Millat al-Islam

Chapter 104 · 9 verses · Abubakar Mahmood Jummi

Surah Al-Humaza in Hausa

Arabic with tafsir Listen to Surah Al-Humaza (1273 reciters)
Meccanسورة الهمزة9 verses

بِسۡمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحۡمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

وَيۡلٌ لِّكُلِّ هُمَزَةٍ لُّمَزَةٍ ١Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa) ٱلَّذِي جَمَعَ مَالًا وَعَدَّدَهُۥ ٢Wanda ya tara dũkiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa يَحۡسَبُ أَنَّ مَالَهُۥٓ أَخۡلَدَهُۥ ٣Yana zaton cẽwa dũkiyarsa za ta dawwamar da shi كـَلَّاۖ لَيُنۢبَذَنَّ فِي ٱلۡحُطَمَةِ ٤A'aha! Lalle ne zã a jẽfa shi a cikin Huɗama وَمَآ أَدۡرَىٰكَ مَا ٱلۡحُطَمَةُ ٥Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama نَارُ ٱللَّهِ ٱلۡمُوقَدَةُ ٦Wutar Allah ce wadda ake hurawa ٱلَّتِي تَطَّلِعُ عَلَى ٱلۡأَفۡـِٔدَةِ ٧Wadda take lẽƙãwa a kan zukata إِنَّهَا عَلَيۡهِم مُّؤۡصَدَةٌ ٨Lalle ne ita abar kullẽwa ce a kansu فِي عَمَدٍ مُّمَدَّدَةِۭ ٩A cikin wasu ginshiƙai mĩƙaƙƙu

Translation: Abubakar Mahmood Jummi.