بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلَّيۡلِ إِذَا يَغۡشَىٰ ١Inã rantsuwa da dare a lõkacin da yake rufẽwa وَٱلنَّهَارِ إِذَا تَجَلَّىٰ ٢Da yini a lõkacin da yake kuranyẽwa وَمَا خَلَقَ ٱلذَّكَرَ وَٱلۡأُنثَىٰٓ ٣Da abin da ya halitta namiji da mace إِنَّ سَعۡيَكُمۡ لَشَتَّىٰ ٤Lãlle ne ayyukanku, dabam-dabam suke فَأَمَّا مَنۡ أَعۡطَىٰ وَٱتَّقَىٰ ٥To, amma wanda ya yi kyauta, kuma ya yi taƙawa وَصَدَّقَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ ٦Kuma ya gaskata kalma* mai kyãwo فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡيُسۡرَىٰ ٧To, zã Mu sauƙaƙe masa har ya kai ga sauƙi وَأَمَّا مَنۢ بَخِلَ وَٱسۡتَغۡنَىٰ ٨Kuma amma wanda ya yi rõwa, kuma ya wadãtu da kansa وَكَذَّبَ بِٱلۡحُسۡنَىٰ ٩Kuma ya ƙaryatar da kalma mai kyãwo فَسَنُيَسِّرُهُۥ لِلۡعُسۡرَىٰ ١٠To, zã Mu sauƙaƙke masa har ya kai ga tsanani وَمَا يُغۡنِي عَنۡهُ مَالُهُۥٓ إِذَا تَرَدَّىٰٓ ١١Kuma dũkiyarsa ba ta wadãtar masa da kõme ba, a lõkacin da ya gangara (a wuta) إِنَّ عَلَيۡنَا لَلۡهُدَىٰ ١٢Lãlle aikin Mu ne, Mu bayyana shiriya وَإِنَّ لَنَا لَلۡأٓخِرَةَ وَٱلۡأُولَىٰ ١٣Kuma lalle ne Lãhira da duniya Namu ne فَأَنذَرۡتُكُمۡ نَارًا تَلَظَّىٰ ١٤Sabõda haka, Na yi maku gargaɗi da wuta mai babbaka لَا يَصۡلَىٰهَآ إِلَّا ٱلۡأَشۡقَى ١٥Bãbu mai shigarta sai mafi Tabewa ٱلَّذِي كَذَّبَ وَتَوَلَّىٰ ١٦Wanda ya ƙaryata, kuma ya jũya bãya وَسَيُجَنَّبُهَا ٱلۡأَتۡقَى ١٧Kuma mafi taƙawa* zai nisance ta ٱلَّذِي يُؤۡتِي مَالَهُۥ يَتَزَكَّىٰ ١٨Wanda yake bãyar da dũkiyarsa, alhãli yana tsarkaka وَمَا لِأَحَدٍ عِندَهُۥ مِن نِّعۡمَةٍ تُجۡزَىٰٓ ١٩Alhãli bãbu wani mai wata ni'ima wurinsa wadda ake nẽman sakamakonta إِلَّا ٱبۡتِغَآءَ وَجۡهِ رَبِّهِ ٱلۡأَعۡلَىٰ ٢٠Fãce dai nẽman yardar Ubangijinsa Mafi ɗaukaka وَلَسَوۡفَ يَرۡضَىٰ ٢١To, lalle ne zai yarda (da sakamakon da zã a bã shi)