بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ
وَٱلسَّمَآءِ ذَاتِ ٱلۡبُرُوجِ ١Inã rantsuwa da sama mai taurãrin lissafin shekara وَٱلۡيَوۡمِ ٱلۡمَوۡعُودِ ٢Da yinin da aka yi alkawarin zuwansa وَشَاهِدٍ وَمَشۡهُودٍ ٣Da yini mai shaidu, da yini da ake halarta* a cikinsa قُتِلَ أَصۡحَٰبُ ٱلۡأُخۡدُودِ ٤An la'ani mutãnen rãmi ٱلنَّارِ ذَاتِ ٱلۡوَقُودِ ٥Wato wuta wadda aka hura إِذۡ هُمۡ عَلَيۡهَا قُعُودٌ ٦A lõkacin da suke a kan (gefen) ta a zazzaune وَهُمۡ عَلَىٰ مَا يَفۡعَلُونَ بِٱلۡمُؤۡمِنِينَ شُهُودٌ ٧Alhãli sũ, bisa ga abin da suke aikatãwa ga mũminai, sunã halarce وَمَا نَقَمُواْ مِنۡهُمۡ إِلَّآ أَن يُؤۡمِنُواْ بِٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡحَمِيدِ ٨Kuma ba su tuhumce su ba, fãce kawai domin sun yi ĩmãni da Allah Mabuwãyi, wanda ake gõdewa ٱلَّذِي لَهُۥ مُلۡكُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۚ وَٱللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيۡءٍ شَهِيدٌ ٩Wanda Yake shi ne da mulkin sammai da ƙasa, kuma Allah a kan kõme halarce Yake إِنَّ ٱلَّذِينَ فَتَنُواْ ٱلۡمُؤۡمِنِينَ وَٱلۡمُؤۡمِنَٰتِ ثُمَّ لَمۡ يَتُوبُواْ فَلَهُمۡ عَذَابُ جَهَنَّمَ وَلَهُمۡ عَذَابُ ٱلۡحَرِيقِ ١٠Lalle ne waɗanda suka fitini mũminai maza da mũminai mãta, sa'an nan ba su tũba ba to, sunã da azãbar Jahannama, kuma sunã da azãbar gõbara إِنَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّٰتٌ تَجۡرِي مِن تَحۡتِهَا ٱلۡأَنۡهَٰرُۚ ذَٰلِكَ ٱلۡفَوۡزُ ٱلۡكَبِيرُ ١١Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashin gidãjen. Wancan abu fa shi ne rabo babba إِنَّ بَطۡشَ رَبِّكَ لَشَدِيدٌ ١٢Lalle ne damƙar Ubangijinka mai tsanani ce ƙwarai إِنَّهُۥ هُوَ يُبۡدِئُ وَيُعِيدُ ١٣Lalle ne Shĩ, Shi ne Mai ƙãga halitta, kuma Ya mayar da ita (bãyan mutuwa) وَهُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلۡوَدُودُ ١٤Kuma Shi ne Mai gãfara, Mai bayyana sõyayya ذُو ٱلۡعَرۡشِ ٱلۡمَجِيدُ ١٥Mai Al'arshi mai girma فَعَّالٌ لِّمَا يُرِيدُ ١٦Mai aikatãwa ga abin da Yake nufi هَلۡ أَتَىٰكَ حَدِيثُ ٱلۡجُنُودِ ١٧Ko lãbãrin rundanõni yã zo maka فِرۡعَوۡنَ وَثَمُودَ ١٨Fir'auna da samũdãwa بَلِ ٱلَّذِينَ كَفَرُواْ فِي تَكۡذِيبٍ ١٩Ã'aha! waɗanda suka kãfirta sunã cikin ƙaryatãwa وَٱللَّهُ مِن وَرَآئِهِم مُّحِيطُۢ ٢٠Alhãli, Allah daga bãyansu, Mai kẽwaye su ne (da sanin Sa) بَلۡ هُوَ قُرۡءَانٌ مَّجِيدٌ ٢١Ã'aha! Shi Alƙur'ãni ne mai girma فِي لَوۡحٍ مَّحۡفُوظِۭ ٢٢A cikin Allo tsararre