Millat al-Islam

Chapter 91 · 15 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Ash-Shams in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Ash-Shams (1346 reciters)
Meccanسورة الشمس15 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَٱلشَّمۡسِ وَضُحَىٰهَا ١Ina rantsuwa da rãnã da hantsinta وَٱلۡقَمَرِ إِذَا تَلَىٰهَا ٢Kuma da wata idan ya bi ta وَٱلنَّهَارِ إِذَا جَلَّىٰهَا ٣Da yini a lõkacin da ya bayyana ta وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰهَا ٤Da dare a lõkacin da ya ke rufe ta وَٱلسَّمَآءِ وَمَا بَنَىٰهَا ٥Da sama da abin da ya gina ta وَٱلۡأَرۡضِ وَمَا طَحَىٰهَا ٦Da ƙasã da abin da ya shimfiɗa ta وَنَفۡسٍ وَمَا سَوَّىٰهَا ٧Da rai da abin da ya daidaita shi فَأَلۡهَمَهَا فُجُورَهَا وَتَقۡوَىٰهَا ٨Sa'an nan ya yi masa Ilhamar fãjircinsa da shiryuwarsa قَدۡ أَفۡلَحَ مَن زَكَّىٰهَا ٩Lalle ne wanda ya tsarkake* shi (rai) ya sãmi babban rabo وَقَدۡ خَابَ مَن دَسَّىٰهَا ١٠Kuma lalle ne wanda ya turbuɗe* shi (da laifi) ya tãɓe كَذَّبَتۡ ثَمُودُ بِطَغۡوَىٰهَآ ١١Samũdãwa sun ƙaryata (Annabinsu), dõmin girman kansu إِذِ ٱنۢبَعَثَ أَشۡقَىٰهَا ١٢A lõkacin da mafi shaƙãwarsu ya tafi (wurin sõke rãkumar sãlihu) فَقَالَ لَهُمۡ رَسُولُ ٱللَّهِ نَاقَةَ ٱللَّهِ وَسُقۡيَٰهَا ١٣Sai Manzon Allah ya gaya musu cewa: "Ina tsõratar da ku ga rãƙumar Allah da ruwan shanta فَكَذَّبُوهُ فَعَقَرُوهَا فَدَمۡدَمَ عَلَيۡهِمۡ رَبُّهُم بِذَنۢبِهِمۡ فَسَوَّىٰهَا ١٤Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan suka sõke ta. Sabõda haka Ubangijinsu Ya darkãke su, sabõda zunubinsu. Sa'an nan Ya daidaita ta (azãbar ga mai laifi da maras laifi) وَلَا يَخَافُ عُقۡبَٰهَا ١٥Kuma bã ya tsõron ãƙibarta (ita halakãwar)

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.