Millat al-Islam

Chapter 94 · 8 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Inshirah in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Inshirah (1282 reciters)
Meccanسورة الشرح8 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

أَلَمۡ نَشۡرَحۡ لَكَ صَدۡرَكَ ١Ba Mu bũɗa maka zũciyarka ba (dõmin ɗaukar haƙuri da fahimta) وَوَضَعۡنَا عَنكَ وِزۡرَكَ ٢Kuma Muka saryar maka da nauyinka, Ashe ٱلَّذِيٓ أَنقَضَ ظَهۡرَكَ ٣Wanda ya nauyayi bãyanka وَرَفَعۡنَا لَكَ ذِكۡرَكَ ٤Kuma Muka ɗaukaka maka ambatonka فَإِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا ٥To, lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi إِنَّ مَعَ ٱلۡعُسۡرِ يُسۡرًا ٦Lalle ne tãre da tsananin nan akwai wani sauƙi فَإِذَا فَرَغۡتَ فَٱنصَبۡ ٧Sabõda haka idan ka ƙãre (ibãda) sai ka kafu (kana rõƙon Allah) وَإِلَىٰ رَبِّكَ فَٱرۡغَب ٨Kuma zuwa ga Ubangijinka ka yi kwaɗayi

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.