Millat al-Islam

Chapter 56 · 96 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Waqi'a in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Waqi'a (1348 reciters)

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

إِذَا وَقَعَتِ ٱلۡوَاقِعَةُ ١Idan mai aukuwa ta auku لَيۡسَ لِوَقۡعَتِهَا كَاذِبَةٌ ٢Bãbu wani (rai) mai ƙaryatãwa ga aukuwarta خَافِضَةٌ رَّافِعَةٌ ٣(Ita) mai ƙasƙantãwa ce, mai ɗaukakãwa إِذَا رُجَّتِ ٱلۡأَرۡضُ رَجًّا ٤Idan aka girgiza ƙasã girgizwa وَبُسَّتِ ٱلۡجِبَالُ بَسًّا ٥Kuma aka niƙe duwãtsu, niƙẽwa فَكَانَتۡ هَبَآءً مُّنۢبَثًّا ٦Sai suka kasance ƙũra da ake wãtsarwa وَكُنتُمۡ أَزۡوَٰجًا ثَلَٰثَةً ٧Kuma kun kasance nau'i uku فَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَيۡمَنَةِ ٨Watau mazõwa dãma*. Mẽne ne mazõwa dãma وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡمَشۡـَٔمَةِ ٩Da mazõwa hagu. Mẽne ne mazõwa hagu وَٱلسَّٰبِقُونَ ٱلسَّٰبِقُونَ ١٠Da waɗanda suka tsẽre. Sũ wɗanda suka tsẽren nan أُوْلَٰٓئِكَ ٱلۡمُقَرَّبُونَ ١١Waɗancan, sũ ne waɗanda aka kusantar فِي جَنَّٰتِ ٱلنَّعِيمِ ١٢A ckin Aljannar ni'ima ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ١٣Jama'a ne daga mutãnen farko وَقَلِيلٌ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ ١٤Da kaɗan daga mutãnen ƙarshe عَلَىٰ سُرُرٍ مَّوۡضُونَةٍ ١٥(Sunã) a kan wasu gadãje sãƙaƙƙu مُّتَّكِـِٔينَ عَلَيۡهَا مُتَقَٰبِلِينَ ١٦Sunã gincire a kansu, sunã mãsu kallon jũna يَطُوفُ عَلَيۡهِمۡ وِلۡدَٰنٌ مُّخَلَّدُونَ ١٧Wasu yara samãri na dindindin gẽwaya a kansu بِأَكۡوَابٍ وَأَبَارِيقَ وَكَأۡسٍ مِّن مَّعِينٍ ١٨Da wasu kõfuna da shantula da hinjãlai daga (giya) mai ɓuɓɓuga لَّا يُصَدَّعُونَ عَنۡهَا وَلَا يُنزِفُونَ ١٩Bã a sanya musu cĩwon jirĩ sabõda ita, kuma bã su buguwa وَفَٰكِهَةٍ مِّمَّا يَتَخَيَّرُونَ ٢٠Da wasu 'ya'yan itãcen marmari daga irin waɗanda suke zãɓe وَلَحۡمِ طَيۡرٍ مِّمَّا يَشۡتَهُونَ ٢١Da nãman tsuntsãye daga wanda suke ganin sha'awa وَحُورٌ عِينٌ ٢٢Da wasu mãtã mãsu fararen idanu da girmansu كَأَمۡثَٰلِ ٱللُّؤۡلُوِٕ ٱلۡمَكۡنُونِ ٢٣Kamar misãlan lu'ulu'u wanda aka ɓõye جَزَآءَۢ بِمَا كَانُواْ يَعۡمَلُونَ ٢٤A kan sakamakon, dõmin abin da suka kasance sunã aikatãwa لَا يَسۡمَعُونَ فِيهَا لَغۡوًا وَلَا تَأۡثِيمًا ٢٥Bã su jin wata yãsassar magana a cikinta, kuma bã su jin sun yi laifi إِلَّا قِيلًا سَلَٰمًا