشِعَةً أَبۡصَٰرُهُمۡ تَرۡهَقُهُمۡ ذِلَّةٌۖ وَقَدۡ كَانُواْ يُدۡعَوۡنَ إِلَى ٱلسُّجُودِ وَهُمۡ سَٰلِمُونَ ٤٣Su fito da idãnu ƙasƙantattu, wulãkanci yana rufe su. Lalle ne a dã sun kasance anã kiran su zuwa, yin sujũdar, alhãli kuwa sunã lãfiya lau, (suka ƙi yi) فَذَرۡنِي وَمَن يُكَذِّبُ بِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِۖ سَنَسۡتَدۡرِجُهُم مِّنۡ حَيۡثُ لَا يَعۡلَمُونَ ٤٤Sabõda haka ka bar Ni da mai ƙaryata wanna lãbãri (Alƙur'ãni). Zã Mu yi musu istidrãji daga inda ba su sani ba وَأُمۡلِي لَهُمۡۚ إِنَّ كَيۡدِي مَتِينٌ ٤٥Ina jinkirtã musu, lalle kaidi Na mai ƙarfi ne أَمۡ تَسۡـَٔلُهُمۡ أَجۡرًا فَهُم مِّن مَّغۡرَمٍ مُّثۡقَلُونَ ٤٦Kõ kana tambayar su wata la'ada ne, sabõda haka sũ, daga wannan tãrar, suke jin an nauyaya musu أَمۡ عِندَهُمُ ٱلۡغَيۡبُ فَهُمۡ يَكۡتُبُونَ ٤٧Ko kuma sunã da ilmin gaibu ne, wãto sunã yin rubũtun (abin da suke faɗã daga gare shi) ne فَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ وَلَا تَكُن كَصَاحِبِ ٱلۡحُوتِ إِذۡ نَادَىٰ وَهُوَ مَكۡظُومٌ ٤٨Sabõda haka, ka yi haƙuri da hukuncin Ubangijinka, kada ka zama kamar Ma'abũcin kĩfi, alõkacin da ya yi kira, alhãli yana cike da hushi لَّوۡلَآ أَن تَدَٰرَكَهُۥ نِعۡمَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ لَنُبِذَ بِٱلۡعَرَآءِ وَهُوَ مَذۡمُومٌ ٤٩Ba dõmin ni'ima daga wajen Ubangijinsa tã riske shi ba, lalle ne da an jẽfa shi a cikin wõfintacciyar ƙasa, alhãli yanã abin zargi فَٱجۡتَبَٰهُ رَبُّهُۥ فَجَعَلَهُۥ مِنَ ٱلصَّٰلِحِينَ ٥٠Sai Ubangijinsa Ya zãɓe shi, sa'an nan Ya sanya shi a cikin mutãnen kirki وَإِن يَكَادُ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ لَيُزۡلِقُونَكَ بِأَبۡصَٰرِهِمۡ لَمَّا سَمِعُواْ ٱلذِّكۡرَ وَيَقُولُونَ إِنَّهُۥ لَمَجۡنُونٌ ٥١Kuma lalle, ne waɗanda suka kãfirta sunã yin kamar su kãyar da kai sabõ da kallonsu (kallon mãmãki), a lokacin da suke jin karãtun Alƙur'ãni, kuma sunã cẽwa, "Lalle ne shi mahaukaci ne وَمَا هُوَ إِلَّا ذِكۡرٌ لِّلۡعَٰلَمِينَ ٥٢Shi (Alƙur'ãni) bai kasance ba, fãce abin tunãtarwa ne ga duka dũniya

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.