بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
ٱلرَّحۡمَٰنُ ١(Allah) Mai rahama عَلَّمَ ٱلۡقُرۡءَانَ ٢Yã sanar da Alƙur'ani خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ ٣Yã halitta mutum عَلَّمَهُ ٱلۡبَيَانَ ٤Yã sanar da shi bayãni (magana) ٱلشَّمۡسُ وَٱلۡقَمَرُ بِحُسۡبَانٍ ٥Rãnã da watã a kan lissãfi suke وَٱلنَّجۡمُ وَٱلشَّجَرُ يَسۡجُدَانِ ٦Kuma tsirrai mãsu yãɗo da itãce sunã tawãlu'i وَٱلسَّمَآءَ رَفَعَهَا وَوَضَعَ ٱلۡمِيزَانَ ٧Kuma samã Ya ɗaukaka ta, Kuma Yã aza sikẽli أَلَّا تَطۡغَوۡاْ فِي ٱلۡمِيزَانِ ٨Dõmin kada ku karkatar da sikẽlin وَأَقِيمُواْ ٱلۡوَزۡنَ بِٱلۡقِسۡطِ وَلَا تُخۡسِرُواْ ٱلۡمِيزَانَ ٩Kuma ku daidaita awo da ãdalci, kuma kada ku rage sikẽlin وَٱلۡأَرۡضَ وَضَعَهَا لِلۡأَنَامِ ١٠Kuma ƙasã Yã aza ta dõmin tãlikai فِيهَا فَٰكِهَةٌ وَٱلنَّخۡلُ ذَاتُ ٱلۡأَكۡمَامِ ١١A cikinta akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno mai kwasfa وَٱلۡحَبُّ ذُو ٱلۡعَصۡفِ وَٱلرَّيۡحَانُ ١٢Da ƙwãya mai sõshiya da ƙamshi فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ١٣To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangjinku *kuke ƙaryatãwa خَلَقَ ٱلۡإِنسَٰنَ مِن صَلۡصَٰلٍ كَٱلۡفَخَّارِ ١٤Yã halitta mutum daga ƙẽkasasshen yumɓu kumar kasko وَخَلَقَ ٱلۡجَآنَّ مِن مَّارِجٍ مِّن نَّارٍ ١٥Kuma ya halitta aljani daga bira daga wutã فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ١٦To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa رَبُّ ٱلۡمَشۡرِقَيۡنِ وَرَبُّ ٱلۡمَغۡرِبَيۡنِ ١٧Ubangjin mafita biyu na rãnã, kuma Ubangijin mafãɗã biyu na rãnã فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ١٨To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa مَرَجَ ٱلۡبَحۡرَيۡنِ يَلۡتَقِيَانِ ١٩Yã garwaya tẽku biyu (ruwan dãɗi da na zartsi) sunã haɗuwa بَيۡنَهُمَا بَرۡزَخٌ لَّا يَبۡغِيَانِ ٢٠A tsakãninsu akwai shãmaki, bã za su ƙetare haddi ba فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٢١To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa يَخۡرُجُ مِنۡهُمَا ٱللُّؤۡلُؤُ وَٱلۡمَرۡجَانُ ٢٢Lu'ulu'u da murjãni na fita daga gare su فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٢٣To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa وَلَهُ ٱلۡجَوَارِ ٱلۡمُنشَـَٔاتُ فِي ٱلۡبَحۡرِ كَٱلۡأَعۡلَٰمِ ٢٤Kuma Yanã da manyan jirãge, waɗanda ake ƙãgãwa a cikin tẽku kamar manyan duwãtsu فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٢٥To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa كُلُّ مَنۡ عَلَيۡهَا فَانٍ ٢٦Dukkan wanda ke kanta* mai ƙãrẽwa ne وَيَبۡقَىٰ وَجۡهُ رَبِّكَ ذُو ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ ٢٧Kuma Fuskarar Ubangijinka, Mai girman Jalala da karimci, ita ce take wanzuwa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٢٨To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa يَسۡـَٔلُهُۥ مَن فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ كُلَّ يَوۡمٍ هُوَ فِي شَأۡنٍ ٢٩wanda ke a cikin sammai da ƙasã yanã rõƙon Sa (Allah), a kullum Allah na a cikin wani sha'ani فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٣٠To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa سَنَفۡرُغُ لَكُمۡ أَيُّهَ ٱلثَّقَلَانِ ٣١Zã mu ɗauki lõkaci sabõda ku, yã kũ *mãsu nauyin halitta biyu فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٣٢To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa يَٰمَعۡشَرَ ٱلۡجِنِّ وَٱلۡإِنسِ إِنِ ٱسۡتَطَعۡتُمۡ أَن تَنفُذُواْ مِنۡ أَقۡطَارِ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِ فَٱنفُذُواْۚ لَا تَنفُذُونَ إِلَّا بِسُلۡطَٰنٍ ٣٣Ya jama'ar aljannu da mutãne! Idan kunã iya zarcẽwa daga sãsannin sammai da ƙasã to ku zarce. Bã za ku iya zarcẽwaba fãce da wani dalĩli فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٣٤To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa يُرۡسَلُ عَلَيۡكُمَا شُوَاظٌ مِّن نَّارٍ وَنُحَاسٌ فَلَا تَنتَصِرَانِ ٣٥Anã sako wani harshe daga wata wutã a kanku, da narkakkiyar tagulla. To, bã zã ku nẽmi taimako ba فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٣٦To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فَإِذَا ٱنشَقَّتِ ٱلسَّمَآءُ فَكَانَتۡ وَرۡدَةً كَٱلدِّهَانِ ٣٧Sa'an nan idan sama ta tsãge kuma ta zama jã kamar jar fãta فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٣٨To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فَيَوۡمَئِذٍ لَّا يُسۡـَٔلُ عَن ذَنۢبِهِۦٓ إِنسٌ وَلَا جَآنٌّ ٣٩To, a ran nan bã zã a tambayi wani mutum laifinsa ba, kuma haka aljani فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٠To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa يُعۡرَفُ ٱلۡمُجۡرِمُونَ بِسِيمَٰهُمۡ فَيُؤۡخَذُ بِٱلنَّوَٰصِي وَٱلۡأَقۡدَامِ ٤١zã a iya sanin mãsu laifi da alãmarsu, sabõda haka sai a kãma kwarkaɗarsu da sãwãyensu فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٢To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa هَٰذِهِۦ جَهَنَّمُ ٱلَّتِي يُكَذِّبُ بِهَا ٱلۡمُجۡرِمُونَ ٤٣Wannan Jahannama ce wadda mãsu laifi ke ƙaryatãwa game da ita يَطُوفُونَ بَيۡنَهَا وَبَيۡنَ حَمِيمٍ ءَانٍ ٤٤Sunã kẽwaya a tsakaninta da ruwan ɗimi mai tsananin tafasa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٥To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa وَلِمَنۡ خَافَ مَقَامَ رَبِّهِۦ جَنَّتَانِ ٤٦Kuma wanda ya ji tsõron tsayãwa a gaba ga Ubangijinsa yanã da Aljanna biyu فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٧To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa ذَوَاتَآ أَفۡنَانٍ ٤٨Mãsu rassan itãce فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٤٩To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِمَا عَيۡنَانِ تَجۡرِيَانِ ٥٠A cikinsu akwai marẽmari biyu sunã gudãna فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥١To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِمَا مِن كُلِّ فَٰكِهَةٍ زَوۡجَانِ ٥٢A cikinsu akwai nau'i biyu daga kõwane 'ya'yan itãcen marmari فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٣To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ فُرُشِۭ بَطَآئِنُهَا مِنۡ إِسۡتَبۡرَقٍۚ وَجَنَى ٱلۡجَنَّتَيۡنِ دَانٍ ٥٤Sunã gincire a kan waɗansu shimfiɗu cikinsu tufãfin alharĩni mai kauri ne kuma nũnannun 'yã'yan itãcen Aljannar biyu kusakusa suke فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٥To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِنَّ قَٰصِرَٰتُ ٱلطَّرۡفِ لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٌ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنٌّ ٥٦A cikinsu akwai mãtã mãsu taƙaita ganinsu, wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗebe budurcinsu ba kuma haka wani aljani فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٧To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa كَأَنَّهُنَّ ٱلۡيَاقُوتُ وَٱلۡمَرۡجَانُ ٥٨Kamar dai su yaƙũtu ne da murjãni فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٥٩To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa هَلۡ جَزَآءُ ٱلۡإِحۡسَٰنِ إِلَّا ٱلۡإِحۡسَٰنُ ٦٠Shin, kyautatãwa nã da wani sakamako? (Ã'aha) fãce kyautatãwa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦١To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa وَمِن دُونِهِمَا جَنَّتَانِ ٦٢Kuma baicinsu akwai waɗansu gidãjen Aljanna biyu فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦٣To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa مُدۡهَآمَّتَانِ ٦٤Mãsu duhun inuwa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦٥To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِمَا عَيۡنَانِ نَضَّاخَتَانِ ٦٦A cikinsu akwai marẽmari biyu masu kwarãrar ruwa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦٧To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِمَا فَٰكِهَةٌ وَنَخۡلٌ وَرُمَّانٌ ٦٨A cikinsu akwai 'ya'yan itãcen marmari da dabĩno darummãni فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٦٩To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa فِيهِنَّ خَيۡرَٰتٌ حِسَانٌ ٧٠A cikinsu, akwai wasu mãtã mãsu kyawun hãlãye, mãsu kyaun halitta فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٧١To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa حُورٌ مَّقۡصُورَٰتٌ فِي ٱلۡخِيَامِ ٧٢Mãsu farin idãnu da baƙinsu waɗanda aka tsare a cikin haimõmi فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٧٣To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa لَمۡ يَطۡمِثۡهُنَّ إِنسٌ قَبۡلَهُمۡ وَلَا جَآنٌّ ٧٤Wani mutum, gabanin mazajensu bai ɗẽbe budurcinsu ba, kuma haka wani aljani فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٧٥To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa مُتَّكِـِٔينَ عَلَىٰ رَفۡرَفٍ خُضۡرٍ وَعَبۡقَرِيٍّ حِسَانٍ ٧٦Sunã gincire a kan wasu matãsai mãsu kõren launi da katĩfun Abkara kyãwãwa فَبِأَيِّ ءَالَآءِ رَبِّكُمَا تُكَذِّبَانِ ٧٧To, sabõda wanne daga ni'imõmin Ubangijinku, kuke ƙaryatãwa تَبَٰرَكَ ٱسۡمُ رَبِّكَ ذِي ٱلۡجَلَٰلِ وَٱلۡإِكۡرَامِ ٧٨Sũnan Ubangjinka, Mai girman Jalãla da Karimci, ya tsarkaka