سَلَٰمًا ٢٦Sai dai wata magana (mai dãɗi): Salãmun, Salãmun وَأَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلۡيَمِينِ ٢٧Da mazõwa dãma. Mẽne ne mazõwa dãma فِي سِدۡرٍ مَّخۡضُودٍ ٢٨(Sunã) a cikin itãcen magarya maras ƙaya وَطَلۡحٍ مَّنضُودٍ ٢٩Da wata ayaba mai yawan 'ya'ya وَظِلٍّ مَّمۡدُودٍ ٣٠Da wata inuwa mĩƙaƙƙiya وَمَآءٍ مَّسۡكُوبٍ ٣١Da wani ruwa mai gudãna وَفَٰكِهَةٍ كَثِيرَةٍ ٣٢Da wasu 'ya'yan itacen marmari mãsu yawa لَّا مَقۡطُوعَةٍ وَلَا مَمۡنُوعَةٍ ٣٣Bã su yankẽwa kuma bã a hana su وَفُرُشٍ مَّرۡفُوعَةٍ ٣٤Da wasu shimfiɗu maɗaukaka إِنَّآ أَنشَأۡنَٰهُنَّ إِنشَآءً ٣٥Lalle Mũ, Mun ƙãga halittarsu ƙãgãwa فَجَعَلۡنَٰهُنَّ أَبۡكَارًا ٣٦Sa'an nan Muka sanya su budurwai عُرُبًا أَتۡرَابًا ٣٧Mãsu son mazansu, a cikin tsãrã ɗaya لِّأَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ٣٨Ga mazõwa dãma ثُلَّةٌ مِّنَ ٱلۡأَوَّلِينَ ٣٩Wata ƙungiya ce daga mutãnen farko وَثُلَّةٌ مِّنَ ٱلۡأٓخِرِينَ ٤٠Da wata ƙungiya daga mutãnen ƙarshe وَأَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ مَآ أَصۡحَٰبُ ٱلشِّمَالِ ٤١Mazõwa hagu, Mẽne ne mazõwa hagu فِي سَمُومٍ وَحَمِيمٍ ٤٢Sunã a cikin wata iskar zãfi da wani ruwan zãfi وَظِلٍّ مِّن يَحۡمُومٍ ٤٣Da wata inuwa ta hayãƙi mai baƙi لَّا بَارِدٍ وَلَا كَرِيمٍ ٤٤Bã mai sanyi ba, kuma bã mai wata ni'ima ba إِنَّهُمۡ كَانُواْ قَبۡلَ ذَٰلِكَ مُتۡرَفِينَ ٤٥Lalle sũ, sun kasance a gabãnin wannan waɗanda aka jiyar dãɗi وَكَانُواْ يُصِرُّونَ عَلَى ٱلۡحِنثِ ٱلۡعَظِيمِ ٤٦Kuma sun kasance sunã dõgẽwa a kan mummũnan zunubi mai girma وَكَانُواْ يَقُولُونَ أَئِذَا مِتۡنَا وَكُنَّا تُرَابًا وَعِظَٰمًا أَءِنَّا لَمَبۡعُوثُونَ ٤٧Kuma sun kasance sunã cẽwa: "Shin idan mun mutukuma muko kasance turɓãya da ƙasũsuwa shin lalle mũ waɗanda zã a kõma rãyarwa ne haƙĩƙatan أَوَءَابَآؤُنَا ٱلۡأَوَّلُونَ ٤٨Shin, kuma da ubanninmu na farko قُلۡ إِنَّ ٱلۡأَوَّلِينَ وَٱلۡأٓخِرِينَ ٤٩Ka ce: "Lalle mutãnen farko da na ƙarshe لَمَجۡمُوعُونَ إِلَىٰ مِيقَٰتِ يَوۡمٍ مَّعۡلُومٍ ٥٠Tabbas, waɗanda ake tãrãwa ne a cikin wani yini sananne ثُمَّ إِنَّكُمۡ أَيُّهَا ٱلضَّآلُّونَ ٱلۡمُكَذِّبُونَ ٥١Sa'an nan lalle ku, ya kũ ɓatattu, mãsu ƙaryatãwa لَأٓكِلُونَ مِن شَجَرٍ مِّن زَقُّومٍ ٥٢Lalle mãsu cĩ ne daga wata itãciya ta zaƙƙum (ɗanyen wutã) فَمَالِـُٔونَ مِنۡهَا ٱلۡبُطُونَ ٥٣Har za ku zama mãsu cika cikunna daga gare ta