Millat al-Islam

Chapter 101 · 11 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Qaria in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Qaria (1290 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

ٱلۡقَارِعَةُ ١Mai ƙwanƙwasar (zukata da tsõro) مَا ٱلۡقَارِعَةُ ٢Mẽnẽ ne mai ƙwanƙwasa وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡقَارِعَةُ ٣Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa mai ƙwanƙwasa يَوۡمَ يَكُونُ ٱلنَّاسُ كَٱلۡفَرَاشِ ٱلۡمَبۡثُوثِ ٤Rãnar da mutãne za su kasance kamar 'ya'yan fari mãsu wãtsuwa وَتَكُونُ ٱلۡجِبَالُ كَٱلۡعِهۡنِ ٱلۡمَنفُوشِ ٥Kuma duwãtsu su kasance kamar gãshin sũfin da aka saɓe فَأَمَّا مَن ثَقُلَتۡ مَوَٰزِينُهُۥ ٦To, amma wanda ma'aunansa suka yi nauyi فَهُوَ فِي عِيشَةٍ رَّاضِيَةٍ ٧To, shi yana a cikin wata rayuwa yardadda وَأَمَّا مَنۡ خَفَّتۡ مَوَٰزِينُهُۥ ٨Kuma amma wanda ma'aunansa suka yi sauƙi (bãbu nauyi) فَأُمُّهُۥ هَاوِيَةٌ ٩To, uwarsa Hãwiya ce وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا هِيَهۡ ١٠Kuma me ya sanar da kai mece ce ita نَارٌ حَامِيَةُۢ ١١Wata wuta ce mai kuna

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.