فَشَٰرِبُونَ عَلَيۡهِ مِنَ ٱلۡحَمِيمِ ٥٤Sa'an nan kuma mãsu shã ne, a kan wannan abin cin, daga ruwan zãfi فَشَٰرِبُونَ شُرۡبَ ٱلۡهِيمِ ٥٥Ku zama mãsu shã irin shan rãƙuma mãsu ƙishirwa هَٰذَا نُزُلُهُمۡ يَوۡمَ ٱلدِّينِ ٥٦Wannan ita ce liyãfarsu a rãnar sakamako نَحۡنُ خَلَقۡنَٰكُمۡ فَلَوۡلَا تُصَدِّقُونَ ٥٧Mũ ne Muka halitta ku, to, don me bã zã ku gaskata ba أَفَرَءَيۡتُم مَّا تُمۡنُونَ ٥٨Shin kuma kun ga abin da kuke fitarwa na maniyyi ءَأَنتُمۡ تَخۡلُقُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡخَٰلِقُونَ ٥٩Shin kũ ne kuke halitta shi, kõ kuwa mũ ne Mãsu halittãwa نَحۡنُ قَدَّرۡنَا بَيۡنَكُمُ ٱلۡمَوۡتَ وَمَا نَحۡنُ بِمَسۡبُوقِينَ ٦٠Mũ ne Muka ƙaddara mutuwa a tsakãninku, kuma ba Mu zama Mãsu gajiyãwa* ba عَلَىٰٓ أَن نُّبَدِّلَ أَمۡثَٰلَكُمۡ وَنُنشِئَكُمۡ فِي مَا لَا تَعۡلَمُونَ ٦١A kan Mu musanya waɗansu (mutãne) kamarku, kuma Mu mayar da ku a cikin wata halitta da ba ku sani ba وَلَقَدۡ عَلِمۡتُمُ ٱلنَّشۡأَةَ ٱلۡأُولَىٰ فَلَوۡلَا تَذَكَّرُونَ ٦٢Kuma lalle, ne haƙĩƙa, kun san halittar farko, to, don me ba zã ku yi tunãni ba أَفَرَءَيۡتُم مَّا تَحۡرُثُونَ ٦٣Shin, kuma kun ga abin da kũke nõmãwa ءَأَنتُمۡ تَزۡرَعُونَهُۥٓ أَمۡ نَحۡنُ ٱلزَّٰرِعُونَ ٦٤Shin, kũ ne ke tsirar da shi kõ kuwa Mũ ne Mãsu tsirarwa لَوۡ نَشَآءُ لَجَعَلۡنَٰهُ حُطَٰمًا فَظَلۡتُمۡ تَفَكَّهُونَ ٦٥Dã Munã so lalle, da Mun sanya shi bũsasshiyar ciyãwa, sai ku yini kunã mãmãkin bãƙin ciki إِنَّا لَمُغۡرَمُونَ ٦٦(Kunã cẽwa) "Lalle haƙĩƙa an azã mana tãra بَلۡ نَحۡنُ مَحۡرُومُونَ ٦٧Ã'a, mun dai zama waɗanda aka hanã wa أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلۡمَآءَ ٱلَّذِي تَشۡرَبُونَ ٦٨Shin, kuma kun ga ruwa wannan da kuke sha ءَأَنتُمۡ أَنزَلۡتُمُوهُ مِنَ ٱلۡمُزۡنِ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنزِلُونَ ٦٩Shin, kũ ne kuke saukar da shi daga girgije, kõ kuwa Mũne Mãsu saukarwa لَوۡ نَشَآءُ جَعَلۡنَٰهُ أُجَاجًا فَلَوۡلَا تَشۡكُرُونَ ٧٠Dã Mun so, dã Mun mayar da shi ruwan zartsi. To don me bã ku gõdẽwa أَفَرَءَيۡتُمُ ٱلنَّارَ ٱلَّتِي تُورُونَ ٧١Shin, kuma kun ga wutã wannan da kuke ƙyastãwa ءَأَنتُمۡ أَنشَأۡتُمۡ شَجَرَتَهَآ أَمۡ نَحۡنُ ٱلۡمُنشِـُٔونَ ٧٢Shin, kũ ne kuke ƙagã halittar itãciyarta, kõ kuwa Mũ ne Mãsu ƙãgãwa نَحۡنُ جَعَلۡنَٰهَا تَذۡكِرَةً وَمَتَٰعًا لِّلۡمُقۡوِينَ ٧٣Mũ ne Muka sanya ta wata abar wa'azi da jin dãɗi ga matafiya a cikin jẽji فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ ٧٤Sai ka tsarkake sũnan Ubangijinka Mai girma ۞ فَلَآ أُقۡسِمُ بِمَوَٰقِعِ ٱلنُّجُومِ ٧٥To, bã sai Na yi rantsuwa ba da lõkutan fãɗuwar taurãri وَإِنَّهُۥ لَقَسَمٌ لَّوۡ تَعۡلَمُونَ عَظِيمٌ ٧٦Kuma lalle ne' haƙĩƙa, rantsuwa ce mai girma, dã kun sani إِنَّهُۥ لَقُرۡءَانٌ كَرِيمٌ ٧٧Lalle shi (wannan littãfi), haƙĩƙa, abin karantãwa ne mai daraja فِي كِتَٰبٍ مَّكۡنُونٍ ٧٨A cikin wani littafi tsararre لَّا يَمَسُّهُۥٓ إِلَّا ٱلۡمُطَهَّرُونَ ٧٩Bãbu mai shãfa shi fãce waɗanda aka tsarkake تَنزِيلٌ مِّن رَّبِّ ٱلۡعَٰلَمِينَ ٨٠Wanda aka saukar ne daga Ubangijin halitta أَفَبِهَٰذَا ٱلۡحَدِيثِ أَنتُم مُّدۡهِنُونَ ٨١Shin, to, wannan lãbãrin ne kuke mãsu wulãkantãwa وَتَجۡعَلُونَ رِزۡقَكُمۡ أَنَّكُمۡ تُكَذِّبُونَ ٨٢Kuma kunã sanya arzikinku (game da shi) lalle kũ, ku ƙaryata (shi) فَلَوۡلَآ إِذَا بَلَغَتِ ٱلۡحُلۡقُومَ ٨٣To, don me idan rai ya kai ga maƙõshi? (Kusa da mutuwa) وَأَنتُمۡ حِينَئِذٍ تَنظُرُونَ ٨٤Alhãli kuwa kũ, a lõklcin nan, kunã kallo وَنَحۡنُ أَقۡرَبُ إِلَيۡهِ مِنكُمۡ وَلَٰكِن لَّا تُبۡصِرُونَ ٨٥Kuma Mũ ne mafi kusanta gare shi daga gare ku, to, amma kũ bã ku gani فَلَوۡلَآ إِن كُنتُمۡ غَيۡرَ مَدِينِينَ ٨٦To, don me in dai kun kasance bã waɗanda zã a yi wa sakamako ba تَرۡجِعُونَهَآ إِن كُنتُمۡ صَٰدِقِينَ ٨٧Ku mayar da shi (cikin jikinsa) har idan kun kasance mãsu gaskiya فَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُقَرَّبِينَ ٨٨To, amma idan (mai mutuwar) ya kasance daga makusanta فَرَوۡحٌ وَرَيۡحَانٌ وَجَنَّتُ نَعِيمٍ ٨٩Sai hũtawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni'ima وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ٩٠Kuma amma idan ya kasance daga mazõwa dãma فَسَلَٰمٌ لَّكَ مِنۡ أَصۡحَٰبِ ٱلۡيَمِينِ ٩١Sai (a ce masa) aminci ya tabbata a gare ka daga mazõwa dãma وَأَمَّآ إِن كَانَ مِنَ ٱلۡمُكَذِّبِينَ ٱلضَّآلِّينَ ٩٢Kuma amma idan ya kasance daga mãsu ƙaryatãwar, ɓatattun فَنُزُلٌ مِّنۡ حَمِيمٍ ٩٣Sai wata liyãfa ta ruwan zãfi وَتَصۡلِيَةُ جَحِيمٍ ٩٤Da ƙõnuwa da Jahĩm إِنَّ هَٰذَا لَهُوَ حَقُّ ٱلۡيَقِينِ ٩٥Lalle wannan, haƙĩƙa, ita ce gaskiya ta yaƙĩni فَسَبِّحۡ بِٱسۡمِ رَبِّكَ ٱلۡعَظِيمِ ٩٦Sabõda haka, ka tsarkake* sũnan Ubangijinka, Mai karimci

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.